Main menu

Pages


 ______Sarautar Makama ,sarautace daɗaɗiya da ake ji da ita a masarautarmu.

Babana Malam Idris Hammad ya gaji sarautar daga hannun babansa kuma ya riƙe ta ƙaƙam da muhimmanci , Babana mutum ne da Allah ya zuba masa azaban Aure saki ,baya iya zama da mace ɗaya sai biyu kazalika bayida isassun ɗakunan da zai ajiye mace fiye da biyu ,wannan shine dalilin da yasa daga zaran ya ƙyalla ido yaga wata a waje tofa zai rori faɗa da ɗaya daga cikin matarsa ya samu ya sake ta don ya saka wata amaryar a ɗakinsa .

Babana bayida sana'ar ko saida minti ,da Albashin fada da take biyan duk wata hakimanta shima dashi ya dogara saikuwa in manya sunzo fada a bisu ɗuuuu da manyan babbar riga su samu a basu na cefane ,kalar rayuwarsa kenan....Ƴaƴan makama sunkai 32 Wanda duk yawancinsu ƴan ubane ,ma'ana basu da wanda suke ɗaki ɗaya kowacce da ta haife masa ɗaya zai saketa ya karɓe ɗan shi yadire a tsakar gidan ,a cewarsa yaransa basa Agolanci .

 Yinada manyan ƴaƴa zaratan maza sun kai  bakwai ,Babban cikinsu shine Ya Ibro ,shima mamansa ita kaɗai ta haifesa don haka yikewa kansa inkiya da nine shugaban ƴan ɗai ɗai,yina nufin cikin yaran babansa 


Ya Ibro shine kusan ya gado Halin babansa in yaga mace wandonsa har motsi zakiga yinayi , saidai ba kuɗin aure ,saidai soyayyar shan minti a ƙwaƙule yarinyar mutane a katanga ,Yinada baƙin ciki ,ƙyashi da Hassada ,sam bayaso wani daga cikin yaran gidan ya fishi ,don haka da yaga ka taso da haske ka kana ɗan sana'arka don ka samu kaci abinci ka huta da yunwar cikin gidan makama to tabbas zaije a maka Asiri 


Ya Ibro akwai fitinannen shishigi wannnan dalilin ne ya sashi kutsawa group ɗin Sadik sarki duk da kasancewarsa ɗan talaka ,kuma suma din moransu yake yayi ta haɗa fada yina samun kudi a kowani ɓangare. 


Kaf yaran makama ba wanda ya gama cikakken Sakandire ,zube suke a tsakar gida sai tsabagen rashin kunya ba A ba Alu .


Hajiya Binta ɗiyace ga Sarkin Dogarai ,Tun bikinta ƴan uwa duk sun ƙi auren amma ta kafe daɗi soyayya ,nan aka ɗakkota aka jefata a gidan yawa ,kuma gidan yunwa ci abunda kika aje. 

Tun sanda ta haifi Bilkisu take ganin rayuwa sai su kwana su wuni da yunwa ,tunda Batada sana'a ,tana samun sassauci wajen makama don itace kadai bai taba gigin sakinta ba,wannan ya ja mata baƙin jini ba a cikin gidanba harma da surukuwarta Bata sonta ,da ta hango Binta na wanke ² ko wani abu a tsakar gida zakiji tana sakin habaici


"Ehem ba ,an wanke gaba an ƙunzugu an basa yaci sai iskanci da tsiya ,Ni maganin mutum zanyi ba wacce zata tsaya mun a makoshi "


Ni Bilki naga Rayuwa Mamana ma ta ganta ,ina shekara uku mamana ta daukeni ta kaini makarantan kudi ,kullum zataje ta kaini ta daukoni har na isa zuwa da kaina ,zamu zauna da yunwa kudin makaranta ko a koroni sama da sau biyar mama na mayar dani tana bada haƙuri kafin ta sama rabin kudi tai masu depositing to balance later ,shikenan karshenta a yafe mata ,kowa ya tsaneni Ni dai bilki har tsoffin kakanninmu mazan gidan ,acewar kowa an dage sai nayi boko ko wa zanzo infi oho.


Bana mantawa idan na dawo daga makaranta tun a dakali za aita tsayar dani ana mun tambayoyin ƙure wanda ansan yafi ƙarfin ƙwaƙwalwata ,amma dayike ilimi baiwace haka zan bawa Kowa mamaki wajen amsawa ,saboda babu yabon kai inada basira 


A makaranta kuwa indai za'a tsamo yaranda sukafi kowa ƙazanta da spring ɗin wando da mugayen faci a uniform to ni Bilkisu Idris Makama nice queen dinsu ,wata zubin a dakeni ,wata zubin asa yara suyi mun dariya da ehoooo.

