Main menu

Pages

FARATAN ZAKI chapter 6 littafin yaki

Shiryawa – Faratan zaki

  • FARATAN ZAKI
  • Littafin Shuraih Usman
  • chapter 6

Cigaba – faratan zaki

Yayin da boka dundamu yaga duk aika aikan sihirinsa sun ki yin tasiri ga Muzaffar sai ya fusata ainun nan take ya sabi karanto wasu zantukan tsafi, a take suffar boka dundamu ta sauya daga na dan adam izuwa jibgegen katon dodo mai kawuna goma da hannuwa dari.

Tunda muzaffar yake a duniya bai taba gamuwa da wata mummunan halitta kamar wannan dodo da boka dundamu ya juya ba, daya daga cikin kawunan dodon nan ya tsage gida biyu sai ga fuskar boka dundamu ta bayyana yana mai bushewa da dariya bayan ya tsagaita da dariyar ne ya ce.

“kai yaro ai in ka iya ruwa to baka iya tabo ba, hakanan in ka iya tabo to baka iya yashi ba, hakika na gamsu kai namijin kwarai ne kuma gwarzon jarumi, domin ko tun da nake a rayuwata babu wani jarumin da ya taba karo dani muka tsawaita fada dashi batare dana karshi ba sai kai, tabbas ka Kafa tarihi domin kaja tunga dani har tsawon wasu yan kwanaki kuma baka rasa rayuwarka ba sai dai kash, yanzu zan shafe wannan tarihi ta hanyar yi maka mummunan kisa, irin wadda ba’ai taba yiwa wani bil’adama ko aljani irin ta ba a duniy…”.

Kalaman Boka dundamu sun fusata muzaffar yai tsawa ga boka ya ce “bar ganin ka juya halittarka izuwa ga wannan dodo, la budda tun da nai rantsuwar halaka ka to sai na cika rantsuwata” yana rufe baki Ya falfalo da masifaffen gudu ya tunkari boka dundamu dake cikin siffar wannan halitta.

halittar tayi ruri ta wangame dukkan bakunanta dake bisa kayukanta ta feso wa muzaffar ruwan dafi, cikin salon bajinta muzaffar ya matsa dafin ya zuba a kasa, nan take kasan wajen ta fara soyewa tamkar an saka kullun waina cikin mai, wannan al’amari ba karamin tayarwa da muzaffar hankali yayi ba.

Amma sai ya dake ya sake yunkurawa ya daka tsalle ya kaiwa kan halittar sara itama halittar ta gitar da kanta gefe sannan ta banke muzaffar da daya daga cikin kawunanta, muzaffar yai baya yaje ya gwaru da jikin bishiya bishiyar ta karye.

FARATAN ZAKI chapter 6 littafin yaki

kafin ya kai ga mikewa tuni har halittar nan ta dako tsalle ta dira a gabanshi, halittar ta dago shi da hannu daya, tamkar shaho ya dau dan tsaki. ta wangame daya daga cikin bakunanta da nufin ta jefa shi ciki nan da nan muzaffar ya murmure ya shammaci halittar nan ya zaro takobinsa ya sare kanta guda, halittar ta sandara ihu da dukkan kayukanta bashiri tayi jifa da muzaffar.

Kuna iya karanta littafin MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN book 1 to 6 complet Audio hausa novel

muzaffar ya mike ya fadawa halittar nan da sara da suka, ya wanzu yana kai mata sara da dukkan iyaka cin karfinsa, cikin kankanin lokaci ya sare gabadayan kawunan wannan halittar sannan ya soka mata takobinsa a ciki. halittar tayi ruri sannan ta fadi matacciya, bayan mutuwar halittar sai ta koma asalin suffar boka dundamu a baje a kasa.

