MU GANI A KASA Hot love story page 1 and 2
GAWURTATTU BIYAR.🔥
Page 1-2
Godiya ga Allah (S A T) da ya sake bani dama da iko da sake zaman rubuta muku wannan labarin, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzonmu Annabi Muhammad (S A W). Da fatan zaku bini sannu a hankali domin jin inda wannan karon labarina ya nufa.
Haƙƙin mallaka na Ummu Affan ne, ban yadda a juya mini labari ta ko wacce siga ba, ko ɗaurawa a wata kafa ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne. Sannan ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi domin kowa ba idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne.
Ɗungurungun littafin nan sadaukarwa ne ga Auntyna Ƴar’uwata Ta gaban goshina ta ƙasan zuciyata MARYAM MODIBBO wato ADDA Maman Hamdana da Hamd. Ke ɗin ta daban ce Zinariya kike a zuciyar Abbansu Humaid.🙈💃😍
Masu san na musu talla a pages na littafina zasu iya magana cikin farashi me sauƙi mai tallah shi ke da riba.
Bismillahir rahmanir rahim.
ABUJA NIGERIA
Sanyayyiyar iskar damina ce ke kaɗawa a daidai lokacin, gari ya yi luf da ni’ima ya yin da sararin samaniya ya yi fayau dashi gwanin burgewa da ban sha’awa. Tuƙi yake cike da ƙwarewa yana sharara gudu saman lafiyayyar kwaltar da ke birnin tarayya Abuja. Yayi tafiya me nisa kafin ya iso babbar unguwar tasu ta Asokoro. Wani katafaren gate ya dosa inda ya buga hurn, da sauri Maigadi yazo tare da wangale mishi ƙaton gate ɗin ya kutsa hancin motar shi ciki. Sannu da zuwa Officer ke masa hannun shi kawai ya iya ɗaga mishi. A cikin babban harabar gidan ne ya samu guri ya yi parking, kusan minti biyu kafin ya iya zuro ƙafarshi daga motar, ƙafar tashi mai sanye da ƙayatattun baƙaƙen takalmi sau ciki ce ya zuro a hankali kamar mai tsoran fitowa. A hankali kuma sassan jikin ya fito da shi, “Ma sha Allah” Ƙyaƙƙyawa ne ajin farko. A hankali yake tafiya kamar mai tsoran takawa hannun shi ɗauke da ƙatuwar wayar shi yana duba saƙon da yaji shugowar sa tun yana tuƙi. Dan tsaki yaja ganin mai saƙon kafin ya zura wayar cikin aljihu ya doshi hanyar da zata sada shi da parlourn gidan. Da gudu ta taso tare da nufarshi da niyyar faɗawa jikin shi “Oyoyo Yaya Aliyu!” Ta furta da tsantsar farin ciki. Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, chak ta tsaya jiki a matuƙar sanyaye.
