FARATAN ZAKI Chapter 8 – littafin yaki
- FARATAN ZAKI
- marubuci Shuraih Usman
- Chapter 8
- Cikakken Chapter
da muzaffar ya ji haka sai ya kuma kamuwa da mamaki sannan ya dada yiwa aljani uddairu godiya ya kuma tambayeshi yanzu ta ina ake shiga wannan hatsabibin gida. aljani uddairu ya ce “ai shi wannan gida da kake gani sihirtaccene boka bishimalu ya rigaya ya sihirceshi kuma wannan kofa da kai yunkurin shiga ta ciki ba kofa bane, akwai irin wayannan kofofi guda ashirin a cikinsu ne kofar gaskiyar take, yanzu gidan zamu zagaye muna duba kofofin ko ma dace da asalin kofar gidan”
muzaffar ya aminta da shawarar aljani uddairu, suka shiga zagaye gidan suna duba kofar shiga, inda suka riga arba da kofofi amma duk bana asali bane.
sai da suka zagaye gidan kaf basu ga kofar nan da suke nema ba, al’amarin daya tashi hankalin muzaffar kenan ya dubi aljani uddairu ya ce “ga shi mun zagaye kofofin gidan gaba daya amma babu asalin kofar yanzu tayaya zamu shiga gidan”
aljani uddairu ya ce “ai yanzu kawai tashi zakayi ka hau bayana mu haura gidan ta sama inajin hakan zaifi”
muzaffar ya mike ya haye bayan aljani uddairu, uddairu ya kada fuka-fukansa yai sama ya durfafi katangar gidan boka bishimalul makani ibni hardubu gadan-gadan, yana karisowa daidai katangar yaji wani tururi na dukansa ba shiri yaja da baya ya ce da muzaffar “ya shugabana ba zan iya ketare katangar nan ba saboda akwai wani dako da akaiwa katangar da bana da iznin kusantarsa inko na kusanceshi to zan mutu,”
koda muzaffar yaji haka sai ya umarci aljani uddairu daya saukeshi kasa, bayan aljani ya saukeshi ya kuma umartarsa daya daukeshi yayi cilli da shi a cikin gidan.
aljani uddairu ya dau muzaffar ya ware iya karfinsa yayi cilli da shi izuwa cikin gidan boka bishimalul makani, muzaffar ya tafi tamkar an harba kibiya daga cikin baka yaje ya haye katangar ya fada cikin gidan.
yana dira a cikin gidan ido ya raina fata, domin kuwa dirowa yayi a tsakiyar dodannin dake baiwa gidan tsaro. dodannin sukaiwa muzaffar kawanya can suka buda hanya shugabansu ya kariso ya dubi muzaffar ya ce “kai bil’adama me ya shigo da kai wannan gida hala ajalinka ne ya karato” yana gama fadin hakan yaiwa sauran dodannin inkiya da idanu akan su gama da muzaffar.
nan fa dodannin na sukai kukan kura suka kifu akan muzaffar, ganin haka muzaffar ya zare takobi ya hausu da sara da suka ya wanzu yana saransu yana turasu kiyama, duk da dodannin sun fishi girma sau biyu amma a haka yake daka uban tsalle ya shaftara musu sara.
ana cikin dauki ba dadin ne wani murgujejen dodo yai nasarar damkan muzaffar, yai jifa da shi yaje ya gwaru da gini, nan take muzaffar ya suma.
dodannin suka daukeshi suka kaishi gaban ubangidansu boka bishimalul makani ibn hardrubu.
boka ya karewa muzaffar kallo, sannan yai tafi da hannunsa sai dukkan lamarin muzaffar ya bayyana gareshi tun daga fitowarsa gida da dalilin fitowar ta sa kawo izuwansa gidansa. yayin da boka bishmalu ya ga haka sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta.
nan yai aikin sihiri muzaffar ya farfado daga suman da yayi, farfadowar muzaffar ke da wuya ya mike tsaye ya karewa boka bishimalul makan kallo kafin ya ce “ko kokonto bana yi kaine boka bishimalul makan ibn hardubu, to kayi sani cewa na zo wannan gida taka da burika guda biyu, da fari ina son ka saki mazajen birnin burkatul aswad da ka kama sannan ka saki aljani maruful halfi.”
