Main menu

Pages

MU GANI A KASA Page 11 and 12

  • MU GANI A ƘASA…
  • Hot Love
  • Written by FATIMA SUNUSI RABIU
  • UMMU AFFAN

Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga AMINATU SANI da kuma MAMAN YASEER da MINATU da HAJIYAR ALLAH, Comments ɗinku na sani nishaɗi Allah ya bar zuminci. Masoya littafin nan duk kuna raina ina ƙaunarku tamkar yadda kuke ƙaunar MU GANI A ƘASA… Tabbas kuna nunawa labarin ƙauna na gode.

YA KUSA FITA KASUWA, MAI BUƘATAR BUGAGGENSA 1K NE KACAL YA MIN MAGANA TA 08104335144

Page 11-12

Numfashi ya sauke tare da fesar da wani huci me zafi idanuwansa akan Daddy. Shima zuba mishi ido yayi kafin ya furta, “Kana da wata maganar ne Son?” A hankali ya girgiza kai alamar “A’a” Daddy ya ce”To ya kamata dai ayi maganar auren naka, domin zama a haka bai kamace ka ba” Ammi da ta zauna yanzu ta ɗaura da ce wa”Ƙwarai kuwa Alhaji kullum maganar da nake mishi kenan amma yaƙi ya gane, to Faruuk dai yayi kai ma sai ka bada azama” Zaiyi magana ya fasa sakamakon sallamar Alhaji Hassan mahaifin su Faruuk.

Sosai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, tun da ya shufo parlourn ya kafeshi da idanu tamkar a ranar ne ya fara ganinsa. Daddy ya miƙe ya tarbi surukin nasa cikin fara’a da girmamawa, hannu suka ba juna bayan sun gaisa duka suka zauna a tare, Ammi ta gaishesa Aliyu kam ya kasa cewa komi sai gabansa da ke yawan faɗuwa. Alhaji Hassan ya ce”Aliyu baka koma bakin aiki ba kenan?” Sai lokacin ya iya sauke kan shi daga duban da yake mishi cikin mury me sanyi ya ce”Jibi nake saka ran komawa Abba, ina wuni?” “Lafiya ƙalau, to ma sha Allahu. Allah ya temaka!” “Amin Abba na gode.”
Sannan suka gaisa da Ammi ma. Gyara zama yayi yana duban Daddyn Aliyu ya ce”Aliyu ya faɗa maka abin da ya faru a masallaci kuwa?” Damm! Ƙirjin Aliyu ya bada wani sauti, kafe Abba yayi da ido ba tare da ya iya furta ko da kalma ɗaya ba ce.

Karanta MU GANI A KASA hot love story page 3 and 4

Daddy ya ɗan muskuta ya ce”Bai faɗa mini komi ba, mene ne ya faru Alhaji? Kasan Aliyu da zurfin ciki ga miskilanci na tsiya!” Abba ya ce”Duk zurfin cikinsa bai kamata ya ɓoye irin wannan magana va, domin ba abar ɓoyewa bace” Nan take ya basu labarin kaf abin da ya faru da auren da aka ɗaurawa Abuturrab. Daddy kafe Aliyu yayi da ido wanda yayi saurin sadda kan shi ƙasa. Ammi ta miƙe da sauri “Haba Alhaji Hassan ya za a haɗa baki da kai a aikata wannan babban kuskuren? Wallahi wannan auren bai auru ba.” Kallonta Abba yayi ya ce”Tabbas aure kam ya auru, idan ba me shi ne ya warware kayanshi ba, amma tabbas Aliyu yana da aure” “To ba zai yuwu ba!” Ammi ta furta da ƙarfi harta miƙewa ta ɗaura da cewa”Idan ban da an mayar da Alhajin shashasha sai ayiwa ɗansa irin wannan gantalallan auren? To ba zai yuwu ba yadda aka haɗa baki da kai aka ɗaura shi haka zaka nemo gantalallun iyayenta a kwance shi domin ba zai taɓa saɓuwa ba wai allura a cikin ruwa.” Daddy da tun ɗazu baiyi magana ba sai yanzu ya kauda idanuwansa akan Aliyu ya ɗaurasu kan Abba kafin ya ce”Amma Alhaji kana gani Aliyu zaiyi irin wannan wulaƙantaccen auren ka kasa dakatar da shi?”

