Main menu

Pages

 

Kewayawa ta bayan gidan tayi ,inda Ladi police ke kiwon kajin turawan ta da su gis ,tolo tolo  da sauran Nau'in tsintsaye masu ban sha'awa .


A hankali ta nufi wajen tulin tantabarun da suka baje a ƙasa fululu,ta shiga ɗiban Alkama tana watsa masu ,aiko kafin ai haka sun fewayeta suna tsinta da en koke koken su mai kamar waƙa 


Lumshe Ido tayi tana shaƙar Ni'imtacciyar iskar dake bugawa ,kukansu na saka mata nishaɗin da sam bata samunsa a gidansu 


Sadiƙu dake can gefe zaune ƙarƙashin rumfar da aka tanada don hutuwa ,sanye yike cikin gajeren wando da singlet na kakin land soldier, chat yake a kan laptop ɗinsa saidai lokaci zuwa lokaci yina ɗagowa yina kallon yarinyar ,sosai yarinyar ta tafi da Hankalinsa musamman yanda ya gane tanada tausayi da son dabbobi ,hakan yasa in tayi wani abun yikan ɗan tsura mata ido wani abun kuma sai ya mere baki ya cigaba da shafa system ɗinsa irin bai masa ba ɗin nan,amma yinajin bagaga ɗin tantabarun zai kuma ɗagowa


Daga ƙarshe dai ɗan tagumi ya rafka ya dogare hannunsa akan table ɗin gabansa ,ya ɗan karkato kaɗan yina ƙare mata kallo ,zuwa yanzu yafara gajiya da damunta ,don sosai ta fara takura masa ,amma kuma halshensa yayi mugun masa nauyi hakan yasa ya kasa magana tsabagen madarar miskilamci .

Ɗan shaking jikinta tayi ,wanda yasa tattabarun tashi firrrrr ,aiko wani ɗan murmushine ya ƙwace mata wanda yasa dimple ɗin gefen kuncinta loɓawa ,a take kuma wasu hawaye marasa dalili suka silalo a kuncinta.


Ɗan tsai da ransa yayi ,tunanin sa me yasata kuka kuma lokaci ɗaya tana dariya ?


Itakam sam batasan wajen da halittan ɗan Adam ba ,cigaba da bin duk inda wasu farare da grey ɗin tantabaru suka saka ƙafarsu take tana ɗan tafa hannu tana masu waƙa 

"Tantabara woooo....Tantabara woooo" 


Tana cigaba da binsu gudu gudu sauri² ,cikin rashin zato ta ƙumu da ginin daya ɗan kewaye wajen da yike zaune ,aikuwa ta faɗa rikicaaa cikin flowers ɗin dake a gefe .

Ta kuwa ƙwalla ƙaran Azaba


Dafe kai yayi cikin takaici ,a duniyarsa ya tsani ƙara 

Wani ɗan siririn tsaki yaja ,kafin a kasalance ya miƙe yaje gabanta ya tsaya ƙerere ya miƙo mata hannunsa alamar ta kama hannunsa ta miƙe 


Bilƙis daga inda take kwance dafe dakai ta ga an sagalo mata kyakkyawar choco hannu lulluɓe da ni'imtaccen gashi 


Ɗago lulun eyes ɗin ta tayi ta kafesa da ido ,saidai tana kallonta taji cikinta ya ɗauki jiniya wui wui wui  . Saboda kayan da suke jikknsa na ɗaya kenan sannan na biyu ya wani tamke fuska sai hura hanci yake .


Wani sautin marayan kuka ta saka ,zufa ta ko'ina na tsatsafo mata a duniyar ta ta tsani ko kakin ɗan sanda bare na soja 


Kansa ne ya sara masa take ya fara jin kansa na masa ciwo ,rayawa yake a ransa meye hadinsa da Wagga yarinyar wacce ruwan hawaye kamar sun mata yawa,da har yike jin ƙolafucin ya taimaketa? 


Duddulo mata Idanuwarsa yayi duka waje sannan ya doka mata tsawa ,wanda ya haddasa ma jijiyoyin kansa bayyana 


Jikinta ne ya shiga ɓari ,take ta fara mulmule cikin ciyayin wajen ta kuwa shokaresa da takalmin ƙafarta a ƙafa 


Wani malolon takaici ne ya ɗebesa baisan sanda ya miƙa hannu ya damƙota ya cikuikuyo wuyar rigarta ya tsinke lafiyayyen kuncinta da mari ba. 


Wani ƙara ta saki sai ga jini na tuttulowa ta kuncinta ,take ta shiga Marisa kamar taliya ta yi luuuuu zata zube a ƙasa yayi saurin tallafota ta riɓu akan ƙafafuwan sa



Hajiya Binta da tun kukan bilki na farko ta fito harabar gidan da gudu tana ƙwalla mata kira ,har ta shigo kuma a daidai nan ,Sadiƙ ya kifeta da mari ta sulale kan ƙafarsa 


Wani vibration ne ya kama jikin Hajiya Binta ƙif taja ta tsaya ta kasa ƙarasawa har saida Ladi police ta ƙaraso da sauri ,saidai ganinta a saman ƙafan Sadik ya sata tsayawa a gabansa ita bata ɗagota ba sai ma ta hau rawan baki 


"My boy ya haka ? Halan ta yi rashin ji?"


Wani kunyane ya kamasa don shi kansa yasan abinda yayi sam bai kyautu ba ,amma saboda aja girma ,kawai sai ya waniyi ball da ita ya zare ƙafarsa ,ya fara taku cike da gadara da ƙasaita ,ba tare da ya tamka Hajiya Ladin ba.