Muzaffar ya share takobinsa ya cigaba da tafiya yana nausawa cikin dawa, haka ya wanzu yana tafiya har sai da ya shafe kimanin Watanni uku sannan ya shigo wani ni’imtaccen lambu ma’abocin ni’ima daga ‘ya’yan itatuwa da Koramu, yayin da Muzaffar ya tsinci kansa cikin wannan lambu sai ya durfafi wata itaciyar rumman yana zuwa ya fara tsinkar ‘ya ‘yan rumman nan yana ci, ya shagaltu da tsinkar ‘ya ‘yan rumman bai yi aune ba kwatsam sai yaga wata jibgegiyar girgizo ta sureshi ta maka da kasa, saboda zafin buguwa Muzaffar ya suma.

Kuna iya downloading indiyan hausa a shafinmu na http://hothausamovies.com

Yana suma Girgizon yayi girgiza ya sauya suffa zuwa kyakkyawar budurwa mai shekaru ashirin da biyar, budurwar tayi tafi da hannunta wasu yan mata ma’abota kyawun suffa da cikar halitta suka fara tsaga kasa suna fitowa, bayan sun gama fitowa daga karkashin kasa dukkansu sukai sujjada ga budurwar nan ta farko sannan wata daga cikinsu da ta kasance waziriya ce ga shugabansu mai suna Murjanatu ta gabato gaban shugabarta su ta russuna ta ce “ya shugabata shin wannan ne mutumin da aka sanar damu zai gabata garemu ya kawar mana da annobar data addabemu”

Shugaban matayen ta ce “babu shakka shine a ka sanar damu zai yaye mana bakin cikin daya addabemu shekara da shekaru to amma magabantanmu sun ce jarumin gaskene mai daka wa yan maza gumba a hannu, kuma gashi nai masa duka daya kacal ya suma anya kuwa shine jarumi Muzaffar ibn Azlam”

Waziriya murjanatu ta ce “ta iya yiwuwa shi dinne, amma koma dai bashi bane mu bari ya farfado tukunna”.

Sudai wayannan mata sun kasance ne suna rayuwa a cikin daularsu mai suna Barhumiyyatul Ruzik, sun kasance bisa bautar Wata gunkiya mai suna Bahashush, wata rana sai wani boka mai babban lamari ya bayyana a birnin shi dai wannan boka sunansa Bishimalul makan ibn hardubu.

shi ya kasance ma’aboci bautar wuta koda bayyanar boka bishimalul makan a birnin barhumiyyatul ruzik sai ya iso fadar birnin, a lokacinnan kuwa sarkin birnin namiji ne mai suna Maddali’u ibn Kulzum.

Sarki Maddali’u na zaune bisa kan karaga ana fadanci kawai sai Boka bishimalul makan ya bayyana tsulum a fadan, Sarki ya dubeshi yace ” yakai wannan bil’adama shin me ke tafe dakai kuma me kake takama da shi da har zakaiwa fadata dirar kawara”.

boka ya numfasa ya ce “ni ne boka Bishimalul makan ibn Hardubu kuma na iso wannan birni naku ne don isar da wata bukata ta, “.

sarki Maddali’u ya ce “to muna sauraranka yakai wannan boka shin mece ce bukatarka garemu”

boka Ya ce “ni na kasance boka mai babban lamari kuma na fahimtu sosai bisa ga harkar tsafi, ina da burin gina wata kasaitacciyar masarauta wacce duk duniya babu irinta a kyau tsaruwa da kawa, bisa ga haka nayi zuzzurfan bincike cikin alkaluman sihiri anan na gano muddin ina son cika wannan buri nawa to fa dole sai na zo wannan birni naku. Gabadayan mazajen birnin sun yanke faratan hannayensu sun diga min jininsu a hannuna, domin kuwa da wannan jini ne zan samu gagarumin karfin da zan bautar da Aljanun da zasu yi min wannan aiki. ” boka bishimalu na gama fadin hakan Sarki maddali’u ya fusata ainun ya kaurara murya ga boka bishimalu ya ce

