Main menu

Pages

MU GANI A KASA hot love story page 3 and 4

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

Page 3-4

Motsin da taji Ummanta nayi ne yasa ta saurin juyowa, da sauri ta ƙarasa kusa da ita. Hawayen da taga Umman nayi yasa ta mance da ciwon da ke goshinta, “Umma kuka? Mene ne ya faru? Dan Allah ki dena kuka Ummata!” Ta ƙarashe maganar ita ma tana hawayen tare da sharewa Umman nata hawayen. ‘Ina ma ina iya magana, ina ma komi nawa yana motsi, ina ma ina da lafiyar da zan iya tsayar da zubar hawayenki, Tataah da bakiyi kuka ba har ƙarshen rayuwarki’ Abin da Umma ke faɗa a zuciyarta kenan sai dai kamar yarda ta faɗa tabbas bata da damar hakan a yanzu. Tataah kuwa ganin tana goge mata hawayen amma wasu na zuba sai ita ta dena kukan nata cikin karyewar murya take faɗin “Umma na bari kema ki dena, zubar hawayenki tamkar ana ɗiga mini dalma ne a cikin jikina na bari” Ta faɗa da sakin dariya-dariya wacce take ta zallar yaƙe tana dariya amma hawaye na zuba. Jin ana kiran isha’i gabatarwa sukayi sannan Tataah ta jawo wani yaƙunannan zani ta shimfiɗa a inda zata kwanta ta gyarawa Umma kwanciyarta a saman tabarmar da ta gama fita hayyacinta sai zanin da ta shimfiɗa mata, wani tsohon bargo ta ɗauko ta lilliɓe Umman sakamakon ruwan saman da akayi ya sakar da sanyi me shiga jiki ita kuma ta rufe da hijabinta, haka bacci ya kwashe su daman suna sallahr isha’i take bacci saboda asubar fari take tashi. Ilai kuwa tun huɗu na asuba ta tashi alwala ta farayi tazo ta gabatar da nafila da yiwa Ummanta addu’ar samun lafiya kullum sai tayi wannan sallah dan roƙawa Ummanta samun sauƙi gurin sarki Allah. Bayan idarwarta fita tayi ta fara share tsakar gidan wanda hasken sola ya mamaye ta ɗayan gidan dake jikin nasu ne, mai gidan ya basu wannan ƙaramin suke zaune to har solar dake gidansa ya jona musu. Bayan kammalawarta ne ta shiga kitchen wanke-wanke tayi tare da gyara kitchen ɗin dake kaca-kaca kuma kullum sai ta gyara amma haka zata dawo ta iske shi kamar anyi yaƙi da kaya a cikin shi, fitowa tayi daidai kiran sallar asubahi wanka tayi da ruwan sanyi sai kyarma take saboda sanyin da ake sannan ta ɗaura alwala ta shiga da ruwa tayiwa Umma wacce ta iske ta tashi alamar gaisheta tayi sannan ta jinginar da ita domin tayi sallah. Ita ma ta gabatar da tata, ko man shafawa bata da zarrar shafa shi domin basu dashi, ta daɗe zaune tana lazumi ƙarfe shidda nayi ta miƙe ruwa ta bawa Umma tasha sannan ta gyara mata kwanciya tare da tofa mata addu’o’i cikin sanyinta ta ce”Kiyi haƙuri Umma yau ma haka zan fita ba tare da kinci komi ba, anan babu shago balle na sayo miki ko wani abu ne da nera ɗarin jiya, amma kiyi haƙuri har na dawo” Ɗan lumshe idanuwanta tayi wanda shine kawai ke aiki a jikinta alama ce ta mata da ba komi, jiki a matukar sanyaye ta fita tare da ja mata ƙofa. Kamar yadda Babanta ya sanar da ita ƙa’ida ne taje gaida Gwoggo kafin ta wuce haka ta shiga amma sai ta iske tana barci kamar kullum Baba ne zaune bakin ƙofa yana wankin Gwoggo da yaranta biyu mace da namiji ƙanne a gurin Tataah. Sudees da Tataah ta girma da shekaru biyu sai