Sai sannan Hajiya Binta ta ƙaraso kan Bilƙis ,ta rarumo kanta "mai gadon  zinare ,me ya faru?...." Damtse bakinta tayi da sauri ganin yanda hancin erta ke bulbula da jini jajazir 


Wani luuuuu ,tayi da ido kamar wacce zata sume,sannan ta miƙa hannunta tana nuna bayan sadiƙu


"Kambala'i!!" Wani zabura Hajiya Binta tayi taje ta bayansa ta damƙo wuyarsa ,batai wata ² ba ta kafe shi da wani irin gigitaccen mari ta sake ɗaga hannu ta wanke ɗayan kuncinsa 



Hajiya ladi ruɗewa iya ruɗewa ko tayi Faɗi take "A'ah Binta karki kuskure ki dakata kinsan shiɗin wanene kuwa?"


Sa hannu tayi ta zungure masa goshi tamkar ta samu ƙaramin yaro


"Yaro na gani wanda aka haifa da jini tamkar yanda na haifa ɗiyata Bilkisu ,don haka ke kika san ko shi wane ne ,mumugunci kawai Azzalumi!"


Dafe kansa yayi da sauri zai iya cewa a iya tsayin rayuwarsa ba'a taɓa zaginsa ba ,kowa girmamasa yike ,sai sanadiyyar zuwan shi wannan Gidan ,dole yau ya koma gidan babansa saidai duk abinda zai faru ya faru


Da kyar ya fara jan sawunsa yina barin hanyar ,ba tare da yace kanzil ba ,itakuwa Hajiya Binta tayi kan ɗiyarta ko a gefen mayafinta ,bata damu da magiyar da Hajiya ladi take ma mumuguncin yaron da taji suna kira da Sadik ba .



Wanene Sadiƙ?

Sadiƙ Yarone na shidda ga sarki Abdul gaffar ,Yinada yayu uku maza ,Adam,sulaiman ,da Ja'afar ,sai mata biyu sadiya da A'isha sai sannan nan shi Abubakar Sadik, bayansa akwai yara Ashirin da takwas wanda suka kasance harda ɗiyoyin ƙwarƙwarorin sarki Abdulgaffar. 


Kaf cikin yaran mai martaba ba wanda ya shiga zuciyar mai martaba kamar Sadik ,a yayinda ba ɗa marar ji kamar sa ,sam bai ɗakko halin babansa na dattako da girmama mutane talakawansa ba ,Girman kai da Izza tamkar shine Sarkin ,wannan dalilin yasa tun sanda ya gama secondary school ga buɗe ɗaya daga cikin guest house ɗinsa dake bayan gari ya maidashi fadarsa 


Sam baya zaman fadanci  tsakaninsa da gida sai in dare yayi ,yina da fadawansa ,da masu hidimta masa ,ana masa zaman fadanci ya hakimce a karaga 

Kafatanin Abokan Sadik ,dole su kasance a karkashin ikon sa ,dole ya bautar dasu in ba haka ba a rabu 


A gida babansa yike sarki Amma shima a fadarsa sarkine ,don haka kowa sarki yike Kiran Sadiq don kawai a zauna lafiya ,Sadik tun yina karamin sa Allah ya hore masa son Mulki hakan yasa sam baya saka ƙananun kaya sai nauyayan kaya ,kuma ko club zasu da Abokai da kayansa yike zuwa .


Tun bayan da Sadik da babban Abokinsa ,yaron fagachi wanda suke kiransa da sarautan gidansu wato  Fagachi ,tun sanda suka gama makaranta fagachi yace shi soja yike son zama ,a ra'ayin Sadik yafison zama lauya amma saboda baison rabuwa da Abokinsa mai fasa masa kai a koda yaushe yina masa fadanci da banbaɗanci yasa yaje ya sama mai martaba ,akan Alankatabir sai a nema masu NDA da Yusuf Fagachi  


Soyayyan da mai martaba kewa Sadik yasa shi kasa gane illan kasancewan jininsa Soja 


Sun fara karatun soja cikin nasara saidai suna tama 3  A lokacin ne tsautsayi ya afkawa Sadik ,Abunda ko ya faru shine sun shirya get together da abokansa a wajen school sai dai ba daman fita ,yayi duk yanda za'a barshi ya fita amma bai yiwu ba 


Ya kuwa fakaici idon kowa ya haure katanga ,dirkansa keda wuya sai a hannun wani major 


Ran manjon ya ɓaci gaya ,saboda kowa yina sane da rashin ji irin na Sadik ,ƙaramun laifi ya zama Babba ƙarshe aka koresa aka dawo dashi gida 


Kasantuwar hakan babbar abun kunya ne ga mamansa Hajiya mai babban ɗaki ,musamman ga tsakankanun kishiyoyinta da sukayi dace da ɗiyoyi nitsatsu ,yasa tayi shawara da jakadiyarta suka turasa  gidan Commissioner of police a matsayin maɓoyan sirri har a gani in za'a iya gyara matsalar sai ya koma makarantar sa batare da kowa ya sani ba ........saidai kuma kash mai hali bayi fasa halinsa  tunda Ladi polis ta ƙyalla ido akan Sadik taji tana azaban sonsa bata damu da ƙananun shekarunsa ba ,yanzu haka kuma taci alwashin sai Sadik ya sota kota halin ƙaƙa ,saidai kuma kashhhhh ,tun kafin ai nisa Hajiya Binta ta kwaɓa mata garinta ,batasan ya zata shawo kan sa ba ,duba da Yarone shi mai azaban zuciya ga baƙin hali ga riƙo da ƙulli.




©Alheri Writers Association

author-img
Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop

Comments

table of contents title