FARATAN ZAKI chapter 5 Littafin yaki
FARATAN ZAKI
Littafin Shuraih Usman
Tel. +2348140419490
Chapter 5.
Kusani
Ku sani: wannan littafin na kudi ne sai dai daga chapter 1 zuwa 10 kyauta ne, zan ruga kawo muku duk bayan kwanaki uku, da zarar mun kai chapter 10, chapter 11 zuwa cigaban littafin zai ruga zuwa ne a shafinmu bayan kwanaki biyu, amma duk chapter guda daya akwai farshinsa. In kuma ya kasance ba zaka iya siyan chapter ba, to zaka iya hakuri duk ranar asabar insha Allahu zamu riga dorawa a nan facebook don ku, amma in ka kagauta to sai kaje shafinmu ka siya duk chapter guda zamu saka farashinsa akan naira hamsin ko naira talatin.
FARATAN ZAKI chapter 5 Littafin yaki
in baku manta ba a babin daya gabata mun tsaya ne a inda sarki huntaru ya fice daga turakar ya bar muzaffar cikin tunanin ta yadda zai sadu da Tasiwarar kogon zakuna don isa can kogon ya yaki sarkin zakuna ya ciro farcensa ya kawo aiwa dan uwansa magani…
Cigaba – Faratan zaki
anan muka tsaya kuma yanzu zamu cigaba. to bayan fitar sarki huntaru muzaffar sai ya tsinci kansa cikin kogin tunanin yadda zai isa birnin burkatul aswad ya sadu da zatal dawahi
ya amshe Layar dake wuyanta, gashi kuma Sarki huntaru ya sanar da shi babu mahalukin da ya isa ya taba taswirar kogon zakuna in ba jinin almadud ba. nan fa ya shiga kullawa yana kwancewa har gabannin sa’o’i biyu.
daga karshe ya yanke shawarar ya kwanta yai barci in ya so gobe ya san dabarar yi, bayan muzaffar ya kwanta sai barci ya kaura daga idanuwansa sakamakon masifaffen yunwar dake cinsa ya mike zaune ya kai duba ga abincin dake gefensa.
Kuna iya karanta littafin FARATAN ZAKI littafi na daya 1 complete hausa novel
ya sake tunawa da kashedin da dattijo yai masa, ya koma ya kwanta can ya kuma mikewa ya sake duban abincin nan cikinsa ta sake murdawa, nan ya yanke duk abunda zai faru sai dai ya faru amma shi sai ya ci abincin nan, imma mutuwar zaiyi to ya mutu a koshe, yafi da yunwa ta kasheshi.
ya mike ya tafi gaban abincin nan ya soma ci cikin Annushwa sai da ya gama cin abincin ya wanke hannunshi baiji komai a jikinsa ba ya ayyana a zuciyarsa dattijon can yai masa karya gashi yaci abincin amma baiji komai jikinsa ha nufi luntsumemiyar katifar dake dakin ya kwanta ya bingire da barci.
washe gari koda ya farka sai ya tsinci kansa a daddaure cikin sarka, ya yunkura ya kwace daga daurin da akai masa amma ya kasa yana cikin wannan hali ne sarki huntaru ya bayyana a gabansa yana mai kyalkyalewa da dariya.
sarki huntaru ya ce “kai namijin gaske, hakika kaine mutum na farko da yaso ya ratsewa sharrina, amma baka samu dama ba to ka saurareni. wannan burin naka na son mallakar Taswirar Kogon zakuna nima shine burina, asalima nine boka dundamu.
bayan dana gama bincike ga hallarar tsafina na gano babu tayadda zan iya kwatar layan dake wuyan zatal dawahi sai na kasance jinin Almadud, sai na kara shiga wani binciken ta hanya daban, in da anan na gano zan iya kasancewa jinin attajiri almadud wato jinina ya zamto irin nasa amma sai na sha jinin bil’adama dubu sannan zan iya zamtowa ire-iren sa tun daga wannan rana na zo wannan daji na kafa birnin nan ina tare fatake da mahaya gamida da duk wanda tsautsayi ta ratso da shi ta cikin birnin nan ina halaka shi ta hanyar sanya guba a abinci.
Sai da na halaka bi’adama dari takwas da hamsin da biyar, na sha jininsu kuma a yanzu zan cika na hamsin da shida da jininka.”.
