Main menu

Pages

MU GANI A KASA page 5 to 10 hot hausa novel by Fatima S Rabiu

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

https://arewabooks.com/u/ummuaffan Kubi link ɗin nan domin yin following ɗina arewabooks please. Sannan acan nake fara posting kafin nan.👎

Page 5-6

Tataah Pov.
“Tataah lafiyarki kuwa?” Da sauri ta juyo don har yaso ya tsorata ta. Numfashi ta sauke tare da sakin murmushin yaƙe. Farhan ne ɗa a gurin Madam ɗin su saurayi ne sosai bai daɗe da dawowa karatunsa ba a ƙasar waje. “Babu komi Yaya Farhan!” Girgiza kai yayi tare da zama gefenta “Ban yadda ba, ko dai kina jin yunwa ne?” Tayi mamakin tambayar da ya mata, tabbas yunwa take ji amma bazata iya cin komi ba saboda tunanin halin da ta baro Ummanta, ganin tayi ƙasa da kai tashi ya yi sai gashi da abinci ya miƙa mata, da sauri ta girgiza kai alamar a’a. Zaunawa yayi yana dubanta sosai “Tataah baki yadda da ni bane” Sadda kai ƙasa tayi cikin sanyinta ta ce”Ba haka bane” “To mene ne?” Kasa cewa komi tayi ta amshi abincin dan bata san tana cika gaddama da mutum, cokali ɗaya taci ta tino da Umma ‘Yanzu a wanne hali take? Ita taci abincin ma kuwa? A’a ita ce amsar dan tasan idan suman mutuwa take Gwoggonta ba zata bata abinci ba. Hawaye ne suka gangaro idanuwanta da sauri ta goge dan bata san Farhan ya gane amma ta makaro “Tataah zan so naji tarihinki, ina jin tausayinki sosai a zuciyata” Kauda kai tayi ba tare da ta ce komi ba. “Dan Allah ki sanar da ni” “Jin sa bashi da wani amfani a tare da kai balle ni da na bayar” Zaiyi magana yaji Madam na kiransa. Ganin ya tashi da sauri ta sami leda ta juyo abincin taje cikin jakarta ta tura domin bata san ci ba tare da Ummanta ba balle har da nama yanka biyu ina zata iya ci ta bar Umma. Farhan ta hanga yana ɗaga mata hannu da alama tafiya zaiyi, gurin wanke-wanke ta ƙarasa ta wanke plate ɗin taje ta ajiye, wasu suka zo sayen abinci taje tambayarsu abin da za a kawo musu, ɗaya cikinsu ya dinga kallonta yana lasar baki, sam bata lura dashi ba sai da ta kai abincin sai ji tayi mutum ya riƙe mata hannu, da sauri ta fincike jikinta na rawa sosai. Ya ce”Dalla can na gani na yaba da yarintarki dare ɗaya zaki bani biya na musamman” Zaro ido tayi tsoro mai tsanani ya shigeta baya ta fara tana girgiza kanta ganin haka ya taso tare da riƙeta, nan fa suka fara kokawa ga mutane a gurin amma kowa harkar gabansa yake ba wanda ya damu dasu (Matsalar bariki kenan) girgiza kai take hawaye masu zafi suna zuba a idanuwanta gashi ta kasa magana, janta yake tare da nufar gurin motarshi da ita “Madamm!!!” Ta kira sunan da karfi, da sauri ta fito jin muryar Tataah. Ƙarasawa tayi gurin da sauri tana cewa”Alhaji dan Allah kayi haƙuri wannan ba irin waɗanda kake tunani ba ce, dan Allah ka rabu da ita!” Wani banzan kallo ya mata ya ce”Bana haƙuri da duk abin da naji ya mini” Girgiza kai Madam keyi cike da jin tausayin Tataah dan har cikin zuciyarta yarinyar ke bata tausayi. Tataah ganin ba wanda zai ceceta kuma wannan mugun da yayi jika da ita ba imani a kamanninsa yasa ta saka haƙoranta tare da gantsara mashi wani mugun cizo. Ai kuwa ba shiri ya saki hannun tare da riƙe hannun nasa, ita kuwa tuni ta arta a saba’in tana ihuw da kuka. Gudu take saman babban titin sam ta fita a hayyacinta, gani take kamar yana bin ta saboda tsoratar da tayi, ƙarar motar da taji bai sata tsayawa ba ta ci gaba da gudu. Ai batayi aune ba taga mota a gabanta ƙara ta saki tare da ɗaura hannu aka ta zube a gurin… Aliyu pov.
