Main menu

Pages

FARATAN ZAKI chapter 10 - birnin Burkatul aswad 2

FARATAN ZAKI chapter 10 – birnin Burkatul aswad 2

  • FARATAN ZAKI
  • Chapter 10
  • Littafin Shuraihu Usman
  • Website Chapter

.

Bayan da muzaffar ya gama jin wannan labari daga bakin aljani maruful halfi sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce “amma ko wayannan mutane suna da babban sha’ani, ya maruful halfi dafatan dai shingen nan nasu bazai hanamu shiga birnin ba” Aljani maruful halfi yayi murmushi bayan daya ji tambayar barde muzaffar ya ce “ai shi shingen yana kare duk wani mutum daya zo da mummunar nufaka ne ga shiga birnin, in muddin ya kasance da mummunar nufaka ne kake son shiga birnin to fa shingen bazai taba bari ka shiga ba”

bayan da muzaffar yaji haka sai yai shiru bai kuma cewa komai ba har dai suka fara hango ganuwar birnin, cikin kankanin lokaci suka isa dab da birnin aljani maruful halfi ya sauka kasa sannan ya rikide ya zama saurayi, nan suka nufi kofar birnin.

koda isowarsu bakin kofar masu gadin kofa suka tambayesu daga ina Aljani maruful halfi ya sanar da su cewa su matafiya ne sun fito neman wani mutum ne mai suna Abu shammata. yayin da masu gadin kofar nan sukaji Saurayi Maruful halfi ya ambaci sunan Abu shammata sai suka kamu da mamaki, sannan daya daga cikinsu ya ce “ai kuwa yau karshen tafiyar ku ta zo, domin kuwa a wannan birni ne Abu shammata yake da zama, kuma shi ya kasance babban malami ne masanin addinin islama. kuna iya shiga cikin salama”

Aljani maruful halfi yayi musu godiya sannan suka shige cikin birnin yana mai yiwa muzaffar murmushi, muzaffar ya tsinkayi birnin burkatul aswad daban da birninsu ta dumbazur sihir, domin kuwa su birninsu na dauke da manyan gine masu benaye, amma cikin wannan birni sai yaga gidaje madaidaita kuma dukka gidajen na kamanceceniya, domin komai na gidajen birnin iri dayane, har da kuwa fentin gidajen. babu abunda ya kara baiwa muzaffar mamaki face gani da yayi wani tajiri ya fito daga gidansa a tare da shi ga bayi da rakuma dauke da laftu, nan da nan ya tambayi aljani maruful halfi game da wannan al’amari.

aljani yace “ai su mutanen wannan birni basa nuna wariya tsakanin talaka da tajiri, dukkansu daya ne wanda ya fi wani a cikinsu shine wanda yafi bautar ubangijinsu, shi yasa ma duk birnin nan ake matukar girmama abu shammata, kuma koda ace kafi kowa kudi a wannan birni to gidanka bazai taba banbanta da ta talaka ba, yi duba izuwa ga wancan tajirin daya fito daga gidansa ka duba irin arzikinsa, ga shi dauke da bayi da barori, ga jakuna da rakuma dukkansu dauke da laftu, duk birnin nan babu wanda ya ko taka kafarsa a arziki amma dubi gidan dayake ciki iri dayane sak da irin gidajen talakawan garin nan, kuma ma abun burgewan shine shi attajiri Abdurrazak ya kasance dukiyarsa bata tsone masa ido ba,duk wannan dukiya daya tara gajiyayyu ne da talakawa ke mora domin kuwa kusan talakawan birnin nan gaba daya shi ke biyan musu haraji”

Muzaffar ya jinjina wannnan lamari ya ce “amma kuwa wayannan mutane suna da ababen al’ajabi gaskiya sun burgeni matuka gaya,”

“su haka suke rayuwarsu babu ruwansu da tashin hankali, kuma duk sa’in da wani bako yazo garesu zaka samu yana yaban halinsu, domin kuwa suna kyautatawa baki fiye da yadda mutum ke tunani”

suna cikin tafiyar ne suka iso kasuwar birnin zanan ma muzaffar ya cigaba da kallin yadda salon mutanen birnin burkatul aswad yake, da kuma yadda suke gudanar da tsarin rayuwarsu kawai sai yaji sun burgeshi harma yana sha’awar kasancewa da su, yana a cikin wannan haline ya dubi aljani maruful halfi ya ce “to yanzu ina muka nufa” Aljani maruful halfi ya ce “gidan malam Abu shammata ” daga nan suka dau hanyar gidan malam abu shammata.

da isowarsu kofar gidan suka iske gidan ya futa daban da sauran gidajen birnin, domin kuwa yafi sauran girma da fadi, sannan ga tangamemen masallaci a jikin gidan, gefe guda kuma yarane yan kananu yan shekaru goma zuwa sha daya ke zazzaune suna karatun littafin annabi ibrahim cikin zazzakar murya, muzaffar ya bisu da kallo cikin sha’awa yana ayyanawa a ransa kan me suke karantawa aiko tamkar aljani maruful halfi ya shiga zuciyarsa sia jinsa yayi ya ce “wannan littafi da ka ga yarannan na karantawa shine littafin da ubangijinsu ya saukar musu da shi”

suka shige cikin gidan inda suka iske Malam abu shammata zaune mutane sun zagayeshi, shidai malam abu shammata ya kasance dattijo dan kimanin shekaru 70, yana sanye da fararen kaya da rawani, koda ya hango su muzaffar sai yayiwa dukkan mutanen dake tare dashi inkiya da hannu akan su dan bashi wuri, sannan ya yafito su aljani maruful halfi da hannu.