Tun ina kuka ina dawowa ina cema mama na daina zuwa ina ɗaga mata hankali daga baya na dawo na gane mama tana matuƙar ƙoƙari a kaina Batada kudin dinka mun uniform 

Daga nan na zama fitinanniyar kaina kina mun dariya aka tashi zamuyi dambe in maki duka ,a gida ma na koma laluwa masifa komun girmanka ka zagin mun mama saina rama mata,don haka kullum bakina a kumbure time saboda shan duka ,kuma mama bata fitowa bare ta tare mun,innaje ɗaki a wata sa'in nikan dinga mata ƙunƙunai 


"Kina kallo kowa yina fitowa yina tare ma ɗansa ,amma ke sai ki ƙi duk sun raina mu,saidai innashigo ɗaki ina kuka kice mun Allah ya kara,kuma wallahi bazan raga masu ba"


Itadai saidai ta bini da ido wata zubin kuma ta bani hakuri.


Inason iyayena saidai Babana maƙetacine ,duk yawan gidanmu kudin cefane dubu daya da dari biyar ne cin safe rana da dare ,don haka ci daya akeyi a gidan sauran zangon yinin kowa ya nemi abinda zai ci.


Akwai watarana mamana itace da girki ,tun safe ta masa maganan kudin cefane ,nan ya zaro kyallen Aljihun wandonsa ya fiddo mata su waje 


"Kin gani ko ? Babu ne fatsima da akwai da na baku,ki basu hakuri kowa yasha ruwa aita salati ,zan fita inna roro zaki ganni "


Girgiza kai kurum tayi ta koma ta zauna ,tana kallo yasa kai yayi ficewarsa 


Nikam dake gefe ina Home work (Aikin gida) ina sauraronsu amma bance komai ba ,saida baban zai fitane na ɗago kai na kallesa


"Baba Allah ya tsare ,Allah ya bani kudi in siya maka mota da ummana in siyan mana buhun abinci muci mu daina kukan yunwa muma "


Ɗan tsam yaji a ransa amma da shike mugune sai ya ɗage kansa sama yayi ficewarsa 


Wasu ƙwallane mama ta yi saurin gogewa da bayan hannunta Ni banma lura ba na cigaba da rubutuna ina en waƙe²n da ake mana a wajen PE .


"Mamana zokije gidan Hajiya ladi kice mata wai nace in akwai sukolau ɗin wankin ta kawo" 


Turo baki nayi na mike na yarda fensiri ɗina a ƙasa 


"Umma Ni banso kina turani anso wankau ana mun wulakanci ,en makarantan mu suna mun gori wai mamana ke masu wanki ana biyanta kudi"


Kamo Ni tayi a hankali ta rungume Ni ,tana hadiye wani irin azababben ƙwalla ,yina komawa yina daskare mata a Ƙirji 


"Laifi na ne da na zaɓa maku ,wannan Rayuwar amma zan nemo mana canji da izinin Allah,kije kinji...ko kinaso mu mutu da yunwa burinki na zama likita bazai cikaba?" 


Murmushine ya suɓuce mun,saboda farinciki 


"To umma ai zanje "


****

Ban daɗe ba na kawo mata ɗimin wanki a kaina ,da kuɗin sabulu ɗari biyar .


Ummana wani sassanyar ajiyar numfashi ta aje ta karɓa kuɗin da sauri,ta kwanto haɓar zani ta ciro mun wasu kanannaɗaɗun canji na ₦80


"Maza siyo mana garin kwakin hamsin ,kullin ashirin maggin goma karfa ki tsaya wasa ko ki dawo kice kudin ya fadi ,ki sauri"


Yankan layi nayi ina tafe ina nanata aiken mamana saboda kar in manta 


"Kwakin hamsin ,ƙulin Ashirin maggin goma..." 


Ɗif na ɗauke wuta ganin Baba a teburin iliya mai shayi ya saki timbi kai da tsibeben rawani ,yana kwasan tea da bread da masan indomie da kwai ,suna hira ana ɓaɓɓakan dariya 


Da gudu na runtuma wajen sa ,naje bayansa na tsaya 


"Aah Zinaru ya dai ? Ina zaki ba na hana fita yawo ba?"


Kallonsa nayi cikin rashin wayo da wauta

"Baba ba yanzu ka fito da Aljihun wandonka ba, ba kada ko sisi ba ,kacema umma ta bamu hakuri mu zauna da yunwa ,shine kai kazo wajen iliya ya baka bashin shayi da biredi?"


 Sosai yaji ya wani irin bala'in muzanta cikin mutanen da tunɗazu yike damunsu da surutu da ƙarya 

Nikam ko sanin halin da ya shiga ma banyi ba na juya na kalli Iliya me tea


"Ɗan Iliya baka da kirki yanzu Babana yazo ka bashi ,bashin shayi da kwai Amma in da ummana ne ta aikoni bashin ruwan bunu da daddare sai ka hanamu ko?..."