Asubar fari ya tashi tare da shiga bathroom ya ɗauro alwala ya nufi masallaci, ko da aka idar da sallah bai shugo gida ba sai wajen shidda na safe, yasan Ammi bata tashi ba dan idan tayi salah tana komawa baccin safe hakanne yasa ya koma part ɗinsa, niyyar kwanciya yake yaji ƙarar wayarsa, ɗan tsaki yaja tare da kai idanuwansa saman wayar. ‘My Dad’ abin da ya gani saman screen ɗin wayar da sauri ya ɗauka dan yayi tunanin Baheerah ce. “Assalamu alaikum” Yayi masa sallama, amsawa yayi Aliyu ya gaishesa ya ce”Daddy da safe haka, Allah yasa lafiya?” Murmushi Daddy ya yi mai sauti har Aliyu yana ji kafin ya ce”Abuturrab ya ka dawo gida?” “AlhamduLillah Daddy!” “Ka koma aikin ne” Tura baki ya yi kamar Daddyn na gabansa ya ce”No Dad ai na ɗauki hutu, sai nan da sati ɗaya” “Ok yayi Alhaji Tasiu ke sanar da ni an kwantar da Baheerah asibiti kaji kuwa” Dam gabansa ya buga amma ba yadda za ayi ka fahimci hakan ya ce”Ban ji ba zan kirata in sha Allahu” “Ya kamata kam, nima cikin satin nan zan dawo” “Tom Dad Allah ya dawo da kai lafiya” Da “Amin” Ya amsa tare da katse kiran. Bin wayar yayi da kallo yana tunanin me zai sa Daddy sanar da shi ciwon Baheerah? Tabbas ɗiyar amininsa ce amma bai taɓa kawo hakan a zuciyarsa ba ‘Allah yasa ba sanar da su tayi abin da ta sanar masa ba” Mtsuww! Yaja tsaki idan ma sanar dasu tayi can dasu gada shi ba ruwan shi. Gado ya faɗa domin yana san ya more hutunsa na satin da ya ɗauka kafin a koma fagen daga, kusan sha ɗaya ya farko wanka yayi tare da brush ya nufi part ɗin Ammi dan ya gaisheta. Ba kowa parlour yasan da wuya ma idan ta tashi fita yayi tare da wucewa gidansu Faruuk can ya karya Mami ta ce”Wallahi gara kuyi-kuyi aure ko ma huta da ciyar daku” Ƙasa yayi da kai bai ce komi ba daman tasan da wuya ta tanka miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi, bayan ya gama office ɗin Faruuk ya wuce can ya kusan awa uku sallar Azhar ta fito dasu bayan su idar yayi mishi sallama ya nufi hanyar gidan saboda miscalls ɗin Ammi da ya gani kusan biyar lokacin suna sallah ta kira shi. Yana hanya tun daga nesa ya hango kamar mutum na gudu a titi haka dai yaci gaba da rahowa hr zuwa lokacin da ya ƙaraso gab da ita a tunaninsa mahaukaciyace saboda yadda take gudu tana waugen bayanta, duk ƙoƙarin kauce mata da yake amma haka ta tunkarosa wani wawan burgi yaja daidai ƙafafuwanta ganin yadda ta zube masa a gaban mota ne yasa shi fitowa da sauri.
Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komi ba kusan na minti biyu, kafin ya koma motarsa baya yaja ya kauce mata tare da fusgar motar a sittin. Nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da bin bayan motar shi da kallo, ta daɗe a gurin kafin ta tashi jiki a sanyaye ta fara tafiya a hankali domin ƙafafuwanta ba kaɗan suke mata zafi ba, tunani ta fara ta nufi guda ko ta koma gurin Madam? Tasan muddin ta koma gida Gwoggo sai ta kusan kasheta da bugu, gurin Madam kuma tana tsoro karta koma Alhajin nan ya kuma kamata, wannan shi ake kira da gaba giwa baya siyaki, haka tana sharar ƙwalla ta nufi hanyar da zata sadata da gurin Madam domin ba wai gudun Gwoggo kawai take tsoro ba har da irin hukuncin da zata ɗauka akan Ummanta a yadda take ji da ka taɓa Ummanta gara ita ka mata ko mene ne. Taci sa’a baya gurin cike da ƙwarin guiwa ta ƙarasa. Madam na ganinta ta kamota da sauri tare da turata wani ƙaramin ɗaki. “Tataah kin san abin da kika yi, kin san wane ne wannan mutumin a ƙasar nan?” Tuni hawaye ya fara ambaliya a fuskar Tataah. Madam ta dubeta cike da tausayawa ta ce”Ya tafi amma ya ce ba zai barki ba sai ya hukuntaki, wallahi Tataah ina jin tausayinki a zuciyata a shawarce ki ajiye aikin nan” A hankali ta ɗago “Allah yasa haka shine mafi alkhairi, da mutumcina ya zube gara na bar aikin” Kularta ta ɗauko Madam ta zuba mata abinci kamar na kullum sannan ta biyata kuɗinta har da ƙari tare da mata fatan alkhairi, jakarta da babban hijabinta ta ɗauko sukayi sallama, tana tafe tana hawaye da tunanin makomar rayuwarta a gaba, shin ya gobenta zai kasance? Ta bar aikin da take samu suke ɗancin abinci a wani sau ɗaya ita da Ummanta yanzu ta bar aikin ya zasu kasance? Ga babban tashin hankalinta Gwoggo wanne irin mataki zata ɗauka idan taji ta bar aikin? Da wannan tunanin ta tare ɗan napep yau ko tayin bata da zarrar yi saboda hankalinta ba a kwance yake ba.
