Main menu

Pages

 

Daɓas tayi zaman ƴan bori a wajen ,sai sharɓe kawai takeyi ,wannan wani irin baƙar ƙaddarace? Uwata mazinaciya ,ƴar maɗigo , menene maɗigo ma tukun na? ,Kenan gorin da ƴan gidanmu ke mun da gaske ne?


Tana nan zaune taga Hajiya ladi police ta fito a hargitse tayi hanyar part ɗin ta ,wani mugun tsanarta taji ya fara shigarta ,sarai tasan collabo ɗin ta da mamanta shi ya canja Hajiya Binta a da sam ba haka take ba .


Ta kwashe kusan 1 hour kafin ta hango Hajiya Bintan ta riƙo hannun Abdul da ɗan firgice a fuskarta sai gyara zaman kallabi da mayafi take ,har ta ƙaraso inda bilki take


"Muje ko? Tsawan awa ina jiran ki falo na aza kon barci a dakin Aminiya ne ashe kina nan kina fama da ƙufulanci?"


Warrrrr ta watsa mata ƙwarar Idonta ,kafin ta raya a zuciyarta 

"Bayan fasiƙanci da cin amanar ƙawance harda ƙarya?? Me ya sama mamana ne wai?"


Tsam ta miƙe ta kawo hannu zata dafa mata kafaɗa tayi saurin ƙwace kanta ,ta yi gaba da sauri ,bayan ta Turo baki gaba ,babu uhm ba um um.


 ******


A ɗan sahu duk yanda taso taji cikin Bilƙis ta kasa fahimtar ta ,kai daga ƙarshe ta ɗebeta tayi watsi da Al'amarin ta 


"Yarinya sai baƙar rai? Allah yasa karki gaji ubanki don zaman gidan miji zaima mutum wuya,don wannan zaman gaban kana gwada wa namiji dukan tsiya zai maki yakuma haramta maki sanwa" 


Ta cigaba da jera sababi har suka isa gida 


Wasa wasa ,sun kwashe kwanaki bata magana da mamanta da kowa ma na gidan tsakaninta da kowa da safe tabi ɗaki ² ta gaishesu da safe ta wuce makaranta.


******


Friday 12.30 

Tunda Bilkisu ta dawo daga Boko ta tarar da umman na zaune a falo tana waya ,da sallama ranganɗau a bakinta ta shigo ,saidai da sauri ta mata birki ta hanyar ɗaura mata yatsa a baki 

"Shisssshhhh" Alamar tayi shiru ,sannan ta nuna mata uwar ɗakinta ,alamar ta wuce taje ta sauya kayanta


Cikin takaici Bilƙis ta girgiza kai ,kawai ta saka kanta ɗakin ,ta ajiye jakar makarantar akan keken ɗinkinsu sannan ta sauya kayan ta zuwa na gida ,A gajiye tayi sallah ta kuma fitowa falon still wayar takeyi ,fuskarta sai blushing yake alamun tana tsananin jin nishaɗin wayar da take 


"Umma Abinci na" 

Tsaki ta doka sannan ta janye wayar a kunnenta da sauri ta matsa dashi can nesa da hannunta ,yanda baza aji maganarsu ta cikin wayar ba 


"Kedai bakida hankali wallahi kina ganin ina waya bazaki iya fita ki jirani in na gama kya dawo ba? To ki wuce wajen matar Audu abincinku nacan ,kuma kar in sake ganin ɗan ƙeyarki a ɗakina sai na gama waya " 


Tana rufe baki ta soka ƴar ƙaramar Torchlight phone ɗin ta a cikin ɗankwali a saitin kunnenta ,ta cigaba da wayarta "Sorry gentle man ,kasan mata with their commitment, now I'm all for you" 


Ɗan jim tayi sai kuma ta saki wani shu'umar dariya ta miƙe ta nufi firinjin ta ta ɗauko lemun ginger a Goran faro ta fara tuttula ma cikinta 


Cikin sanyin jiki Bilƙis ta fice wasu ƙwallan baƙin ciki sun taru sun cika mata kwamin ido 

"Wai da gaske ne mamana karuwa ce,ko kuwa kalar nata social life ɗin kenan? ...kai Innalillahi wainnailaihir rajiun" 


Raɓewa a bakin ƙofa tayi sam ta nemi yunwar cikinta ta rasa ,tana kallon sa'ointa sai tsula rashin kunyarsu suke a tsakar gida ,ita dai ba um ba uhmuhm,gabadaya halin mamanta ya sa ta zama mara kwarin gwuiwa ,tana tsoron shiga sa'ointa saboda gori.