Wani wawan tsawa Babana  ya doka mun


"Kin wuce ko saina sassaɓa maki?,Ina zaki?"

"Mamana ne bayan ta aikeni gaidan matan ɗan sanda na anso sukolau ,shine ta cire kuɗin ta bamu mu siyo uhmmm mene ma?(na tsaya Ina bubbuga kai) yawwa na tuno😁 Garin rogon hamsin ,ƙulin Ashirin ..." 


Dakatar dani yayi yina ya isah ya isa ,amma ina saida na ƙarasa ƙarshen aikena


"Maggin goma"

Aiko kofin shayiya ɗauka ya watso mun na kuwa ƙalƙala da gudu ina haki


Zabu zabu ya tashi ,ya bar sauran shayin dasu indomien ya sallami ɗan iliya ya basa kuɗinsa ya wuce yina sababi


"Iyaye mata ba ƙana'a kaba mace wadataccen kudin cefane amma da sanyi safe ta aike yarinya siya garin rogo? Wato za ayi adashi da kuɗin ko? Zanje in sameku "


Kowa a wajen caɓe baki yayi ,wasu kuma suna guntse dariya ,don sunajin labarin gidansa a bakin matayensu .


******

Rayuwa juyi juyi ce ,yau dai gashi na fara tasawa ,har na ƙare makarantar firamare ,rashin ji sai abinda yayi gaba ,saidai na fara gane halin da uwata ke ciki don haka ina tsananin tausaya mata .


Bayan na kammala primary ne kukan mama ya karu ba tada aikin yi ,ba abinci ba kuɗin kashewa balle ta samu kudin kaini makarantan gaba da sakandire,na sama admission kyauta saboda kokarina a makarantan da ragin dubu goma a cikin kudin makarantan mu amma ,ina Batada inda zata nemo mun kudin uniform,safa,jaka ,harma da tsibin kudin littafai 


Don haka na fara shiga makota ina koyon ɗinki wajen wata maƙociyarmu ,itakuma dai still mama sai fafata sukolau take tana zubawa a katin adashi sauran kuɗin muci abinci .


Akwai wata rana mama ta ida wankin gidan matar ɗan sanda ,muna zaune tana ninke kayan ina tayata ,daidai nan wani Almajiri ya kwaɗa sallama ,da gudu naje na ɗage labule tare da tamabayar "waye"


"Wai Hajiya Ladi ne tace in ba damuwa Binta me wanki tazo"


Zazzare masa ido nayi na shiga tsiya


"Kai mamana din kake kira Binta me wanki" kunsan dai Almajirai in sun sama waje .


"To ba wankin takeyi ana biyanta ba ,shegiya me suffan er ruwa "


"Kam kam kam ,nadaiji mun gode Allah tun da uwata tana gidanmu tana kula damu kaifa ,uwarka bata tausayinka ta kawo ka almajiranci kana Bara da ɗebo ma mutane ruwa "


"Habawa yarinya bar ganin a gidanku nake zan iya jawoki in kila banza , ke kinga ko bara muna zuwa gidanku ? Shegu mitsiyata ,mutanenda har yayyunku sun fara ɗan tari saboda yunwa wazaizo Bara babanku ya koreshi da bulala saboda matsolanci irin na ubanku ..." 


Ɗaura hannu nayi aka na fashe da ihu wai yaci mutuncin Baba ,ai kafin ayi haka yaran gida sun fara tuttuɗowa kaman zuma suka bishi hanyar zaure karce,ina binsu a baya nima da gudu ina labarta masu abinda yace 


Duhun zauren ya sa ɗan Almajirinka ya dinga ƙumewa da garuka,mukuwa yaran gidan da mun daɗe da hardace hanya ,tar muke gani haka muke binshi da gudu ,yina fita waje ko kallan hanya baiyiba ya tsallaka titi da gudu aiko keken wani tsoho ta ɗaga shi ta Nana a kwalta


Ehoooo muka ɗauka ,muna Allah shi ƙara ,Allah ya mana maganinshi 

Ba wanda yabi ta kanmu haka akayi kan ɗan Almajirin don babu wanda baisan halin rashin tarbiyyan en gidanmu ba 


Mamana kam tana gama haɗa wankin ta saɓa mayafi ta shiga gidan ,saboda tsananin matsuwarta da A biyata kudin wankinta suci abinci tsabar yunwa har jiri take gani 


A bakin ƙwar gida muka haɗe ,da sauri ta damƙi hannuna ta saka mun ɗan makullin kwaɗon ɗakinmu


"Ina gidan matar ɗan sanda yanzu ki biyoni da kayan su"


*****

Gidane ɗan madaidaici mai cin mota ɗaya sai mai gadi .