Koda boka bishimalu yaji haka sai ya dada takarkarewa ya bushe da dariya, sai da yayi ta isheshi sannnan ya ce da muzaffar “kai yaro kai sani cewa na dade daman ina nemanka don na dau fansar ran dan uwana daka kashe, to yanzu gashi ka kawo kanka gareni, labudda kuwa in halakaka”
Yayin da muzaffar yaji kalaman boka hardubu sai ya ce
“Wanene dan uwan naka daka ke inkarin na kashe shi”
Boka yace “ai boka dundamu daka kashe a can birnin nan daka baro dan uwana ne, ubanmu daya uwarmu daya, kuma shi ya kasance kanine gareni ina matukar sonsa fiye da komai a wannan duniya hasalima don shine nake burin gina wannan birni da babu kamarsa a duk fadin duniya, sai gashi ka kashe shi,kuma asalin sunansa ba boka dundamu bane, sunansa boka sha’asha’irul makani ibn hardubu.”
Muzaffar ya zare takobinsa ya ce “yakai wannan boka kai sani cewa na kashe boka dundamu ne saboda yayi yunkurin halakani, muddin kaima kace zaka yakeni to kuwa zan sada ka da dan uwanka” wannan kalamai sun batawa boka bishimalul makani rai, nan da nan ya harzuka ya fara cika yana batsewa ya fara hanhama yana dandama wani farin hayaki na fita daga bakinsa. Ya sabi karanto dalasiman tsatsuba, nan da nan sai wasu dirka dirkan zakuna biyu suka bayyana a gefensa.
Su dai wayannan zakuna sun kasance jibga jibga don kuwa sun ninka muzaffar biyar a girma, boka bishimalu yaiwa zakunan tsawa suka durfafi muzaffar cikin masifaffen gudu, aiko suna gabda karasowa gareshi dukkansu suka daka tsalle sukai sama, ganin haka muzaffar ya gyara tsayuwarsa shima ya dako tsalle ya taryesu a saman suka gwamutse da masifaffen artabu mai tada hankalin yan kallo, zakunan nan suka wanzu suna kaiwa muzaffar yakushi da faratansu, gamida cizo da bakunansu, shi ko ya kasantu a tsakiyarsu yana gocewa gamida zillewa dukkan hare haren su kana yana maida martani.
Ana cikin wannan artabu ne muzaffar yai nasarar sokawa zaki guda takobi a baki, takobin ta shige cikin bakin zakin ya fadi matacce, dayan zakin na ganin haka ya fusata ya kuma afkawa muzaffar inda shima muzaffar ya sada shi da ajalinsa.
Bayan ya gama da zakunan nan sai ya juyo ya dubi boka bishimalul makani ibn hardubu, yayin da boka yaga muzaffar yai nasarar kashe wayannan zakuna sai ya dada yin wani aikin sihirin ya samarda wasu jibga jibgan dodanni masu kan batoyi da jikin bishiya, dodannin suka afkama muzaffar, shima ya tarbesu yana mai saransu da rantsastsiyar takobinsa, duk inda yasa gaba sai kaga dodannin nan na zuba a kasa tamkar ana sassabe a gona.
Cikin kankanin lokaci muzaffar ya halaka gabaki dayan dodannin nan ya zamana daya daga cikinsu bai saura ba, haka dai boka bishimalul makani yaita aikawa da muzaffar da masifu kala-kala shi kuwa yana halakasu, daga karshe dai sai boka bishimalul makani ya zare takobinsa yace “kai yaro maza bisa kanka”
Ya tari muzaffar suka ruguntsume da masifaffen artabu, suka dau tsawon lokaci suna fafata gumurzu tsakaninsu, har takobin boka bishimalu ta dakushe,muzaffar ya rinjayeshi ya daga boka sama ya maka da kasa, ya saka takobi zai datse kansa, kwatsam sai wata guguwa ta bayyana ta suri boka bishimalu ta tafi da shi.