Ko da ta sauka ta biyashi tafi minti biyar tsaye ƙofar gidan kafin ta shiga jiki sanyaye. Ba kowa tsakar gidan hakanne yasa cikin sauri ta shiga ɗakin Ummanta, tana nan kwance kamar yadda ta barta da sauri ta ƙarasa tare da jinginar da ita jikin bango dan tasan ta gaji da kwancin “Sannu Umma!” Ta furta hawaye na zubo mata, ƙura mata idon da tayi ne ta gane tambayarta take yi me ya faru? Kukan da take dannewa ne yaƙi dannuwa ta fashe da shi amma a hankali domin bata san Gwoggo ta gane ta dawo gidan. Nan take ta fara ba Umma labarin abin da yw faru domin Ummar na jin komi amsawa ne kawai bata iyawa, sai gani tayi Umman na hawaye da sauri ta fara share mata “Umma bana so kina kuka, wannan yana ɗaya daga cikin tarin jarabawata kar ki damu” Sai ita ta dena hawayen domin Umma ma ta bari, hakan yasa ta jawo kular tare da buɗe abincin tasa cokali tare da kaiwa bakin Umma amma sai taƙi buɗe bakin daman daƙar take buɗesa kaɗan-kaɗan take ci, ganin hakan yasa Tataah cewa”Dan Allah karki sa wannan damuwar a ranki komi zai zo cikin sauƙi” Da ƙyar ta samu Umman taci sai ta rufe musu sauran da dare ta ɗauko na ledar da ta zuba da Farhan ya bata taci. A ɗaki tayi akwalar sallar azahar tayiwa Umma sukayi tare basu daɗe da idarwa ba aka kira la”asar duk suka gabatar.
Kwanciya tayi domin wani zazzafi ne ke damunta duk da yamma ce kasa ƙin kwanciyar tayi, baccin wahala yayi gaba da ita Umma nata kallonta har ta farka wajen shidda na yamma. Miƙa tayi tare da hamma fitsari take ji sosai hakan yasa ta ciro kuɗin da Madam ta bata ta ciro ta irga daidai wanda take bata kullum sauran ta ɓoye domin kuɗi sosai ta bata. Fita tayi ba kowa kamar ɗazun daman Gwoggo ko yaranta basu fiya zaman tsakar gidan ba, sun fi son rayuwar jin daɗi a rayuwarsu. Hakan yasa buta ta ɗauka tare da shiga banɗaki ta rage mararta, tana fitowa Ruhaima na shugowa cikin wata banzar shiga da bata dace da ita ba a matsayinta na musulma tana wani taunar cingam ji kake “Ƙas! Ƙass!! Ƙasss!!!” Tana gaba Tataah na bin ta a baya har suka shiga madaidaicin parlourn na Gwoggo. Ruhaima ta saki ɗan mayafinta wanda dashi gara babu a saman matsagaitan kujerun parlourn tana furta “Wash! Yau na gaji” “Sannu Ruhaima bari in kawo miki ruwa da abinci kici ki kwanta ki huta” Shugowar Tataah ne yasa Gwoggo ɗaure fuska tana bin ta da wani mugun kallo, da sauri ta zube “Sannu da gida Gwoggo!” Hannu ta miƙa mata “Ba sannu na tambayeki ba danƙa min” A sanyaye ta miƙa mata kuɗin, irgawa tayi daidai na kullum tare da cewa “Tashi ki fitar mini a parlour” Ruhaima ta ce”Gwaggo ki basu abinci na yau dan Allah” Da sauri ta juyo da cewa “Karki haɗani da Allah Baby bazan iya basu ba” “Tashi ki fita!” Ta daka mata tsawa, da sauri ta miƙe ta fita. Jiri take gani sosai tasan ciwon goshinta ne ya sakar mata da zazzaɓi ga gudun da tasha ɗazu, tana shiga ɗaki kuɗi ta cira tare da fita, tana tafe tana layi, gashi duk inda ta duba bata sami chemis ba, hankalinta ya tashi sosai ta nufo hanyar gida. Titi ta hau ba tare da ta sani ba, tun daga nesa yake danna mata hurn amma bata sani ba saboda yadda taji zazzaɓin ya fara hawar mata kai tafiyar kawai take ba tare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta ba. Daidai ƙarasowar motar daidai zubewarta a gurin a sume, a furgice ya fito daga motar duk da yaga ba wai bugeta yayi ba amma yanayin da ya ganta da alamar tana neman temako shi kuwa Faruuk Allah yasa masa zuciyar tausayi ga fara’a dawowarsa daga wajen aiki kenan yau yayi yamma sakamakon wani aiki da yayi.