Post and Published at https://dlhausanovels.com.ng


“Alhaji Muhammad bai kamata ka furta irin wannan kalma ba” Cewar Abba yana duban Daddyn Aliyu kafin ya ɗaura da cewa”Ko wanne aure ba wulaƙantacce ba ne, baka sani ba ko wannan da kake ganin wulaƙancewarsa shine me tarin albarkar akan wannan yaro, ba zato ba tsammani har mutum ya ɗauki auren ƴarsa bai san waye kai ba ya baka, idan baka gode mishi ba ai baka tsine mishi ba.” “Waye shi, me ya mallaka a garin nan ƙasar nan da wajen ƙasar nan da har zai ba ɗa kamar Abuturrab?” Cewar Ammi a ƙufule ta ɗaura da cewa”Wallahi Aliyu yafi ƙarfin ƴar sadaka, Allah sitiri biƙu, yo Mu gani a ƙasa… Wannan ma zancen banza zancen wofi ne, daman can an haɗa baki da kai ne domin a cuci Aliyu domin wannan auren ba na Allah da Annabi ba ne” Daddy zaiyi magana Aliyu yayi saurin cewa”Daddy and Ammi ku kwantar da hankalinku, sannan ku dena cewa da haɗin bakin Abba akan auren nan nawa, domin babu ruwansa hasalima shi sadaki ya miyamin da me zan iya biyansa?” “Sadakin banza da wofi, Aliyu bana so ka tafka uban kuren da zakazo kana danasani, dubu hamsim ko albashin me gadin gidanka ya wuce wannan ballantana kuma ace ga matar da zaka aura? Shin kai kuwa kasan irin matar da ta dace da kai?” Ammi ta furta cikin tsantasar ɓacin rai. Numfashi ya sauke domin magana me yawa wahala dake bashi abin baiyi tunanin duk zasu ɗaurawa Abba laifi ba. Daddy ya ce”Aliyu da sa hannunka akayi wannan gantalewar ta aurenka?” Da sauri ya gyaɗa kai alamar “I” Ya ɗaura da cewa”Abba yana zaune ne a gurin amma ni ne nacewa uban yarinyar ina son aurenta.” Dam ƙirjinsa ya buga jin maganar da ya faɗa tare da ƙasa da idanuwansa domin baya son haɗa ido da Daddy. Shi kuwa Daddy murmushi ya yi ya ce”Babbar damuwata yi maka abin da baka so, tun da har kai ka aminta da auren to Allah yasa alkhairi yasa abokiyar alkhairinka ce uwar zuri’arka” Abba ne ya amsa da “Ameen!” Ammi ta ce, “Yanzu Alhaji ka bada goyan bayan wannan gantalallan auren wanda baka san da shi ba? To ba zai yuwu ba.” Da sauri Aliyu ya miƙe tare da cewa Abba “Taso muje Abba” Babu musu yabi bayansa. Ammi kamar jira take su fita ta fara surfa ruwan bala’i.
Daddy dai bai kulata ba har dai da ya gaji shima ya fice, abin da ya ƙara fusata ta, ta dunga masifa ita ɗaya kamar mahaukaciya sabon kamu, wai har Aliyu ne zai aure ba tare da saninsu ba, babban tashin hankalinta ma irin halin da Sareenah zata shiga muddin taji wannan maganar….. A hankali ta fito sanye da dogon hijabinta har ƙasa, “Mtsuww!” Gwoggo taja tsaki kafin tayi gaba. Tataah ta bi bayanta jiki a sanyaye. Kekenapep Gwoggo ta tara suka shiga har lokacin Tataah kanta a ƙasa yake sam bata so ko ido su haɗa da Gwoggon, sun ɗanyi tafiya kusan ta minti goma kafin