Ruhaima wacce ta girmi Tataah da shekara ɗaya amma sune BAba ke yiwa wanki, har ƙasa ta duƙa. “Baba ina kwana” Da sauri ya ɗago dan sam bai lura da zuwanta ba sai maganarta yaji, duba gefe da gefensa yayi dan ko gaisuwarta Gwoggo ta hana ya amsa a hankali ya ce”Lafiya ƙalau Tataah zaki wuce gurin aikin ne?” Gyaɗa kai tayi alamar “I” Ba tare da ta ce komi ba, shuru ya biyo baya na ɗan wani lokaci a hankali ya ce”Ki tashi kije kawai basu tashi bacci ba” Miƙewa tayi tana tafiya a hankali ba tare da ta ce ƙala ba, yabi bayanta da kallo yana girgiza kansa. Tayi tafiya mai nisa kafin ta iso bakin titi sannan ta daɗe tsaye kafin ta samu abin hawa, lokacin da ta isa gidan abincin bakwai saura minti goma, hamdala tayi domin ƙa’idar shiga gurin bakwai ne bata san latti kamar yadda aka gargaɗe su da hakan shiyasa take fitowa da wuri. “Baki latti har kin iso?” Ɗan murmushi tayi bata ce mishi komi ba, ciwon da ya gani a goshinta ne yasa shi salati tare da faɗin “Ciwo kikaji?” Sai lokacin ta tuna da ciwon ta ce”Faɗuwa nayi!’ Tare da wucewa dan bata san wata magana kuma akan ciwon. Lawan abokin aikinta ne a gurin suna ɗan gaisawa da shi amma ita ba da kowa take magana ba saboda kamun kai da gudun shiga abin da bai dameta ba. Gurin masu girki ta ƙarasa tana temaka musu duk da ba aikinta bane amma tana sa hannu don sam bata da ƙiwwar aiki, suma duk suka tambayeta ciwon abin da ta cewa Lawan shi ta maimaita musu, wajen takwas duk an gama wasu yayin da kuma wasu aka barsu a wuta saboda karsu huce. Mutane ma banbanta ne ke ta shugowa gurin abincin saboda sunan da gurin ya yi ana son abincin gurin sosai ko ba komi akwai tsafta ga daɗin abinci.
Tun bayan barin shi gurin abincin yake yawan tuno fuskar yarinyar, yaja tsaki yafi cikon masaki, kai tsaye gida ya wuce daret part ɗinsa ya shiga saman bed ya faɗa nan take kuwa barci me nauyi ya ɗauke shi. Ya daɗe yana barcin har zuwa lokacin da aka fara ruwan sama, sanyayyen sanyin da ake ne ya ƙarawa barcin nashi armashi ya shige cikin bargo ya naɗe yana kwasar baccinsa. Yaye bargon da akayi ne yasa shi buɗe idanuwa a hankali, idanuwansa suka sauka akan Faruuk dake riƙe da bargon, guntun tsaki yaja tare da gyara kwanciyarsa ba tare da yayi magana ba. “Aliyu magana fa nake” Ma’aruf da ya ƙarasa shugowa ne ya ce”Kai sai kace baka san wane ne Aliyu ba, ka barshi fa idan ba haushi ne kake so ya kar ka ba” Zaunawa Faruuk ya yi bakin bed ɗin yana faɗin “Tun jiya da yake ƙasar jajayen can nake kiransa yana wulakantani amma ba komi na shi auren zai zo ne?” Jin abin da Faruuk ya faɗa ne yasa shi tashi yana ɓata fuska “Auren wa?” Ya tambaya so silent, Ma’aruf ya ce “Aurenka! Ko bazakayi ba ne?” Ɗan smile ya saki na gefen baki kafin ya ce”Ku dai fitinannu Allah ya baku sa’a, ku dena lissafi da ni” Dariya suka saka su biyun har da tafawa “Ana maganar fitina har kai kayi magana Aliyu, wannan baccin ma da kake daga gani na wahala ne” Cewar Faruuk. Tsaki Abuturrab yaja tare da miƙewa ya nufi bathroom ba tare da ya ce musu komi ba, su kuwa dariyar shaƙiyanci sukaci gaba da yi mishi. Bayan ya fito dukansu sukayi alwala sannan suka