Main menu

Pages

FARATAN ZAKI chapter 9 - Birnin Burkatul Aswad

FARATAN ZAKI chapter 9 – Birnin Burkatul Aswad

  • FARATAN ZAKI
  • Littafin Shuraih Usman
  • Chapter 9

.

Jarumi muzaffar ya kasantu bisa ga bayan aljani maruful halfi, sukai ta keta hazo a sararin samaniya, tun da suka fara tafiyar tasu basu yada zango koda sau daya ba.

Kuma wani abun al’ajabi da muzaffar ya tsinkaya shine kwata-kwata baiji bawali ko bayan gida yazo masa ba, aduk kwanakin da suka shafe a wannan tafiya, har ta kai ga ya kasa hakuri rannan da suke cika kwanaki tara cif da fara tafiyar tasu, ya tambayi aljani maruful halfi gameda wannan al’amari.

Bayan da aljani maruful halfi yaji tambayar muzaffar sai ya bushe da dariya sai da yayi mai isarsa kafin ya ce “ya shugabana kayi sani cewa ni fa aljani ne mai babban sha’ani, ina da baiwan da bakowanne aljani ke gareshi ba, daya daga cikin baiwannan tawa kuwa itace, duk yawan kwanakin da zanyi ina tafiya a sararin samaniya, koda ace zan shekara guda ne to wata bukata daga dangin fitsari ko bayan gida, baza su taba zuwan mini ba, hakanan duk mahalukin dana dauko shima bazai ji bukatar wayannan abubuwa ba.”

Mazuffar ya yi mamaki da jin wannan baiwa ta aljani maruful halfi da ba kowanne aljani ne keda ita ba sannan ya ce “yanzu shaura kwana nawa mu isa birnin burkatul aswad din”

Aljani maruful halfi ya ce “gobe zamu isa birnin, yanzu hakama ina jiyo kamshin birnin”

Muzaffar ya kuma tambayar aljani maruful halfi “yakai maruful halfi kaiko me ka sani gameda birnin burkatul aswad da mutanen cikinsa” aljani ya ce “birnin burkatul aswad birni ne na bakaken fata, gabadayan jama’ar birnin suna bin addinin musulunci ne, kuma suna da ababen al’ajabi gaya, domin su basa tsafi ko sihiri hakanan tsafi baya tasiri a kansu, dukkan mutanen birnin suna shiga ta kamala, mazansu suna sanya doguwar riga da rawani, mata suma suna sanya doguwar riga har kasa ta yadda ko kafafunsu ba’a gani, kana suna rufe gashin kawunansu da mayafi. Tun dana ke yawace yawace a duniya ban taba ganin mutane masu kamala da cikar haiba ba kamarsu. Kuma birninsu na da wani tsari wanda duk gawurtar mutum a fagen tsafi bai isa ya karya wannan tsari ba. Tunda aka kafa birnin shekaru masu yawa baya ba’a taba nufosu da yaki ba, duk da baya manyan sarakunan duniya sun sha yin gangami su zo su murkushesu amma da zarar sun kariso ganuwar birnin sai wani shinge ya bayyana yai musu iyaka da birnin, tayadda gashi suna ganin birnin kuma suna hangen mutanen ciki amma basa da ikon cutar da su.

A wancan lokacin sarkin KISRA mai suna hambanush shu’uba ya shiga halwar tsafi yana bincike akan yadda zasu karya wannan shinge dake yi musu tsakani da mutanen birnin BURKATUL ASWAD, sai da yayi shekaru uku cikin halwar tsafinsa sannan ya gano wata hanya.” Aljani maruful halfi na zuwa nan a zancensa muzaffar ya ce”to amma me ya sa sarakaunan duniya na wancan zamanin ke kokarin murkushe jama’ar wannan birni” aljani yayi shiru kafin ya ce “saboda su mutanen wannan birni sun kasance suna bin addinin musulunci, kuma sarakunan wancan zamani sun tsani addinin musulunci fiye da yadda suka tsani mutuwansu, domin kuwa sun gani bisa aikin sihirinsu cewa nan gaba addinin musulunci sai ya yadu a duniya,kuma su ma’abota wannan addini zasu mulki wannan duniya tamu, to kaji dalilin daya sanya suke son su murkushe birnin burkatul aswad.

Bayan da sarkin kisra hambanush shu’uba ya fito daga halwar tsafinsa sai ya tattara gaba dayan rundinarsa suka je DAJIN MUTUWA wurin wani hatsabibin aljani mai suna baugazatu, aljani baugazatu ya kasance gawurtacce kuma hatsabibin boka daya gagari duk jama’ar aljanu, ance a lokacin samartakarsa shi kadai yake nufan babban daula ta aljanu ya yakesu ya karkashe kowa da kowa, bayan da sarkin kisra hambanush shu’abu suka isa ga aljani baugazatu suka nemi daya taimaka musu wurin rusa shingen birnin burkatul aswad.