napep ɗin ya tsaya bakin wani ƙaton gate. Sauka Gwoggo tayi tana ciro kuɗi a jaka, hakan yasa Tataah saukowa don ta rura an kawo inda zasu kenan, Gwoggo na biyan kuɗin ta juya tare da nufar gate ɗin, da sauri tabi bayanta tana duba haɗuwa irin ta gidan. Ƙwanƙwasawa Gwoggo tayi mai gadi ne ya leƙo, ganin Gwoggo suka gaisa kafin ya basu hanya suka shiga ciki. Kai ma sha Allah ba a cewa komi gida ne da ya tara komi, ba shida girma sosai amma ba ƙarami can ba ne, sosai madaidaicin parlourn zai burgeka saboda yadda aka tsara komi a muhallinsa parlourn bai cika tarkace ba tamkar gidan turawa komi cikin tsari. Gwoggo ta zauna saman ɗaya daga cikin jerin kujerun dake parlourn, Tataah sami guri saman carpet ta zauna kanta a ƙasa gabanta na faɗuwa. Gwoggo ta ciro waya tare da yin kira “I Mun ƙaraso!” Abin da Tataah taji ta faɗa kenan ta katse kiran. Kusan minti biyar kafin wata dattijuwar mata da zata kai shekaru hamsin da biyar ta sakko daga benen dake parlourn. Gwoggo na ganinta ta fara washe baki kamar gonar auduga, “Hajiya barka da marece, fatan mun same ku ƙalau?” Sai da matar ta zauna kafin ta ce”AlhamduLillah!” A takaice Gwoggo har da duƙawa ƙasa kamar zatayiwa matar sujjada ta ce”Hajiya kiyi haƙuri fa, da ba wannan yarinyar naso miki ba a can ƙauye na aika ganin har yanzu ba a kawo su ba ita kuma wannan ta yiwa waccen aikin nata riƙon sakainar kashi nace bari na kawota nan kawai.” Matar wacce da alamar zantukan Gwoggo sun fara isarta ta ce”Ya isa haka, zaki iya tafiya” Jiki a sanyaye Gwoggo ta miƙe tana hararata “Wallahi idan bakiyi abin da ya dace ba sai kinji a jikinki na dai faɗa miki” Kaina na sadda ƙasa cike da jin takaici a raina sai dai bani da yadda zanyi, har Gwoggon ta kusan fita Hajiyar nan ta kirata, wasu maƙudan kuɗi ta miƙa mata da bazan iya cewa ga yawansu ba, ai nan bakin gwoggo ya buɗe ta dunga ƙwararo godiya kamar ƙyautarsu aka bata! Kodayake a gurinta tamkar ƙyauta ne tun da ba ita zatayi aikin wahalar ba. Da haka ta fice a parlourn. Tataah tana zaune tamkar kayan wanki ba wanda yayi magana daga ita har Hajiyar kusan minti goma suna zaune kamar kurame “Halan a gidanku ba a koya miki yadda ake girmama na gaba ba ne?” Tambayar da Hajiyar ta banko mata ta sauka cikin masarrafar sautinta. Bata ɗago ba domin batayi tunanin da ita take ba ganin tun da ta shugo magana bata haɗasu ba. Hakan da tayi kuwa ya ƙara baƙanta zuciyar Hajiyar ta ce”Titaa kike ko Tataah ba magana nake miki ba?” Sai lokacin ta ɗago cikin sanyinta ta ce”Kiyi haƙuri banyi zaton da ni kike ba!” Mtsuwww taja tsaki tare da miƙewa. “Hajara! Hajara!!” Da sauri wata matashiyar mata da bazata wuce shekaru talatin da ɗoriya ba ta fito, kanta a ƙasa ta ce”Barka da fitowa Hajiya” Bata amsa mata ba