wuce masallaci jin ana tada salla. Ko da suka dawo cikin gidan suka nufa Ammi tasa house girl ɗinta ta shirya musu komi. Aliyu ko kallon abincin bai yi ba, Faruuk daman yasan baci zai yi ba hakan yasa duka suka tashi kai tsaye motar Faruuk suka hau duka suka nufi Husse two gidansu Faruuk. Ammi da ta fito bin gurin tayi da kallo sosai ranta ya ɓaci da ganin abin da sukayi “Abuturrab!” Ta furta da huci kafin ta tuno Faruuk “Shege yaro da maƙar fuskarsa irin ta uwarsa wallahi duka sai nayi maganinku mtsuuuw!” Ta ƙarashe maganarta da jan tsaki. Sareenah wacce ta fito yanzu ita ma bin gurin tayi da kallo kafin ta ce”Ammi ina su Yaya Aliyun?” “Yadda kika ga gurin wayam haka nima na fito na gani, ai kin san wannan Faruuk ɗin idan har suna tare komi yayi shi Abuturrab ke yi” Sareenah da idanuwanta yayi ja saboda ɓacin rai ta ce”Wallahi ba tun yau ba na tsani Faruuk kina ganin ko gani na yayi sai ya dinga mini wani kallo a raine” “Barni da shi daga shi har uwarsa na tsane su kuma nice maganinsu, kwanaki akan uwar Faruuk sai da mukayi faɗa da Alhaji kin san ƙanwarsa ce kuma su biyu uwarsu ta haifa sonta yake kamar me, ni kuma bazan iya jura ba” Sareenah kasa cewa komi tayi sai numfashi da take saki cike da jin tsanar Faruuk a ranta.
Sosai Mami ta cikawa su Abuturrab gaba da abinci, cikin farin ciki suka fara cin daddaɗan abinci Mami da ta kasance gwana gurin iya tsara girki. Faruuk ya kai lomar jellop rice bakin shi da taji haɗi na musamman ya ce”Mami gaskiya ko dai anan gidan zamu zauba da Rahina domin ta iya girki kamar naki?” Abuturrab ya ɓata rai kafin ya ce”Sai ana maganar mutane kana sako wannan ƙwailar yarinyar dan Allah ka din ga magana irin ta mutane” A yadda yayi maganar sai ka rantse da Allah ba shine ya yi ta ba domin laɓɓan sa ne kawai ke motsawa Faruuk ne kawai yaji mai ya ce yadda kuma ya mayar da hankalinsa wajen cin abincinsa sai ka rantse da Allah ba shine yayi maganar ba. Mami kam murmushi take ta ce”Wallahi ba dani ba wai gaɗa a hurumi, me zai jani zama da ku a gidan nan? To sai dai idan wata laluuraramma kaje da matarka can da rawar kanka” Tana faɗa ta miƙe ta basu guri, dan tasan halin Faruuk da shegen rawar kai yanzu sai ya ce zaiyi wata maganar. Faruuk ya mai da hankalinsa gurin Abuturrab bayan wucewar Mami “Limamin bayan fage me kake cewa ɗazun?” Banza Aliyu yayi masa yana ci gaba da cin abincin. “Da a maimaita mana da anji zazzafar amsa” “Mtsuw!” Abuturrab yaja tsaki ba tare da ya kuma cewa komi ba har suka ida. Ganin lokaci yaja ya ce”Malam zo ka mayar dani gida dare nayi” “Gida kuma? Wallahi baka isa ba zance zaku raka ni gurin Rahina” Ɗan zaro ido Abuturrab yayi alamar tsoro kafin ya ce”Zance? Mene ne hakan!” “Oho dai idan mun je ka san ko mene ne” Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa cikin cool voice ɗin sa ya ce”Allah ya raka taki gona ba da Aliyu za a ganin shirme ba” Wata muguwar dariya Faruuk ya saki Ma’aruf ya ce”Ina rabaka da kiwo kana ƙyalla ta mutu Aliyu, kar nan gaba kaɗan ka afka ƙaton tafkin so kafi mu zaƙewa” “Allah sitiri buƙwi ba da ni ba” “Wai nikam ina kaji hausa ne?” Ɗan murmushi ya yi tunowa da wani abu kafin ya basar bai ce komi ba. Faruuk shi ya maida Aliyu gida kafin ya sauke Ma’aruf a nasu gidan sannan ya wuce gida dan sanyin da ruwan saman da akayi ya sakar yasa shi jin bazai iya zuwa gurin Rahina a yau ba.