Karanta TA LEKO TA KOMA complete hausa novel written by Fatima Aminu
Ƙarasawa Yayi gaban Amminsa dake tsaye tana kallon abin da ke faruwa. Zaunawa yayi saman Cushin yana me duban Ammin tashi. “Barka da hutawa Ammi!” Ya furta cikin sanyi bazaka taɓa cewa shine yayi maganar ba, sakamakon laɓɓansa ne kawai suka motsa idan ma ba kusa dashi kake ba, ba lallai ne kaji me ya furta ba. Wani kallo ta ma shi ba tare da ta amsa ba, ta mayar da kallonta ga yarinyar da ya nunawa ko in kula wacce ke tsaye kamar gunki har zuwa lokacin. “Sareenah tsayuwar ta isa haka, ko baki gaji da kallon nashi ba ne?” Cike da kunya tayi wani far! Sai ta juyo a sanyaye tare da zama gefen shi. “Abuturrab har yanzu halinka na nan ko? Ko ka mance wacece Sareenah a gareka ne?” Wuci ya fesar me zafi kafin ya ce”Ammi yunwa nake ji” Ya faɗa da nufin ɓangarar da wancen zan cen. Kallonsa take ko ƙittawa babu, wani murmushi ta saki wanda ita ce kawai tasan ma anarsa kafin ta kalli Sareenah “Ki kai mishi abinci part ɗin shi” “No Ammi!” Ya furta kamar zai yi kuka. “Ki kawo mishi anan” Girgiza kai yake amma ya kasa cewa komi sakamakon kallon da Ammi tayi mishi. Tashi tayi a gurin yabi bayanta da kallo har ta ƙarashe hawa saman benen, sanyayyar ajiyar zuciya ya saki ƙirjin shi na wani irin bugu. Bai san time ya ɗan ja yana gurin zaune ba sai da Sareenah ta ƙara so tare da ajiye tray ɗin dake hannunta. “Yaya Aliyu ga abincin!” Ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefensa. Da sauri ya miƙe yana jifanta da wani mugun kallo, ƙala bai iya ce mata ba ya miƙe tare da nufar ƙofar parlour. “Abincin fa? Ko na biyoka da shi part ɗinka?” Ta jero mishi tambayoyin a lokaci guda, juyowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata. Yana fita kai tsaye part ɗin sa ya dosa, komi fes-fes kamar yadda ya zata. Kai tsaye bedroom ya wuce yana zuwa komi na jikinsa ya cire tare da faɗawa toilet, wanka ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fito ɗaure da towul ɗaya a hannunsa yana goge sumar kan shi. Mirror ya nufa inda ya shafa maya-mayansa tare da feshe jikinsa da turaren sa mai daɗin ƙamshi, Ƙananun kaya ya saka dogon wando tare da riga t-shirt sai ya ɗora wata me kauri ta sanyi me haɗe da hula, sakamakon yanayin garin na sanyi. Ya so ya huta amma kiran sallar ta Azahar da ake ƙwala kira a masallacin ƙofar gidansu ne ya sashi nufar hanyar fita daga badroom ɗin. Yana fita kai tsaye masallaci ya nufa.
Sareenah bayan fitarsa da gudu ta hau sama bedroom ɗin Ammi, tana shiga ta sami Ammin na waya da gudu ta ƙarasa tare da faɗawa jikinta ta saki wani kuka. Ba shiri Ammi tayi sallama da wacce suke wayar tare da sanar da ita anjima zata kirata. “Sareenah lafiya kuwa?” Ammi ta tambayeta bayan ta ajiye wayarta saman ƙaramar durowar dake kusa da ita. Cikin kuka wanda zallarsa shagwaɓa ne da sangarta ta ce “Ammi Yaya Aliyu ne! Mene ne na masa ya tsane ni haka?” Da sauri Ammi ta katseta ta hanyar ɗaura ɗanuatsanta saman laɓɓan Sareenah “Kar in kuma ji” Ammi ta faɗa tare da kawar da ɗan yatsanta kafin tacigaba da cewa”Shi har ya isa? Bai kai matsayin tsanarki ba Sareenah kicigaba da shige masa kamar yadda na nuna miki a juri zuwa rafi dai, nasan dole wata rana tulu zai fashe.”
“Har zuwa yaushe ne tulun zai fashe Ammi? Kin san dai yarda Yaya Aliyu ke zuciyata!” “Ke dai Sareenah albasa ba ta yi halin ruwa ba, da tayi tabbas ba za ta yi yaji ba tun da har na ce miki haka to ki ɗauka mana, kin san bana san ɓacin ranki” Ammi ta faɗa tana sharewa Sareenah hawayen dake zuba a fuskarta. Numfashi ta sauke tare da lafewa jikin Ammin tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, sannan tasan wacece Ammi bata faɗin ƙarya sai abin da ke ƙasan zuciyarta.
