Main menu

Pages

FARATAN ZAKI Chapter 7 littafin yaki

  • FARATAN ZAKI
  • Littafin Shuraih Usman
  • Chapter 7

Cigaba – Faratan Zaki

Sarauniya shumaira da jama’arta suka dau Muzaffar suka nufi cikin birninsu da shi inda suka gabatar da shi ga sarki maddali’u.

sarki maddali’u ya dube shi yayin da yake a halin suma sannan ya shafa masa ruwa a goshi, nan da nan muzaffar ya farka a firgice ya mike tsaye yai baya yana mai zare takobinsa.

Muzaffar ya cigaba da kallon Sarki maddali’u da Shumaira cikin rashin yarda ya ce “su waye ku sannan me kuke nufin aikatawa a gareni.”

Sarki maddali’u ya mike tsaye ya ce “Shin kaine muzaffar ibn Azlam” muzaffar yai mamakin jin Sarki maddali’u ya ambaci sunansa ya dubi sarki ya ce “ya akai kasan sunana” Sarauniya shumaiara ce ta matso kusa da muzaffar kana ta ce “muzaffar ibn azlam Ka yarda damu mu bamun kasance daga cikin mugayen mutane bane ba, kasani cewa mune zamu dora ka bisa turbar nemo abunda ya baro dakai gida wato FARATAN ZAKI”

Muzaffar najin kalaman Sarauniya shumaira ya maida takobinsa cikin kufe, ya matso kusa da Shumaira ya ce “yake wannnan kyakkyawar sarauniya ma’abociya zati da cikar halitta Shin me kika sani a gameda Faratan Zaki”.

sa’adda shumaira ta ji kalaman Muzaffar sai ta dubi mahaifinta sarki maddali’u inda shi kuma ya gabato gaban muzaffar ya ce “hakika mu mun san abubuwa da yawa wanda kai baka sani ba hakanan, kuma ubangijinmu gunkiya bahashush ta sabbaba sanadin Taimakonka bisa ga hannunmu, amma kafin nan kaima zaka taimakemu wanda wannan taimako da zakai mana shine Zai baka damar da kaima zaka samu biyan bukatarka.”

Muzaffar ya sake shiga rudani bayan sauraren kalaman sarki maddali’u ya ce “to wani taimako ku kuke nema daga wurina sannan nima wanne taimako zakuyi mini”

kodajin hakan sai sarki maddali’u ya kwashe labarin birninsu da yadda boka bishimalu ya aikata musu aikin sihiri ya kwashe duk mazajen garin ya tafi da su har ya zuwa sa’adda yaje wurin bokayen nan dari uku ya gana da shugabansu boka darra’u, da kuma yadda ganawar ta su ta kasance daga karshe ya dauko madubin tsafin nan da boka darra’u ya bashi ya shafi madubin da tafin hannunsa sai ga fuskar boka darra’u ta bayyana a jikin madubin.

fuskar ta fara magana da ce wa “lale marhabun da babban jarumi gwarzon gwaraza Sadauki Muzaffar ibn azlam Nine boka darra’u shugaban bokaye dari uku da duk duniya babu kamarsu yanzu a harkar tsafi”

Muzaffar ya matso kuaa da sarki maddali’u ya ce “ina sauraranka ya wannan boka “.

Boka darra’u ya ce “kamar yadda sarki maddali’u ya baka labari kuma ya sanar da kai cewa suna neman taimakonka wanda ta sanadiyar taimakon da zakai musun ne kaima zaka hadu da Aljani Maruful halfi, muzaffar kai sani cewa inda ka nufa yanzu tafiya ce mai tsawo domin kuwa daga nan zuwa birnin sarauniya Badariyya wato birnin burkatul aswad tafiya ce ta kimanin shekaru goma bisa lafiyayyen doki mai kuzari. kaga kuwa kafin ka isa can birnin ma dan uwanka daka fito gida don shi cutar nan na iya halaka shi. Aljani maruful halfi ne kadai zai iya daukarka ya kaika birnin burkatul aswad cikin kwanaki goma domin kuwa shi aljani maruful halfi ya kasance aljani mai saurin tafiya yana iya yin tafiyar shekara guda cikin kwana daya, duk jinsin aljanu na yanzu babu wani aljanin daya kaishi sauri hakanan aljani maruful halfi yana iya gajarce tafiya mai nisan shekaru yayi ta cikin kwanaki kalilan, a yanzu haka aljani maruful halfi na tsare a hannun boka bishimalul makani ibni hardubu.”

muzaffar ya jinjina kai cikin mamaki ya ce da boka darra’u shugaban bokaye dari uku

“mene ne dalilin daya sanya boka bishimalu ya tsare aljani maruful halfi”

yayin da boka darra’u yaji wannan tambaya ta muzaffar sai ya bashi amsa da cewa “boka bishimalu ya kasance boka mai babban lamari yana da sha’ani mai girma tun shekaru dari uku baya yake da wani buri a zuciyarsa na ganin ya gina kasaitacciyar birni wadda babu kamanta a duniya wurin kayatuwa.

a bisa wannan buri nashi ne ya shiga bincike cikin alkaluman tsafi, bayani ya bayyana gareshi kan cewa muddin yana son ya gina wannan birni da babu kamarta a duk fadin duniya to fa dole sai ya mallaki aljanin da yafi kowanne aljani sauri, gudu da kuma gajarce tafiya a duniya. da jinin wannan aljanin ne zaiyi amfani wurin sana’anta wasu mutum mutumi na aljanu sama da dubu hamsin masu irin baiwar wancan aljanin, wato suma mutum mutumin su kasance masu gajarce tafiya, da kuma sauri.