Ammi da ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Abuturrab anan bacci ya yi gaba da ita, duk a tunaninta da mota ya fita idan ya dawo dole zataji ƙarar motarsa, shi kuwa a bakin gate yasa Faruuk ya ajiye shi sannan ya shugo ta ƙaramar ƙofa, daret part ɗin sa ya nufa bai ma yi tunanin shiga part ɗin Ammin ba. Coppe ya haɗa yana sha a hankali daidai ringing ɗin wayarsa, jawo wayar yayi ganin mai kiran yaja tsaki kafin ya ɗauka. “Lafiya cikin tsohon daren nan?” Sanyayyar ajiyar zuciya ta saki wanda shi kansa da yaji ta, cikin kwantar da murya ta ce”Tun ɗazu nake turo maka saƙo ba amsa, daman so nake naji ko ka sauka lafiya?” Huci ya fesar me zafi kafin ya ce”Baheerah please ki bar ni, wai ana so dole ne?” Tun kan ya sauke numfashi ya fara jin ƙarar kukanta Ƙit! ya yanke kiran cike da fusatuwa ji yayi coppe ɗin ma ya fita ranshi kitchen ya mayar tare da shigewa bedroom sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kunna na’ura me ɗumama ɗaki. Sareenah ce ta fito cikin sanɗa ta niyyarta na barin gidan domin saurayinta ya kirata yana wuce zasu wuce club, ganin Ammi a parlour taji ranta ya ɓaci, gurinta ta ƙarasa sai ta tarad da bacci take mai nauyi ajiyar zuciya ta saki tare da ficewa daga parlourn cikin sauri. Officer na ganinta ya sara mata “Ranki ya daɗe barka da fitowa” Murmushi ta saki tare da zage zagarta ta ciro dubu biyar ta bashi. Godiya ya fara mata da wasata ta ce”Kamar kullum kar wanda yasan da fitar nan, har Ammi” “An gama ranki ya daɗe” Har takai gate kuma ta juyo “Officer Yaya Aliyu ya dawo kuwa?” “I Ya shugo tun ɗazu kuwa” Gyaɗa kai tayi tare da fita daga gidan, nesa kaɗan da gidan ta hango shi cikin baƙar motarsa da sauri ta ƙarasa, tun kafin ta iso ya buɗe mata gaban motar, murmushi suka sakarwa juna “Ma’aruf!!!” Ta ambaci sunansa cike da ƙwarewa. Tada motar yayi sai da ya hau titi ya ce”Sareenah ta Aliyu” Gabaɗaya suka saka dariya ta ce”Har kasa naji wani sanyi, amma nazu raina ya ɓaci da Faruuk ya jaku wallahi ban taɓa tsanar wani irin Faruuk ba” Numfashi ya fesar da cewa”Faruuk bai da matsala jininku ne kawai bai zo daidai ba, shi ya mayar dani gida yana wucewa kuma na samɓo nan” Dariya tayi ta ce”Shi ya sa fa nake ƙaunarka kai ma kasan kan bariki” Ya ce”Hahahaha Sareenah kenan” Da wannan hirar suka ƙarasa shahararren gidan rawar dake garin na Abuja. Guri suka samu sukayi ciye-ciyensu da shaye-shayensu abin da Aliyu ko Faruuk basu san Ma’aruf nayi ba kenan. Daga ƙarshe ma ɗaki suka kama suka gama sheɗancinsu. Sareenah bata dawo gidan ba sai wajen biyar na asubahi, har lokacin Ammi na gurin tana sharara bacci, kasancewar Sareenah ba cikin hayyacinta ta ke ba yasa bata lura da ita ba bedroom ɗinta ta wuce tana zuwa ta faɗa saman bed wani fitinannan bacci ya yi awon gaba da ita….

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

Comments

table of contents title