Kuna iya downloading fina-finan indiyan hausa kyauta ta a shafinmu na https://hothausamovies.com
sarki huntaru ya sake kyalkyalewa da dariya a karo na biyu, sannan ya bace bat daga gaban muzaffar, nan take nadama ya zowa muzaffar bisa cin abincin birnin lamfur da dattijo ya haneshi, yana a cikin wannan tunanin ne idanuwansa suka kai ga wani dan karamin allura dake kusa da shi, yai ja da gindi ya isa ga allurar ya dauka ya sanya cikin kwadon da aka kulle sarkokin da suka daureshi yana mai murmurzawa cikin sa’a kuwa sai kwadon ya bude, Muzaffar ya mike tsaye yana mai karewa dakin daya ke ciki kallo. sai a sannan ya gane cewa a magarkama ya ke. ya dumfari kofar magarkamar ya tura ya jita a kulle, yayi kururuwa ya take kofar da kafa kofar ta karye ta fadi gefe.
ya fito daga magarkamar yana huci tamkar zakanyar da aka kwashewa ‘ya ‘ya, koda dakarun dake tsaron magarkamar suka ga muzaffar ya fito sai suka nufoshi hannuwansu ruke da takubba.
muzaffar yai dubi dama da hagu baiga wani makami da zai kare kanshi ba, sai ya shigesu hakanan hannunsa babu komai. dakarun suka tsayu suna masu kaimasa munanan sara da suka shi ko ya wanzu yana kaucewa gamida zillewa kaifin makamansu. kuma lokaci lokaci yakan farmakesu da naushi ko mangari amma basa faduwa saboda taurin rai irin na dakarun.
ana cikin dambarwar ne muzaffar ya daga wani kato ya buga da kasa ya bishi ya turmushe da naushi, ya kwace takobin katon ya kifu ga dakarun nan yana sara da sukansu suna zubewa kasa tamkar manobi na sassabe a gona, kace shi ifiritu ne ko bakin aljani.
koda dakarun suka fahimci muguwar barnar da muzaffar yai musu sukai dubi ga rabin mutanensu da suka kwanta dama, ai sai suka zubda makamansu suka arce. muzaffar ya fice daga magarkamar dake a bayan gari.
shiko al’amarin boka dundamu bayan daya samu nasarar kama Jarumi muzaffar ya ajjiyeshi a kurkuku ya sanya dakaru sama da dari uku suyi gadinshi sai ya isa turakarsa yana mai kyakyata dariyar kyeta. yana yiwa kansa kirari yana ce wa “Ni ne boka dundamu ibn Murzalush shabu, nayi rantsuwa da burina, gamida sihirina sai na sha daga jinin mutane dubu na zamto jinin almadud la budda kuma sai na isa ga kogon zakuna na mallaki dukiyar attajiri almadud daya taskance, duk wata halittar datai yunkurin shiga tsakanina da burina walau mutum ko aljan to sai na kauta daga ban kasa”.
yana zuwa nan a zancensa ya kara bushewa da dariya a karo na biyu, daga nan ya ambaci wani dalasimin tsafi ai sai turakar daya ke ciki ta sauya daga turaka izuwa kogon tsafe tsafensa.
yakai dubansa ga wani bigire daga cikin kogon ya tafa hannunsa nan take sai madubin tsafinsa ta bayyana a hannunsa ya shafi madubin tsafin surar fuskar gimbiya zatal dawahi ya bayyana bisa madubin boka dundamu ya kare mata kallo sannan ya shafi wuyarta inda layar nan take yayi murmushi yana mai ayyanawa a ransa cewa ya kusan mallakar layar dake wuyar tata.
yana a cikin wannan hali ne wani bakin aljani ya bayyana a gareshi yana mai kwasar gaisuwa boka dundamu ya dubi aljani ya ce ” ya Ubbasul laisu ina dalilin barinka bisa ga tafarkin dana ajjiyeka na saka ido ga al’amarin barde muzaffar, Aljani ubbasul Laisu ya ce ” ya shugabana hakika ni nazo gareka tare da mummunan labari ce wa shi jarumi muzaffar ya tsira daga magarkamar daka ajjiyesa kuma ya kashe gabadayan baradan dake tsaron magarkamar. yanzu haka ya nufi hanyar ficewa daga birnin nan.”