Bayan da aljani baugazatu yaji bukatarsu sai ya takarkare ya bushe da dariya sannan ya dubi sarki hambanu ya ce “yakai wannan sarki kayi sani wannan aiki da kuke nemon taimakona akai ya kasance tamkar farali ne a gareni, domin kuwa nima ina da irin wannan buri naku na murkushe dukkan ma’abota wannan addini, dun haka ni da gabadayan runduna na muna maraba da zuwanku kuma lallai a gobe da yardan wuta abar ruruwa, zan karya wannan tsinannen shingen da karfin sihirina” aljani baugazatu na gama fadin hakan ya bace bat, nan da nan sai dajin mutuwa itama ta bace sarki hambanu suka tsinci kansu bisa sahara a tsakiyar hamada, bayan dan wani lokaci sai suka hango kura ta tokare sararin samaniya daga yammacin hamadan nan, kana kasa na girgiza tamkar zata zaizaye, aiko kuran nan na kusan to su suka ga ashe, aljani baugazatu ne da dukkan jama’arsa sukayi gagarumin shirin yaki, nan fa rundunar aljanu data mutane suka tashi suka nufi birnin burkatul aswad, da zuwansu bakin birnin nan sai wannan shinge ya kuma bayyana, aljani baugazatu ya sauko kasa ya zo gaban shigen.

Nan ya fara tsatsuba yana hanhama yana dandama, ya kwanto jakar bokancinsa ya fiddo da wata macijiya ya cillata ta nufi shingen, macijiyar na karisowa ta rikide ta zama jibgegiyar gamsheka mai kawuna uku, nan da nan ta fara dukan shingen da dukkan kawunanta a duk lokacin da ta doki shingen da kanta sai wani sauti ya tashi kana birnin burkatul aswad tayi girgiza, jama’ar birnin burkatul aswad sukayi gangami cikin shigar yaki, suka tsaya suna jiran rugujewar shingen nasu su afkawa makiya, da dai wannan macijiya ta ga ta gagara karya shingen nan sai ta bude duka bakunanta uku, ta feso dukkan dafinta wa shigen, ai kuwa nan da nan sai shingen ya canza launi ya koma baki, ganin haka sai aljani baugazatu yayi wani aikin sihiri ya samarda babbar guguwa, guguwar ta je ta gwaru da shingen, nan fa shingen ya soma tsastsagewa, macijiyar nan ta cigaba da dukan shingen da dukkan kawunanta.

Duk wannan abu dake faruwa akan idanun jama’ar birnin burkatul aswad yake faruwa, sun rike takobi tsirara suna jiran faduwar shingen tasu, sai da aka dau lokaci mai tsayi kafin Aljani baugazatu ya samu nasarar karya shingen birnin burkatul aswad, koda karya shingen sai aljani baugazatu ya takar kare da dariyar mugunta, sannan yai wa rundunarsa umarni da su ratsa shingen.

Nan fa gabadayan rundunar nan ta aljanu da mutane da adadinsu yakai dubu dari takwas suka kewaye birnin burkatul aswad, dakarun birnin da ba su fi dubu goma ba dake cikin shiri, suka karewa rundunar makiya kallo, suka ga basa ganin karshensu. Sarki hambanu ne ya fito gaban rundunarsa ya daukaka murya ya ce “yaku jama’ar birnin burkatul aswad kuyi sani cewa yau dayanku bazai tsira daga kaifin takubbanmu ba, shin ina abun dogaran naku, wannan ubangijin dake taimakonku, na rantse da wuta abar ruruwa yau babu mai cetonku daga ukubata…” wata rantsastsiyar takobi data raba kan sarkin kisra hambanu da gangar jikinsa itace ta katse maganar tasa, kan yai gare bisa kasa, a zahirin gaskiya babu wanda yaga wanda ya jefo takobin nan hatta jama’ar birnin burkatul aswad kuwa.

FARATAN ZAKI chapter 9 – Birnin Burkatul Aswad

Ganin sarkin kisra a mace, hakan ya harzuka aljani baugazatu nan da nan yai wa jama’arsa umarni da su afkawa mutanen birnin burkatul aswad, aiko dakarun nasa sukai ruri sukai kuwwa suka afka musu, to fa anan ne suka ga wasu mutane suna saukowa daga sama sanye da fararen tufafi, mutanen na dauke da fuka-fukai a bayansu.

yayinda jama’ar birnin burkatul aswad suka ga wayannan mutane sai suka hakikance lallai Mala’ikune, haka dai mutanen nan suka aukawa dakarun Aljani hambanu, aka kaure da masifaffen yaki mai tada hankali.

nan fa aka dunga gwabza yaki har tsawon kwanaki uku batare da tsagaitawa ba, Mutanen birnin burkatul aswad na gefe suna kallon wannan fafatawa, a rana ta uku ne mutanen nan sukai nasarar karar da dukkan aljanu da dakarun Aljani baugazatu, suka karkashesu sannan shugabansu ya zo gaban wannan birnin nan ya shafeta, cikin mamaki sai akaga shingen nan ya kuma bayyana.

Shugaban Mutanen nan ya iso gaban sarkin birnin burkatul aswad na wancan lokacin ya ce “Sunana Muntadihu, kuma ni na kasance sarkin yakin sarkin fararen Aljanu abayaro, muma mun kasance musulmai kamarku, sarki abayaro shi ya turo mu da mu kareku daga sharrin wayannan aljanu, kuma mu sabunta shingen wannan birni, Alhamdulillah mun idar da aikin daya turomu don haka mu zamu wuce”

shugaban Aljanun na gama fadin haka ya bace shi da dukkan Fararen aljanun nan.” yayin da Aljani maruful halfi ya zo nan a labarin sa ya ce “to fa tun daga wannan rana ba a kuma samun wani sarki na aljanu konna mutane da yayi yunkurin afka wa birnin burkatul aswad da yaki ba. to kaji tarihin birnin burkatul aswad”.

zamu cigaba

Comments

table of contents title