ba komai ya sanya boka bishimalu ke da bukatar aljani mai sauri ba face yana son dukkan mutum mutumin nan da zai sana’anta na aljanu su shiga sassan duniya su isa dukkan masarautun duniya su sato mai abubuwa masu daraja na wannan masarautun.

a bisa ga hakane yai nasarar kama aljani maruful halfi cikin ilimin bokanci yanzu haka yana can a tsare a gidan boka bishimalul makani yana zukar jinin jikinsa, saura kwanaki dari cif ya gama zukar jinin jikinsa kuma da zarar ya kammala zukar jinin aljani maruful halfi nan take zai tashi wayannan mutum mutumi daya sana’anta su dubu hamsin, kuma ya gabatar da bukatarsa garesu, kuma muddin wayannan mutum mutumin na aljanu suka shiga duniya sato manyan kayan tarihin masarautun duniya to fa duniya zata shiga cikin wani hali na musiba da tsanani, kowanne birni zasu shiga cikin fatara da yunwa gamida matsin rayuwa, ya kasance dukkan mutanen duniya basa jin dadin zaman birane da garuruwansu. bisa dole dukkan mutanen duniya zasuyi hijira su nufo birnin da boka bishimalul makan ke kokarin ginawa, kaga kuwa muddin hakan ta kasance kaima birninku na cikin hadari kai bama birnin ku ba dukkan jama’ar duniya suna cikin tashin hankali marar misaltuwa.” fuskar boka darra’u na zuwa nan a zancenshi sai fuskar ta bace bat daga jikin madubin tsafin nan.

muzaffar ya kamu da mamaki ya dubi sarki maddali’u ya tambayeshi bigiren da boka bishimalu ke da zama. sarki maddali’u ya bude baki kenan za bashi amsa kawai sai suka ji wata kakkausar murya na cewa da su “wannan tsuntsu zatai maka jagora izuwa ga bigiren boka bishimalul makan, daga karshe ina mai yi maka fatan nasara.”

muryar na zuwa nan ta dauke dif tamkar daukewar ruwan sama, nan da nan sai wata farar tsuntsu ta baiyana ta tsaya bisa kafadar muzaffar, koda ganin hakan sai muzaffar da sarki maddali’u da sarauniya shumaira suka hakikance cewa boka darra’u ne mai wannan muryar kuma shine ya aiko da tsuntsunnan tayiwa muzaffar jagora.

muzaffar yayi bankwana da sarki maddali’u inda sarkin ya nemi daya bishi amma muzaffar ya hanashi ya ce da shi yayi jiran dawowarsa kawai.

sai da muzaffar ya kwashe kwanaki ashirin yana tafiya cikin daji kafin ya iso bigiren da boka bishimalu ke da zama, a duk wayannan kwanaki tsuntsunnan ita ke yiwa muzaffar jagora tana gaba yana biye da ita a baya bisa kan dokinsa.

tun daga nesa muzaffar ya hango hasumiyar gidan da boka bishimalu ke zaune, bayan sun kariso bakin kofar gidan shi da wannan tsuntsu suka tadda gidan babba irin ginin kasar rum, kofar gidan a bude take muzaffar yasa kai da nufin shiga cikin gidan, ai yana jefa kafarsa guda a cikin gidan sai wurin daya daura kafar tasa ta burme wani wawakeken rami ya bayyana mai fadi da zurfi, ga wuta ganga-ganga na ci a kasar ramin, kafar muzaffar ta fada cikin ramin, sai ji yayi tamkar ana fincikoshi ana janyoshi cikin ramin.

nan fa muzaffar ya fara kokarin ganin bai fada ramin nan ba amma ina, tuni wata iska ta fara fitowa daga cikin ramin nan tana fisgo muzaffar ciki, duk kokarin da muzaffar yayi don tsira amma ya gagara sai ji yayi ya fada cikin ramin nan, ya wanzu yana mai gangarawa kasar ramin, ya cire tsammani ga rayuwa ya sadakar ga halaka, daidai lokacin da ya rage baifi saura taki kalilan ba ya kai karshen ramin inda wutar nan ke ci, har tururin wutar ta fara dukarsa kwatsam sai yaji wani abu ya fincike shi yai sama da shi.

shi dai muzaffar bude idanunsa yayi ya gansa akan turba a bakin kofar gidan boka bishimalul makani, ya mike tsaye inda yai arba da wani aljani a gefensa.

muzaffar ya dubi aljani ya ce “yakai wannan aljani nagode a bisa ceto rayuwata da kayi, sannan wanene kai sannan mene ne dalilin daya sanya ka ceto ni alhalin ni ban sanka ba”

koda aljani yaji haka sai ya ce “da fari dai sunana uddairu kuma ni ne wannan tsuntsun da yai maka jagora izuwa wannan wuri, kasantuwar naga kana shirin halaka ne ya sanya na rikida na koma siffana na asali na ceto rayuwarka.

da muzaffar yaji haka sai ya kuma kamuwa da mamaki sannan ya dada yiwa aljani uddairu godiya ya kuma tambayeshi yanzu ta ina ake shiga wannan hatsabibin gida.

zan cigaba

Chapters na Baya

Comments

table of contents title