Koda boka dundamu yaji zantukan aljani ubbasul laisi sai sai ya takarkare ya kwarara ihun bakin ciki, nan da nan ya mike zumbur ya sabi ambaton dalasiman tsafi yana hamhaman yana dandama, aiko nan take ya bace bat.
Muzaffar kuwa tunda ya fice daga kurkukun da boka dundamu ya kulleshi ya yanki daji ya cigaba da tafiya a kafa. yana cikin tafiyar ne yaga gari yayi duhu hadari ya gangamo tamkar za’a tsuke da ruwan sama, aka fara sakin wata iriyar tsawa mai razanarwa, muzaffar yayi nufin ya jinkirta tafiyar tasa ya samu wani wuri ya jira a idar da ruwan dake shirin saukowa sai kuma yaga boka dundamu ya bayya cikin Asalin siffansa, shidai boka dundamu ya kasance katon gaske ma’aboci manyan damatsa da fadin kirji, boka dundamu na rataye da jakar sihirinsa ya nuno muzaffar da hannu ya ce ” kai iblishin bil’adama kayi min mummunar barna na kashe mini baradana har mutum dari uku, a bisa ga haka zan aikata gareka mummunan kisa wanda wani mutum bai taba samun irinsa ba a duniya” yana gama fadin hakan ya zare takobi ya nufo muzaffar.
muzaffar ya zare takobinsa shima ya kifu akan boka dundamu ya zamana suna kaiwa sunansu sara da suka cikin gwaninta da salon iya yaki, sai da suka kwana suka wuni suna artabunnan amma dayansu ya kasa samun nasara bisa ga abokin gwaminsa, karshe sai da takai ga takubbansu sun dakushe bisa tilas suka yada takubban suka cigaba da naushi gami da bugun junansu sai dai dukkaninsu basa jin naushin da suke yibwa junansu, domin ko Boka dundamu sai tabe iya karfinsa ya dirkawa muzaffar naushi ko mangari amma hakanan zaka ga muzaffar ya cije tamkar an daki ganga haka shima zai gabza wa boka dundamu naushi shima ya shanye.
a haka suka wanzu har washe gari, a sannan ne fa rn boka dundamu ya baci ya tuna cewa shifa boka ne mai babban lamari, ya shahara bisa ga ilimin bokanci, yana daga cikin tsirarun bokayen da suka tsira yayin binciken dukiyar almadud ace karamin yaro kaman muzaffar na neman ya gagareshi ai nantake ya harzuka matukar harzuka. ya dauko farin takarda daga jakar sihirinsa ya jefowa muzaffar yana mai ambatar wata kalmar tsafi ai take sai takardar nan ta rikide ta koma jibgegiyar zakanya.
zakanyar nan ta nufo muzaffar da mugun nufi shi ko ya tsayu yana jiran karisowarta, zakanyar na karisowa ya tarbeta da mummunan naushi a ciki, sabida karfin naushin sai da hannun muzaffar ta fasa cikin zakanyar ta fadi matacciya.
al’amarin daya kara fusata boka dundamu kenan ya sake yin wani aika aikan tsafin ya samarda katuwar gansheka mai kawuna bakwai, nan ma muzaffar ya kuma kashe wanan gamshekar, haka boka dundamu ya tsayu yana ta aikawa da muzaffar munanan dabbobi masu hatsari bisa alkaluman tsafi muzaffar yana kashesu…
© Shuraih Usman 2022
Ku sani: wannan littafin na kudi ne sai dai daga chapter 1 zuwa 10 kyauta ne, zan ruga kawo muku duk bayan kwanaki uku, da zarar mun kai chapter 10, chapter 11 zuwa cigaban littafin zai ruga zuwa ne a shafinmu bayan kwanaki biyu, amma duk chapter guda daya akwai farshinsa. In kuma ya kasance ba zaka iya siyan chapter ba, to zaka iya hakuri duk ranar asabar insha Allahu zamu riga dorawa a nan facebook don ku, amma in ka kagauta to sai kaje shafinmu ka siya duk chapter guda zamu saka farashinsa akan naira hamsin ko naira talatin.
Comments
Post a Comment