ta ce”Ga sabuwar ƴar aiki nan, zata zauna ɓangaren Baheerah ne da zatw dawo gobe, dan haka ki nuna mata duka aikinta.” “Angama Hajiya!” Matar ta faɗa Hajiyar ta koma sama ita kuma Hajara ta ce”Yarinya taso muje” Babu musu Tataah ta miƙe, wani part aka kaita wanda suke haɗe da wanda ta fito, sai dai shi bai kai girman na farkon ba yafi shi ƙanƙanta sosai dan ƙaramin parlour ne da ɗakin bacci guda ɗaya sai toilet da ƙaramin kitchen. Saman kujerar da duk tayi ƙura Hajara ta zauna, Tataah kuma tana tsaye domin ƙurar parlourn tayi yawa da bazata iya zama ba da alama an daɗe ba a shugo gurin ba. Hajara ta ce”Sunana Hajara a ɓangaren Hajiya nake aiki ke mene ne sunanki?” “Sunana Tataah!” “Tataah kuma? Ai Tataah ba suna bane” “Uhmmm!” Kawai ta iya cewa domin bata jin zata faɗi sunanta na gaskiya a yanzu. “Ok tun da baki san faɗa mini bazan takuraki ba” Duk abin da zatayi Hajara ta nuna mata kafin ta fita. Tataah kwaɓewa tayi ta fara da gyara parlourn sannan tayi moping tas parlourn, ta shiga ɗakin baccinta nan ma ta share da goge, duk wasu kayan wanki ta haɗasu guri ɗaya sannan ta koma kitchen nan ma ba ƙaramin aiki tayi ba.
Duk kayan kitchen ɗin ta wanke ta goge komi su gas saman das ɗin kitchen ɗin da frigde sannan tayi mopping. Toilet ta wuce shima ba ƙaramin wanki tayi mishi ba, A wahale ta dawo parlour ga wata yunwa da take ji, Haraja ce da Hajiyar nan suka shugo, ko ina Hajiya ta fara duba. Hajara ta ce”Sannu da ƙoƙari Tataah duk kin gama aikin? Ina ta ƙoƙarin na ida girki nazo na kama miki” Ƙasa tayi da kai tare da cewa”Ba komi Aunty” Wace baki Hajara tayi cike da jin daɗin sunan da Tataah ta kirata. Hajiya ta ce”Kinyi ƙoƙari Tataah” “Na gode Hajiya!” Hanyar fita ta nufa tana cewa”Hajara idan ta huta taci abinci ki tayata wankin kayan Baheerah” Cike da girmamawa Hajara ta ce”Angama Hajiya” Sallah suka farayi tare da Hajara sannan ta kawo musu abinci mai rai da lafiya sukaci, tana ci tana tunanin Ummanta a hankali ta ce”Aunty har abincin dare za a dinga bamu?” Hajara ta washe baki ta ce”I Mana ai ya zama dole, nifa ke girkawa” Numfashi Tataah ta sauke ta ce”Toni bazan dinga cin na dare anan ba a dunga samin a leda ina tafiya gida da shi” Da sauri Hajara ta dubeta ta ce”Saboda me ƙanwata?” Sadda kai ƙasa Tataah tayi ba tare da ta ce komi ba. Hajara ta lura yarinyar ba mai buɗe ruwan cikinta bace tun da tayi shuru sai bata ƙara tambayarta ba, da haka suka kammala, wajajen ƙarfe bakwai bayan tayi sallar magrib tayi musu sallama Hajara ta zuba mata abinci a wata roba me kyau me murfi sannan sukayi sallama ta wuce gida….

http://aihausanovels.com.ng

FARATAN ZAKI Chapter 8 – littafin yaki

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

Comments

table of contents title