Fitowarsa daga masallaci ba ɓata lokaci ya ɗauke key ɗin motarsa, cikin tafiyarsa ta alfarma ya doshi harabar gidan, tun daga nesa ya dannawa motar key ta buɗe yana zuwa ya faɗa ciki tare da kunnawa. A ɗari ya fita gate ɗin gidan daman tuni Maigadi ya buɗe masa tun lokacin da yaga ya doshi motar. Wani gidan abinci ya nufa na manya sai wanda ya amsa sunansa ke cin abinci a gurin. “Barka da zuwa ƴallaɓai” Wata murya siririya ce tayi maganar. Bai ɗago kan shi ba, tun bayan zamansa saman kujerar haka jin maganarta bai sa shi jin zai ɗago ba, duk kuwa da jin bugun zuciyarsa da ya tsananta. “Me kake buƙata?” Maganar ɗazu ta ƙara ratsa masarrafar sautin sa, bai ce ko ci kanki ba wata farar talarda ya ga an ajiye mishi, sai lokacin ya kai idanuwansa kan takardar, abinci ne da nasha da dangin na ƙwalama kala-kala rubuce a jikin takardar. Pen ya ciro gaban rigar shi tare da making abin da ke buƙata tare da ture takardar da baya jin zai iya magana miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi. Ta ɓangarenta kuwa tun bayan parking ɗinsa Madam (Shugabar gurin abincin) Ta ce”Ke Tataah ga kostoma nan jeki gurinsa” Cikin sanyinta ta miƙe tana ta fiya sulow kamar yarda take, daidai zamansa ta ƙarasa tare da tambayarsa abin da yake buƙata. Jin shuru ta ɗago idanuwanta ta dubesa, gabanta taji ya bada dammm! Haka ta daure ta kuma tambayarsa cikin sanyi amma bai bata amsa ba sai ta saka mishi takardar tana mai jin haushi a zuciyarta sakamakon ko in kula da ya nuna mata. Ganin abin da yayi a ranta ta ce”Uhmm! Masu abu da abin su, tabbas a rashin kira karen bebe ya ɓata” Tana duba irin wannan izza da girman kai na wannan mutumin. Lokacin da Madam ta ce taje tsoro ne ya fara ɗarsar mata sakamakon yadda ƙadangarun bariki ke kai mata haushi a gurin, tana tsananin tsoron zuwa tambayar abin da masu sayen abinki ke buƙata saboda wasunsu maganar banza suke mata, a kallon farko ta ɗauka shima hakanne musamman da ta ganshi matashi sai ta fuskanci maganar nan ta kowa da halinsa amma wannan kuma girman kai ke damunsa, da wannan tunanin ta ɗauki takardar tare da nufar gurin Madam ta miƙa mata. Komi da ya buƙata aka haɗa masa tare da ba Tataah ta kai mishi, tsaye tayi a gurin tana kallon yarda yake danna wayarsa bai damu da kallon kowa dake gurin ba. Jin tsayuwar mutum kuma ba a ce komi ba ya sashi ɗagowa a hankali, idanuwansu ne suka gauraya da na juna, sauran kaɗan tiren hannun Tataah ya sun ɓule saboda tsorata da tayi da yarda da tsinci gabanta na dukan tara-tara. Da sauri ya saka hannun ya amshi Tray yana jan dogon tsaki duk da shima yaji shock a haɗa idanuwansu amma ba zaka taɓa gane hakan ba. Wani banzan kallo ya aika mata da faɗin “Noneses baki da hankali ne zaki ɓata ni?” Da sauri ta juya tare da barin gurin. Duk bayan saƙon ɗaya sai yaja tsaki jin zuciyarsa ya yi sam babu daɗi, yunwar da yake ji ne yasa shi buɗe abincin ya fara ci, amma da ya tuno fuskarta sai yaja tsaki da haka ya cika cikinsa, Drink ya ɗauka yana sha a hankali yana amsa wayar da ake ta kiransa tun ɗazu. “Aliyu ka shugo ne?” Abin da aka faɗa daga can ɓangaren kenan, sai da ya kurɓi lemunsa ya haɗiye sannan ya furta “I akwai wani abu ne?” “Ɗan renin wayau, mu muna nan muna jiranka kana shanya mu!” Robar lemun ya ajiye tare da cewa “Faruuk bacci zanyi” Ƙit! Ya katse kiran daidai miƙewarsa. Gurin biyan kuɗi ya dosa tare da barin gurin cikin sauri.