Bayan da Aljani muruful halfi da muzaffar suka isa ga malam abu shammata suka zazzauna sai ya dubesu ya ce “maraba da zuwa birnin burkatul aswad ya barde muzaffar da aljani maruful halfi”

muzaffar yai mamaki da yadda akai wannan dattijo yasan sunansa, dattijo abu shammata ya kuma cewa “kada ku damu da yadda akai nasan sunayenku, jiya ubangiji ya sanar dani dukkan al’amuranku cikin barcina, nagani cewa kai kana son mallakar taswirar kogon zakuna da yanzu haka yake rataye a wuyan sarauniyarmu, kai sani cewa a baya wani boka yai kokarin kwatar taswirar nan daga hannun sarauniyarmu amma bai samu nasara ba sakamakon bayyanar wani aljani daga cikin Aljanun dake hidimtawa taswirar, tun daga wannan lokaci sarauniya badariyya ta killace yarta gimbiya zatal dawahi, to bayan kwanaki uku da faruwar wannan al’amari sai aljanin dake hidimtawa taswirar nan wanda ya kasance ya hidimtawa Attajiri almadud a zamanin sa ya kuma bayyana, bayan da Aljani Harijul burkatu ya bayyana a tsakiyar fada, a gaban sarauniya da kuma yarta zatal dawahi. koda sarauniya badariyya taga wannan aljani sai ta tunashi, Aljanin ya kwashi gaisuwa gareta sannan ya fara bayani kamar haka ” ya shugabata a baya na sanar dake wannan taswira dana baki shi zai jagoranceki ga bigiren da kakanki attajiri almadud ya adanta dumbin dukiyarsa da babu wani mahaluki da ya keda kwatankwacinsa cikin duniyar nan, ki sani cewa yanzu haka manyan bokaye, da sarakuna sun samu labarin bayyanar tasiwar nan gareki a sabida haka zasuyi ta kokarin ganin sun rabaki da taswirar. Da yawa daga cikin jama’ar Aljanu da mutane sun rasa rayukansu bisa tafarkin neman dukiyar attajiri almadud, kuma da yawa suna shirye da su fuskanci kowacce iriyar waki’a don mallakar dukiyar. kuma shingen birninku bazai iya kareku daga manyan bokaye irinsu boka dundamu ba.

bisa binciken da nayi na gano cewa a yanzu duk duniya babu wani barde ko jarumin daya isa yai miki rakiya izuwa bigiren da dukiyar ke adance face wani jarumi da akewa lakabi da muzaffar ibn azlam, shi wannan jarumi zai zo garemu don biyan bukatarsa shima yana bidar taswirar dake wuyan yarki zatal dawahi, sai dai shi burinsa dabanne don ba dukiyar nan yake kokarin mallaka ba, burinsa ya isa ga Kogon zakuna ya kashe sarkin zakuna ya ciri farcensa, domin sana’anta maganin da zai warkar da amininsa daga cutar shanyewar barin jiki data sameshi. duk duniya a yanzu babu wani magani ga wannan cuta face farcen sarkin zakuna, bisa ga hakane muzaffar ya baro birninsu ta marhabur sihiri dake can alkaryar dumbazur sihir alkaryar da ke dauke da manyan manyan matsafa da bokayen duniya. aduk lokacin da saurayin nan yazo gareku to ku tarbeshi cikin girmamawa, sannan ku sanar da shi bukatarku “

bayan da sarauniya badariyya ta gama jin bayanan aljani harijul burkati sai ta mike tsaye ta ce da aljanin ” sam bana bukatar wannan dukiya domin kuwa ko dama na mallaketa babu abunda zan da ita, itafa wannan dukiya da kake magana akai, tayi sanadin halakar rayuka da dama to abisa wani dalili ni zanyi kokarin mallakarta. a sabida haka ka amshi taswirar kogon ka tafi da ita”

Aljani harijul burkati ya nunfasa ya ce “ai wannan dukiya taki ce, kuma ki sani koda ace kin ki amsar dukiyar ko kuma ki ka ki tafiya daukota to manyan bokaye da sarakunan kafurai zasu yi ta kawo muku hari don ganin sun kashe diyarki zatal dawahi sun sana’anta wani aikin sihiri da zai basu daman zuke jinin jikinta suyi amfani da shi wurin isa kogon zakuna,” Aljanin na zuwa nan a jawabinsa ya bace daga fadar.