“ba zamu taba aminta da wannan kudiri naka ba a garemu, Sabida haka ina umartarka daka yi gaggawan bace min da gani kafin na sauke fushina akan ka”.

boka bishimalu ya babbake da dariyar mugunta ya dubi sarki ya ce ” yakai wannan sarki ma’abocin girman kai da dagawa ga Manyan bokaye irina , na rantse da Tauraruwa Zahlu, da kuma wuta abar ruruwa sai na cika wannan buri nawa a gareku, koda kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwar gaba dayan jama’ar birnin nan.”

sarki maddali’u yai tsawa ga sarkin yaki daya gaggauta raba kan boka bishimalu da gangar jikinsa, Sarkin yaki Hubbazu ya zare takobi da nufin aiwatar da umarnin sarki, ganin haka boka bishimalu ya bace daga fadar.

sarki maddali’u yayi kiran bokansa bisa ga alkaluman tsafi, sai ga bokannasa daya kasance yakunannen tsoho ya bayyana yana dogara sanda.

boka Gulmanu yai dubi ga sarki maddali’u ya ce “ya shugabana hakika musifa ta tunkaromu gadan gadan, domin kuwa wannan boka daya ziyarceka a yau wato boka bishimalul makan ibni hardubu hatsabibin boka ne, wanda duk nahiyar nan babu hatsabibi kamarsa, ya yi sani bisa ga Alkaluman tsafi dubu Dari tara da sittin da tara, wanda duk duniya a yanzu babu wani bokan dayai sani da su.”

hankalin sarki maddali’u ya dada dugunzuma ya ce da bokansa gulmanu “yanzu mene ne mafita ya babban boka”

boka gulmanu yai shiru sannan ya share kasa ya baza alkaluman sihirinsa ya kama sambatu yana furta wasu kalamai na tsatsuba kafin daga karshe yayi attishawa sau uku sannan ya fadi a kasa baya motsi. Al’amarin daya kara jirkita hankalin sarki kenan ya durkusa ya kara hannunsa ga hancin boka yaji baya numfashi, ya dago domin ya sanar da yan majalisarsa, anan fa yaga dukkan yan majalisar sun fadi kasa basa motsi irin yadda dai boka gulmanu yayi, daga nan sai yaji dariyar boka bishimalu.

dariyar na tsagaitawa muryar ta ce “kai sarki maddali’u duk duniya iyanzu babu wani mutum daya isa ya tsaidani bisa ga wannan Nufaka nawa, na sumar da gabadayan mazajen birnin nan, kuma yanzu zan kwashesu na kaisu ga bigirena inda zan riga zukar jininsu har sai na kammala Aikina da su sannan zan kashesu, wannan shine hukuncin jayayya dani muryar na zuwa nan a zancenta ta dauke dif tamkar daukewar ruwan sama.

Wata irin guguwace ta bayyana a fadar ta kwashe gabadayan Yan majalisa da hadiman da suka suma ciki kuwa har da boka gulmanu tayi sama da su, irin wannan guguwar ce ta rika bayyana a cikin birnin barhumiyyatul rizik tana sunkutan mazajen birnin a haka sai da guguwar ta dauke gabadayan mazajen ya kasance matane kadai suka rage a birnin.

wannan Al’amari ya tayarwa da matan birnin hankali suka dunguma suka zo fada inda suka tadda sarki maddali’u shi kadai a zaune bisa kan karagarsa cikin tsananin bacin rai, Sarki maddali’u ya dago kai ya dubi matannan ya bayyana musu bisa ga abun daya kasance tsakaninsa da wannan hatsabibin boka.

haka mutanen barhumiyyatul Rizik suka wanzu tsawon shekara daya suna rayuwa batare da mazajensu ba a wannan lokaci sarki maddali’u ya sauka daga kan karagarsa ya dora yarsa, sannan ya nada mata hakimanta da sauran fadawa shi kuwa ya shiga duniya yana bin manyan bokaye yana tambayarsu gameda lamarin boka bishimalu ibn hardubu, duk bokan daya je gareshi sai ya sanar da shi girman lamarin boka bishimalu ya wuce zatonsa, a haka har ya samu labarin wasu gungun bokaye su dari uku.