3.17pm 

Hajiya Binta a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ,hannunta da mahucin kaba ,ta saɓe labulen akan ƙofa saboda iska ya shigo mata ,sai sannan ta gama wayarta na farali ,wanda inda sabo yaci zuwa yanzu Bilƙis ta saba dashi 


Ɗago ido Bilƙis tayi ,gamida kallon mamar Tata ,itama ita ɗin take kallo


"Shegiya daddage ki zama saniyar ware ,kin zo kin rakuɓe anan,ace ɗa baida karsashi a cikin sa'oinsa ? Zaki bar wajen nan ko sai nazo na ɓarar dake "


Cikin layi ta miƙe wani irin jiri na kwasarta 

Tana shiga ɗakin tayi arba da lemun ginger da uwar tasha ta aje,da sauri ta ɗauka ta kwankwaɗe ,sannan tayi baya ta faɗa kan kujera rikica ,wasu lafiyayyun hawaye suka fara mata sintiri a kunci 


Tsai da ranta Hajiya Binta tayi a take kuma taji ,damuwar ƴarta na damunta ,abunka da ɗa da mahaifi 


A sanyaye taje kujeran da take ta zauna ta jawo kanta ta ɗaura akan cinyarta tana goge mata ƙwallarta a hankali tana shafa mata gadon bayanta 


"Me gadon zinare ,waya taɓa mun ke ? Na kwana biyu rabon da inga murmushi a fuskarki meyasa ,kinaso ki jamun asaran ranki ne ehemm?"


Shiru tayi bata tamka mata ba ,saida ta cigaba da nacuwa ,kafin ta soma magana cikin shesheƙa 


"Umma wai ke ....wai ke ....wai ke karuwa ce" kawai saita tuske da wani irin firgitaccen kuka wanda yasa Hajiya Binta faɗuwar gaba ,a tsorace ta cillo mata tambaya


"Inji wani Algungumin Allahn?"


"Umma me ke kaiki gidan ladi police ? Ance da ita da mijinta basuda kamun kai ,umma nifa ƴar kice kinaso in rasa mijin aurene ace mamana fasiƙa....? Umma ya mu'allim ɗinmu yace zina bin jini take ,kullum inajin yina yiwa mazan ajinmu nasiha kar su yarda su auri ɗiyar lalataccen zuriya irin mu maaamaaa😭"


Sosai ta gama firgice mata da ihu sam ta kasa shawo kanta 


"Bilkisu ki nutsu ki saurareni ,Ni ba fasiƙa bace..." Da sauri ta katse ta 

"Amma kullum kina waya da maza da rana ku raba dare kuna waya da daddare da maza...a gidan mama ladi ku kulle ƙofa a bedroom ɗin ta kuna wani irin gunji ke da ita kamar muzurai ,umma me kuke yi eheee?"


"Balkisu dama samun ido kikayi haka ?"


"Umma ba samaki ido nayi ba wallahi kawai na girma ne ,shekara ta sha huɗu ,to karantar ki nayi kawai"


Wani wahalalllen Numfashi Hajiya Binta ta aje ta daɗe tana ɓoyewa yarinyar abinda ke faruwa ashe kallon kitsen akewa rogo


"Bilkisu Na yarda ki tuhumeni ,amma lokaci yayi da zan fayyace maki daga Ina matsalar take ,Ke macece babbar ɗiyata wanda watarana zaki zame mun Aminiya abokiyar kukana ....Bilkisu kome ya samu shamuwa watan bakwai yaja mata ...babanku baya bamu ci ,baya bamu sha ,baisan kuɗin makarantan ku ba....Daya bamu tiyan gero mu jiƙa muyi maku kunu ya gunmace yaje ya siyo ma dokinsa buhun dussa  ,komai naku ya barmun ,gashi inaso kuyi karatu ,Inaso kusa sutura mai kyau kamar na sauran yara masu uwa da uba .....Bilkisu ga matsatsin gidan yawa, Bani da sana'a ga sharrin kishiya ,ki faɗa mun taya zan tsira dani daku in ban nemi hanyar da zan samu kuɗi koda zan yasar da mutunci na ba ne indai ku zaku rayu ba?"