muzaffar ko ya kutsa kai cikin gidan nan inda ya tarar da tarin mazajen birnin burkatul aswad daure cikin keji, nan da nan ya hau kuncesu. bayan ya gama kuncesu ne ya fara duba gidan yana duba inda Aljani maruful halfi yake, cikin sa’a kuwa ya ganshi a cikin wani daki an aikata aikin sihiri gareshi ya sandare a sama ga wasu jijiyoyin tsafi da suka shiga jikinsa suna zuko jininsa suna zubawa cikin wata battar karfe.
muzaffar ya sanya takobi ya sare jiniyoyinnan gaba daya, Aljani maruful halfi ya fado kasa. sannan wannan battar ta karfe da jinin aljani maruful halfi ke taruwa a ciki, ta fashe fus anan take dukkan jinin dake cikinta suka Tashi suka nufi jikin aljani maruful halfi suka shige.
faruwar hakan keda wuya sai aljani maruful halfi ya farka yana mai tari, ya dubi Muzaffar ya ce “madalla da kai wannan sadauki da ka kubutar da rayuwata daga hannun wannan hatsabibin boka, shin me kake bukata dana aikata a gareka”
Muzaffar ya ce “yakai aljani maruful halfi ka sani cewa na samu labarinka ne daga wurin boka darra’u shugaban bokaye dari uku, cewa babu wani aljani da ya fika saurin tafiya, yacr kana gajarce tafiyan shekaru kayisu cikin kwanaki, a bisa hakanne na zo gareka domin ka daukeni ka kaini wani birni dayake can nahiyar bakaken fata don na biya wata bukatata”.
da aljani maruful halfi yaji haka sai ya ce ” babu damuwa yanzu maza ka hau bisa kaina mu kama tafiya kuma daga yau zan kasance bawa a gareka, domin kuwa kai kasance mutum mai tausayi da jinkai, kuma ni ina kaunar ire-iren mutane haka”
muzaffar ya ce “to yanzu ka kwashe dukkan mutanen nan ka kaisu birninsu nima ina nan tahowa bisa kan wani aljani da muke tare”
Aljani maruful halfi ya kwashi dukkan mazajennan na birnin Barhumiyyatul Ruzik ya nufi birnin da su, muzaffar na biye da shi a baya.
bayan sun isa birnin ne aljani maruful halfi ya sauke mazajennan, sarki maddali’u yai farin ciki ainun da wannan nasara da Muzaffar ya samu akan boka bishimalul makani yai masa godiya tamkar zai shide a kasa.
a wannan rana Uwa ta sadadu da danta,Mata ta sadu da mijinta hakanan yar uwa ta sadu da dan uwanta, murna a wurin jama’ar wannan birni bashi faduwa, sai dai aka dau kwanaki bakwai ana shagali na murnanr dawowan mazajen birnin kafin muzaffar yayi shirin tafiya, ya zo fada ya samu sarki maddali’u zaune bisa karagar mulki ga fadawa da hadimai sun zagaye shi ya ce shifa zai wuce yanzu, sarki najin haka ya ce ya bari yadan kwana biyu ya huta sai ya tafi amma muzaffar ya hakikance yace shi sam bazai kara kwana a garin ba.
da dai sarki maddali’u yayi yayi da muzaffar ya zauna yaki sai ya bashi guzuri mai tarin yawa da dukiya amma muzaffar yaki amsan dukiyan ya amshi iya guzurin daga nan ya kira aljani maruful halfi ya daukeshi ya luluka da shi a sararin samaniya.
- Zamu dakata anan, sauranmu chapters biyu mu idar da free chapters, insha Allahu gobe zamu saka chapter 9 a website namu, jibi kuma a nan facebook, na dawo kenan gadan-gadan babu kama hannun yaro.
Shuraihu Usman
Whatssap: 08140419490
Comments
Post a Comment