Birkito da ita yayi nan take idanuwansa ya sauka akan fuskarta ‘Tataah!’ Ya ambaci sunan da ta faɗa musu ranar shi da Ma’aruf. Da sauri ya kinkimeta sai cikin mota inda ya tada ya nufi wani private hospital dake kusa da gurin, yana zuwa ƙara surarta yayi cikin asibitin nan take aka fara bata temakon gaggawa. Faruuk sai safa da marwa yake a harabar gurin ya kasa zama ji yake tamkar ƙanwarsa Nanaah da suke ciki ɗaya ce babu lafiya, kusan awa guda kafin Likitan ya fito da sauri ya nufe shi, tun kafin yayi magana Doctor ya ce”Kwantar da hankalinka ta farfaɗo, zazzaɓi ne me zafi na maleria sannan ciwon goshinta ma ya ƙara assasa mata zazzaɓin sannan tana da ulcer” Numfashi ya sauke a hankali tare da furta “Na gode Doctor zan iya ganinta?” “I Zaka iya amma ta samu bacci saboda mun mata allurar bacci tana buƙatar hutu sosai” Gyaɗa kai yayi tare da nufar ɗakin da aka kwantar da ita, tun da ya shugo idanuwansa ke kan fuskarta da tayi fayau sai ciwon goshinta da aka wanke mata shi ga allurar ƙarin ruwa liƙe a hannunta. Kujera ya jawo ta zaman masu jinya ya zauna har lokacin idanuwansa na kanta, kusan minti ashirin yana zaune gurin kafin ya miƙe da sauri jin wayarsa na ringing Mami ce ya ɗauka da sauri “Faruuk lafiya har yanzu baka shugo gida ba?” Yana ɗauka yaji muryar Mami na tambayarsa. Numfashi ya fesar ya kalli gadon da Tataah ke kwance “Lafiya ƙalau Mami wata yarinya na kaɗe da mota shine na kawota asibiti yanzu haka ina can” Kawai ya tsinci bakinsa da furta wannan kalmar. “Asibiti ya jikin yarinyar?” Mami ta tambaya a kiɗime “Ki kwantar da hankalinki ba wani ciwo taji me yawa ba yanzu haka an sa mata ƙarin ruwa ta samu bacci” “To Allah ya ƙyauta gaba, wanne asibiti ne?” Sunan asibitin ya faɗa mata tare da yanke kiran. Kusan minti talatin sai ga Mami tare da Nanaah sunzo hannunta riƙe da kwando da kulolin abinci. Kasancewar asibitin bai da wani girma sosai yasa tana shugowa basu sha wahalar gane ɗakin da suke ba. Bakin gadon ta ƙarasa bayan Faruuk ya amshi kwandon hannunta yana mata sannu, gabanta ya buga da ƙarfi ta ƙure Tataah da kallo kafin taja numfashi “Allah ya bata lafiya” Suka amsa da amin ya ce”Mami bare naje nayi sallah banyi magrib ba” Ta ce”Sai ka dawo” Fita yayi ya bar Mami da Nanaah ya nufi masallacin dake asibitin…

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

*MU GANI A ƘASA…* _Hot Love_©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN_GAWURTATTU BIYAR._🔥https://arewabooks.com/u/ummuaffan Follow me fans.