"Umma ki zina saboda ki bamu abinci? Kiyi zina saboda ki bamu kayan sawa ƙawa da za'a barta anan duniya ? Wanda Allah yayi alƙawarin bawa duk wani mutum abinci da abunsha da zai yi rayuwa saidai in ya raina ne ,misali mangoron gidan nan abincine in muka tsinka mukaci zamu koshi ,ruwan rijiya birgiman kwaɗi ruwane Allah bai ƙoronsa ba ko ina akwai shi in mukasha zamu rayu....kin zaɓi muci abinci da nama da kifi muci kpomo musha ruwan leda tayaya ,Allah bazai barmu da kanmu ba ?.....Umma kin taɓa Addu'a akan matsalar ki ? Amma kinje kina turamu islamiyyar da ake biyan 5k a wata ,idan kin samu makarantar zaure ba'a karatune? Kin saka mu Makarantar boko na dubu casain a wata uku ,idan kin samu makarantun gomnati ba'a karatune? Wait mama kijini don Allah da kuɗin zina fa kike biyan kuɗin makarantar  ilimin mu har kike tunanin zai mana albarka kuma ya Amfane mu dake a gaba?...kaicon wannan rayuwa tamu mara balance" 


Dafe kai tayi da sauri 


"Ilahu yau ake yinta ,Baƙar tukunya kenan mai fidda farar tuwo " Bata gama Ankarewa ba ,kawai saidai taga ta miƙe da sauri zata shige uwar ɗaki ,da sauri ta miƙe itama ,ta bi bayanta 


"Bilkisu ina zaki ?"

"Umma bakiji an kira sallah ne? Zanje in sallah in shirin Hadda kuma" 


"Yau Inaso ki fasa zuwa Haddan ki zauna muyi magana " kallonta tayi ƙur ,sai kuma tai saurin cire idonta akanta taje gaban dressing mirror ta jawo kujeransa ta zauna ,tana kallon Hajiya bintar 


A hankali ta nemi gefen gado ta zauna 


"Bilkisu ?"

Ɗagowa tayi ta kalleta ba tare da tace mata uffan ba


"Balkisu magana nikeso kiyi mun "


"Na'am umma"


"Balkisu Inaso daga yau ki fara sani a cikin Adduoinki ,Allah ya shiryeni Ni ummanki yasa in daina abunda nikeyi ,kawai tashi ki tafi makarantar ki"


"Umma kince da zamuyi magana in zauna in fasa zuwa"


Tsawa tayi mata ,a take idonta suka kaɗai wasu daskararrun hawaye da ta mance yaushe rabon da su sauka a kuncinta ,yau kumatunta ya fara masu maraba lale


"Ɗauki jakarki ki bar ɗakin nan nace ,tabbas balkis kin girma koda yau na mutu zaki iya riƙe kanki da ƙaninki ,kinsan fari da baƙi ,kin san hukuncin Allah ,zan barki ki taɓa rayuwar sufaye ,mu gani sufiya zaki zama ko kuwa waliyya ,fita!!!!" Ta ƙara jifarta da wani tsawan da ya fi na farkon tarwatsa zuciya .


 Da gudu ta ɗauki hijabin Haddarta ta yi waje ,yanzu kam ko hawayen ma babu a fuskarta ,sai tarin mamaki",Mai yasa umma kuka haka? Me ya tsinkar mata da kafaffiyar zuciyar nan Tata?" 


Wai wani iriyar gidane Wagga ?? Wanenne makama baban su Bilkisu mijin Hajiya Binta??

Anya yasan Halin da matarsa ke ciki kuwa???Mafarin wahala

MAKAMA....✍️


author-img
Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop

Comments

table of contents title