Sarauniya badariyya ta sanya aka yi kirana ta umarceni da na buga kasa naga yaushe wannan saurayi da Aljani harijul burkati ya sanar da ita zai zo wannan kasa tamu, nan da nan na baje rairayi na zana alkalumman hisabi, nagani bisa rairayi cewa cikin wata mai kamawa zaka iso kuma nan wurina zaka fara zuwa, koda na fadawa sarauniya badariyya hakan. sai ta umarceni da duk sa’adda kazo na sanar dakai bukatarmu gareka sannan nai maka jagora izuwa gareta”

.

bayan da muzaffar da aljani maruful halfi suka saurari bayanin dattijo abu shammata, sai suka aminta da zantukansa, nan da nan suka nufi fada.

suna isa fadar muzaffar da aljani maruful halfi suka cigaba da karewa fadar kallo, ita dai wannan fada an ginata ne da dutsi mai daraja dangin jauhari da zubarjadi, akai mata dabe da zinare, sannan akai wani ado a kasan tsakiyar fadar da lu’u lu’u yadda ya bada taswirar tsuntsu, A karshen fadar kuwa tangamemen karagar sarautace da aka sana’anta da zinare, akayi masa ado da takubba, suma takubban aka lillika musu lu’u lu’u a marikinsu tayadda suke daukan idanu.

Sarauniya badariyya ce bisa kan wannan karagar, yarta gimbiya zatal dawahi na daga gefen damanta,waziri na daga gefen hagunta.

sauran yan majalisu na zazzaune bisa kujerun alfarma sun fuskanci junansu.

ai koda jarumi muzaffar yai arba da gimbiya zatal dawahi sai ya kasantu cikin rudu da mamaki na tsananin kyawunta, ya kura mata idanu baya ko kiftawa, har suka karisa gaban sarauniya badariyya idanun muzaffar na kan gimbiya zatal dawahi.

ita dai gimbiya zatal dawahi ta kasance kyakkyawar gaske, ta mallaki dogon fuska mai dauke da madaidaitan dara daran idanu, hakanan tana dauke da dogon karan hanci da tsukakken bakinta ke kasansa, fasalta suffar gimbiya zatal dawahi cikin wannan kankanin littafi ma bata lokaci ne.

a wannan lokaci gimbiya zatal dawahi ta yi shiga da ado irin na gidan sarautar kasar Hindu, ta maye ga fuskarta da jikinta da sarkokin zinare sai kyalkyali suke.

yayinda zatal dawahi taga kallon da muzaffar ke yi mata yayi yawa sai ta dukar da kanta kasa.

adaidai wannan lokaci ne muzaffar ya dawo hayyacinsa ya tuna a inda yake, nan da nan ya duka shida Aljani maruful halfi da Malam abu shammata suka kwashi gaisuwa ga sarauniya badariyya, bayan sarauniya ta amsa akai musu izni da su zazzauna, suka samu wuri suka zauna sarauniya ta numfasa ta ce “yakai wannan jarumi hakika al’amarinka ya bayyana garenu tun kafin zuwanka, ka fito gida don nema wa dan uwanka magani a bisa lalurar dake damunsa, lallai zamu taimakeka ka isa kogon zakuna ka cimma burinka amma a bisa sharadi guda biyu.”

koda muzaffar yaji batun sarauniya badariyya sai yai shiru yana tunani kafin ya dago kansa ya ce “yake wannan sarauniya mai babban sha’ani, fadi sharuddan na ki, zaki sameni mai kiyayewa”

sarauniya badariyya ta ce “sharadi na farko shine, muddin kana son mu taimakeka to muma zaka taimakemu yayin wannan tafiya, zamuyi tafiyar nan a tare har mu isa can Kogon zakuna, sharadi na biyu shine sam bana son wani abu ya hadaka da ‘yata gimbiya zatal dawahi koda kuwa magana ce, muddin zaka iya kiyaye wayannan sharuddan to a shirye muke da mu taimake ka”

bayanda muzaffar ya idda sauraren sharuddan Sarauniya badariyya sai yai na’am sa su ya dubeta ya ce “na amince da dukkan sharuddan ki kuma zaki sameni mai kiyayewa garesu”

nan da nan sarauniya badariyya ta dubi sarkin gida idrisu ta ce “ya idrisu maza ku shiga da wayannan baki namu ku basu masauki gibe zamu shirya mu yi wannan tafiya a tare” sarkin gida idrisa ya duka ya ce “naji kuma nabi ya shugabata” yana gama fadin hakan yaiwa su Muzaffar jagora izuwa masaukinsu

Washe gari muzaffar da Aljani Maruful halfi suka fito fada inda suka iske cincirindon jama’a sun cika fadar daga, bayan zuwansu da dakiku tamanin sai aka fara jin bushin algaita wanda ke tabbatar da zuwan sarauniya badariya da gimbiya zatal dawahi

http://fb.me/shuraih.usman

Comments

table of contents title