Tataah dake leƙensa ganin yarda motarsa ta fita harabar gurin a sittin ta sauke numfashi nan take kuma idanuwanta suka kawo ruwa, kawar da abin da yazo mata tayi tare da dosar gurin zamanta. Ba ita ta bar gurin ba sai gabda magrib lokacin da ma’aikatan dare suka iso, gurin Madam taje inda ta bata sallamarta na ranar. Ƙarasawa tayi gurin kayanta tare da ɗaukar babban hijabinta da ke gurin wanda ya tsufa sosai, sakawa tayi ta ɗauki ƙaramar jakarta tare da kularta. Madam ta kai mawa ta zuba mata abincinta na rana da na dare wanda take basu, to ita bataci sai zata tafi take amsa. Kai tsaye bakin babban titin ta nufa domin samun Kekenapep da zai mayar da ita gida, ta tare kusan napep uku amma rashin daidaitawa yasa suke wucewa domin a kullum nera ɗari biyu ta ware domin zuwanta gurin a ɗari ta koma ɗari, idan bata samu wanda zai kaita a hakan ba to tana haƙura har ta samu. Tana tsaye gurin rungume da kularta da jakarta, yadda garin ya kaɗa hadari ne ya bata tsoro duk ta cure guri guda, tsoranta ɗaya karta ƙara hamsim ya zama ɗari da hamsim taci bugu gurin Gwoggonta domin duk wanda ta tsayar haka yake ce mata. Shada tayi akan ta sayar ta hau tasan dai bugu kam sai ta shashi haka ta fara ƙoƙarin tsayarwa amma duk wanda ta tsayar basu tsayawa sakamakon hadarin da ya ƙara turniƙe garin na Abuja har yayyafi aka fara, duk ta tsure sai kama hijabinta take daidai tsayuwar wata ƙatuwar mota. “Yan mata ina zaki?” Mai motar ya tambaya bayan yayi parking ya buɗe gilas ɗin gaban motar. Gabanta ne ya buga amma bata da zaɓi dole a wannan lokacin tana amsa mishi saboda tana buƙatar temakon nasa tabbas. Cikin rawar murya da sanyi ta ce”Maitama zani” “Hanyar za mubi zo mu rage miki hanya” Ma tuƙin motar ya faɗa domin sai yanzu na lura ashe su biyu ne cikin motar, matasa ne da baza su wuce 32 ba, ba yadda ta iya dan har ruwa ya fara sakkowa, ganin ya buɗe mata back sit da sauri ta shiga tare da furta “Na gode” Tun da suka hau titi ba wanda yayi magana har suka isa Maitama sai lokacin Matuƙin motar ya tambayeta inda zai ajiyeta domin an tsuge da ruwa sosai. Da sauri ta ta ɗago fuskarta domin ta cure guri guda sanyin gari da na Ac dake kunne a motar ya ƙara mata jin sanyi gashi daman basu shiri da sanyi har wata ƴar kyarma take. Kwatanta masa tayi har ƙofar gidan da suke zaune ya kaita. Tana niyyar fita ya ce”Sunana Faruuk ke baki faɗa mini naki sunan ba” Gabanta ya buga sosai “Faruuk!” Ta nanata cikin sanyi ta ce”Na gode sunana Tataah!” Daga haka ta fita da sauri, da gudu ta shiga cikin madaidaicin gidan. Tana motar Faruuk yayi abokinsa dake gefe mai suna Ma’aruf ya ce”Faruuk ka cika kwashe-kwashe daga temako mene ne kuma na faɗa mata sunanka da tambayar nata, bakaji rainin wayaun da ta maka ba wai Tataah wannan suna ne?” Murmushi ne ɗauke fuskar Faruuk ya ce”Tun da kaji ta ce haka to sunan nata kenan, ni fa ban faɗa mata sunana da wata manufa ba, kamar yarda ban tambayi nata da niyyar komi ba” Taɓe baki Ma’aruf yayi tare da lumshe idanuwanshi da haka suka ƙarasa gida.