Wayannan bokaye dai hatsabibai ne sosai a sha’anin bokanci sunansu yai shuhura a duniya, anayi musu lakabi da Mafakan Mutuwa, koda Sarki maddali’u ya isa ga bokayennan dari uku akai masa iso ga shugabansu mai suna Darra’u.

sarki maddali’u ya gabata gaban darra’u yayi nufin sanar da shi bukatarsa amma boka darra’u daya kasance Saurayi kyakkyawa dogo fari ya dakatar da shi sannan ya ce “sarki maddali’u ai mun dade da sanin lamarinka cewa kai kana tafe ne bisa ga bukatarka na ganin bayan boka bishimalul makan ibn hardubu, a sabilida kwashe mazajen birninka da yayi, shin ba wannar bace bukatar taka”

sarki maddali’u ya gyada kai tare da fadin “kwarai kuwa”

saurayin boka shugaban bokaye dari uku boka darra’u yayi nuni da hannunsa ga jikin bango, haske yayi fitar burtu daga hannun nasa ya bayyana a jikin bangon inda sarki maddali’u yayi arba da hoton mutanensa daddaure cikin kurkuku wasu jibga jibgan halittu na gana musu azaba.

boka darra’u ya ce “Tauraruwa zahalu bata bamu ikon taimakonka ka ba amma ta sabbaba taimakon naka bisa ga hannunmu, nan da kwanaki goma wani saurayi zaizo wucewa ta birninka saurayin ya kasance jarumi kuma yanzu haka yana kan hanyansa ce ta zuwa KOGON ZAKUNA don dauko FARATAN ZAKI, wannan saurayi shine zai kubutar da mutanenka daga hannun boka bishimalu ibn hardubu sunansa Muzaffar Ibn Azlam.”

Sarki maddali’u ya ce ” ya shugabana amma tayaya shi saurayin zai amince har ya taimakemu”

boka darra’u najin hakan yayi murmushi ya ce “shi saurayin nan ya kasance matafiyi ne Izan kuka hadu da shi ka sanar sa shi cewa zaka hada shi da Aljanin da zai kaishi duk inda yake so cikin kankanin lokaci.”

Sarki maddali’u ya sake cewa da boka darra’u “to aini bana da Aljanin da zan iya hadashi da saurayin a yanzu”

boka darra’u ya sake yin murmushi ya mika wa sarki wani mudubin tsafi ya ce “a duk lokacin da kuka hadu da saurayin ka shafi mudubin nan da hannunka na hagu fuskata zata bayya a ciki, anan zan sanar daku dukkan abun da kuke da bukata, yanzu na sallameka zaka iya tafiya”. sarki maddali’u yayi godiya ga boka darra’u sannan ya kamo hanya ya dawo birnin barhumiyyatul rizik ya sanar da yarsa Sarauniya Shumaira wannan lamarin, sannan ya ce duk ranar da sukai arba da wani saurayi a birnin nan to su kawoshi gareshi”.

tun daga wannan rana Sarauniya Shumaira ke futa bayan gari su buya karkashin kasa suna jiran isowar Saurayin da Sarki ya sanar da su zuwansa, kwatsam yau sai gashi muzaffar yazo garesu har lamarin daya afku ya afku.

Sarauniya shumaira da jama’arta suka dau Muzaffar suka gabatar da shi ga sarki maddali’u…

Anan zan dakata cikin littafin FARATAN ZAKI chapter 6,

wanda ni Shuraihu Usman na rubuta

Zan cigaba .

Comments

table of contents title