Saida tayi sallama kusan sau uku kafin aka amsa daga ciki ,tsayuwar minti biyar kafin aka amsa da "A shigo,waye"


"Hajiya me wankine wai kina kirana"


"Shigo " aka kuma amsawa ,wani sallamar ta daɗa saki sannan ta danna kai ɗakin 


Turus tayi ganin mace ƙosashiya ma'abociyar manyan kuturai da Jiga²n Na shanu ɗaure da Tafkeken towel ɗin wanka da ya saukar mata har ƙasa kamar zani ,ba birexiya a jikinta tayi sakawa sakwa da ɗaurin ƙirjin da tayi da towel ɗin ana ganin kusan duk nonuwanta.....gefen kujeran da take ,wani bijiras ɗin Yarone da gani kaga bagidaje wanda bazai wuce shekaru 26 ba sai sunkuyar da kai yike ,yina satar kallon Hajiya Ladin


Nuna mata wajen zama tayi ,a ɗarare ta zauna ta fara jero mata gaisuwa 


Gyaran murya tayi 

"Malam Binta kike ko?"


"Eh haƙƙun Binta nike"


"Yawwa dama Kukuna mai dafa mun abinci ne ya yi tafiya so, ina neman me mun girki na wucin gadi kafin ya dawo ,ina ciyar dashi in masa sutura da sallah ,Albashinsa a wata kuma dubu ashirin da biyar . ..shine nace ko kinada ra'ayi ? zan maki kwatankwacin kudinsa ba canji , tunda Na dade da jin labarin halin talaucin gidanki kinga nan bakida matsalar abinci ...... (Jan fasali tayi taji ko ummana zatayi magana amma tayi shiru) ko da matsala?"


"Ehto Hajiya Nagode amma kinsan sha'anin mazan mu ,zanje in tambayi mijina in ya amince zaki ganni "


"To ba matsala ,Ɗallami kawo mata ruwa mana"


"A'ah wallahi Hajiya dama kin barshi ,Na aza wankinki ne ma kikaji shiru ,gayican nasa yarinyata ta kawo maki"


"Aah Ni banson ƙauyanci ki saki jiki dani ki ɗauka nan gidanki ne ,ɗallami kawo ruwa man " 

Ta ƙare tana ɗage ƙafa ɗaya ta ɗaura a hannun kujera ta saki wawan zama  


Kamar zai faɗa mata haka ya raɓa ya wuce ,itadai Binta Banda ƴar murmushi da nonnoƙe kai ba Abinda takeyi kamar mahaukaciya sabon kamu. 


Da gudun ƙarshe na tankaɗo ƙofar ɗakin na shigo na jibge kayan a tsakiyar center carpet ɗin wajen 


"Wayyo Allah na kuru da sun watsar mun da haƙora" na ƙare magana ina haki na wanda yaci gudu ya ƙoshi


"Amma kedai yarinyar nan sam zamanki gida bai ƙareki da komai ba sai rashin ji ,ina lura dake tunda kukayi common entrance shikenan kika shiririce ,Allah ka bani kudi watan nan zaki fara zuwa makaranta inshallah ,Ki gaisheta ki Bata hakurin shigowa daki ba sallama"


Ƙurrrr tabi mu duka da ido ,nikuma na sulale ƙasa na sunkuyar da kai 


"Yi haƙuri"

"Bakomai.......ammm me yafaru da makaray nata?"


Nan mama ta tsinke da bada labarin komai na makaranta na ,ta ɗaura da cewa 


"Amma yanzu in kika ɗaukeni aikin nan kinga ai sauki ya ƙara samuwa "


"Nawane kuɗin?"

"Hhmmm dubu tamanin da bakwai komai da komai"


Ko damuwa Hajiya Binta batayi ba ,ta miƙe cak ta shige wani ɗaki wanda yafi kama da ya zama bedroom dinta ne ,jimawa kadan sai gata da rafan ƴan 500# guda biyu


"Gashi wannan dubu ɗari ne ,aje a sakata a makaranta ....Amma fa da sharaɗi rance na baki zaki biyani dubu tamanin da bakwai sauran a siyama yar makaranta indomie da Alawa"


Hannun mama ɓari ya shiga yi da ƙyar ta karɓa ,amma itakam ilahirin idon Hajiya ladi na cikin rigar ummana tana kallon nonuwanta da suka ɗan zamo cikin riga , sakamakon mayafinta da ya ɗan zame tsabagen godiya 


Da ƙyar ta iya cire idonta akanta ta haɗiye wani kakkauran miyau "maƙururut!!"


"Bakomai yiwa kaine ,sai na jiku...." 

author-img
Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop

Comments

table of contents title