Tataah tana shiga kai tsaye ɗakin Ummanta ta nufa.
Da sauri ta ƙarasa gabanta ganinta kwance kamar yarda ta barta tun safe, daman tasan hakan zata kasance, kular hannunta ta ajiye tare da cire hijabin dake jikinta, kama mahaifiyar tata tayi tare da saka fillow ta jinginar da ita jikin bango. “Sannu Umma!” Ta furta cikin tsananin jin tausayin mahaifiyar tata, kallonta kawai Ummar ke yi ko ƙittawa babu, tsumma ta ɗauko tare da share mata miyun dake zuba a gefen bakinta sannan ta ɗebo ruwa ta kafa mata kai, sosai Ummar tasha ruwan da alamar ba ƙaramin ƙishi take ji ba ‘Dole taji ƙishi Tataah tun safe fa’ Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita. Bata cika mata ciki da ruwa ba da sauri ta ɗauko abincin da tazo dashi tare da cokali ta fara ba Umman, ta ɗan ci ba laifi sannan ta ƙara mata ruwa tasha, duk bayan minti ɗaya tana jerowa Ummar sannu. Ganin Ummar ta ƙoshi sai lokacin hankalinta ya kwanta ta ci ragowar itan ma tun safe sai yanzu take ci, bayan ta gama sake tattare ƙaramin ɗakin nasu tayi tare da ɗaurawa Umma alwala jin ana kiran sallar Magriba ita ma fita tayi ta ɗauro. Salla ta gabatar ita ma Umma a yadda take zaune take tata a haka. “Tataah! Tataah!! Tataah!!!” Yarda taji muryar mahaifinta na ƙwala mata kira yasa ƴan hancin cikinta murɗawa. Tana ƙoƙarin miƙewa sai gasu sun shugo ɗakin shi da Gwoggonta, jiki na rawa ta duƙa ƙasa “Gwoggo sannu da gida…” Tsawa ta daka mata “Baƙar munafuka algumguma me baƙin hali baƙar fuska! Ashe kin dawo hakima mandiya shine kika barni ina ta jiranki” A sanyaye ta ce”Kiyi Haƙuri lokacin da na shugo ana ruwa ne shiya…” “Dakata mini haka!!” Ta katseta ta hanyar daka mata tsawa. Baba ya ce”Amma me na ce miki akan idan kin dawo gidan nan?” Tuni idanuwanta suka cika da hawaye “Kace na fara zuwa na gaisheta tare da bata duka kuɗin aikin” “To uwar waye ya ce yau ki karya dokar” “Kuyi haƙuri wallahi ruwa akeyi lokacin” “Karya ne ai kafin magariba kike dawowa kuma sai da aka kira sallah aka fara ruwa” Da sauri Baban ya kalli Gwoggo da ba hakan bane amma kallon da ta wurga mishi ne yasa yayi saurin cewa”Haka ne” Jawota Gwoggo tayi tare da fara kilarta tana cewa”Saboda kin raina maganar ubanki danni nafi ƙarfin ki rainani, kin zo gurin nakasasshiyar uwarki da bata da mamora to bani kuɗin da uwarki gantalalliya kawai, a haka zaki ƙare a gantale ke da uwarki!” Jiki na rawa tana kuka ta ta miƙa mata kuɗin duka, Allah yaso ta cire ɗari biyun motar gobe da kuma ɗarin ta ta yau da Allah yasota aka rage mata hanya, dan da tasan tana cirewa bazata bari ba..
daga https://fb.com/hausaebooks
Tana amsa ta turata ta faɗi tare da tasa Baba gaba suka bar ɗakin. Tataah ɗagowa tayi tare da sakin ƙara ganin hannunta da ta ɗora a goshi da jini, sake kama goshinta tayi tare da sakin kuka…..
GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE
1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan
2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher
3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam
4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari
5_ AUREN WATA TARA👩❤️👨
Miss Hajo
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
………..🥚👩❤️👨💥🌎….
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76
MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO
Comments
Post a Comment