😍*Page 7-8*”Umma! Umma!!” Tataah ta furta da ƙarfi tare da ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Mami ta ƙarasa tare da riƙeta ganin tana niyyar cire ƙarin ruwan da ake mata, “Ki natsu kina asibiti ne!” Komawa tayi ta kwanta tana sauke numfashi tare da kafe Mami da bata san ko wacece ba da ido. Tea Mami ta fara ƙoƙarin haɗa mata kafin ta tasota zaune ta ce”Sannu ga tea bari na baki” Ƙasa tayi da kai bata ce komi ba, Nanaah ta kawo ruwa aka ɗauraye mata baki kafin Mami ta fara bata tea ɗin daidai shugowar Faruuk. Ƙure shi da kallo Tataah tayi a ƙoƙarin gano inda ta taɓa ganin fuskar, can ta tuno da shine ya taɓa taimakonta ana ruwa ranar. Sosai tasha tea ɗin saboda yunwar da take ji kawai ta isa ta sa mata ciwo, farfesun kaza Mami ta zuba mata ai kuwa ta lashe tas! Ganin irin kallon da Faruuk ke mata yasata jin kunya sosai tayi ƙasa da kanta. Ummanta ta tuna da sauri ta ɗago “Ina so na koma gida” Kafin Faruuk ya ce wani abu Mami ta maganantu “Baki lafiya fa, ki bada addres sai Faruuk ya faɗo musu kina asibiti” Da sauri ta fara girgiza kai idanuwanta suka cika tab da hawaye ta ce”A’a ba sai yaje ba, dan Allah a sallame ni na wuce wallahi naji sauƙi” Suna maganar likita ya shugo “Ah me jinyata taji sauƙi irin wannan zance” Ya faɗa da alamar yana da barkwanci. Tataah ta ce”I Na warke dan Allah likita ka sallame ni gida zani” “Ai ƙya bari zuwa gobe ko? Bai kamata a sallame ki yanzu ba” Cewar likitan. Mami ta ce”Nima abin da nake faɗa mata kenan!” “Wayyo Allah! Ummata” Ta furta hawaye na zuba “Umma!” Faruuk da bai san kalmar ta fito ba sai jin sautin ya yi “I Umma, dan Allah ka mayar dani gurin Ummata” Ta faɗa tana hawaye domin bata jin zata iya kwana wani guri ba tare da Ummanta ba. “Likita kawai ka sallamemu, ka haɗa mana duk maganin da kasan ya dace” Faruuk ya faɗa idanuwansa na kan Tataah wacce tayi saurin ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Likitqn kwance mata robar ƙarin ruwan yayi saboda tuni daman ta ƙare amma cire allurar, bayan fitarsa Mami ta ce Nanaah ta gyara musu kayan basket ɗin. Minti goma bayan fitar likitan Faruuk yabi bayanshi kuɗi ya biyashi na komi ya bashi magungunan sannan ya koma ya ce su fito su wuce. Gida ya fara kai su Mami ta tun da kallonsa da mamaki shi ɗinma kasa ce mata komi ya yi bayan isarsa bakin gate ɗin, ganin ba zai ce komi ba ta ce”Ai sanake gidansu yarinyar nan zamu fara zuwa muba iyayenta haƙuri ko?” Sosai yake jin kunyar Mami a bisa ƙaryar da ya mata cewa bige Tataah yayi amma ya daure tare da cewa “Ku shiga gida naga dare yayi ne Mami bari ni naje kawai” Ko da yayi maganar ya kasa ɗago kai ya dubeta, ba musu ta cewa Nanaah ta sauka suje, kallon Tataah Mami tayi tare da dafa kafaɗarta “Ƴata Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri da abin da ya faru sannan ki gai da mini Ummanki” Gyaɗa kai kawai tayi kanta a ƙasa, bayan fitarsu yaja motar ya doshi unguwarsu Tataah. Tun da ya hau titi bai ce mata komi ba ita ma kanta na ƙasa burinta kawai sanin halin da Ummanta take, Faruuk bai mance layin ba domin daidai ƙofar gidansu ya tsaya, sai lokacin ya juyo ya kalleta. A sanyaye ta ce”Na gode Yaya Faruuk Allah yasaka da alkhairi” Daga haka ta fara kiciniyar buɗe motar, magungunanta ya ɗauko tare da miƙa mata “Ga magungunanki ki daure kina sha kamar yadda likita ya rubuta miki zaki gani sannan ki dinga cin abinci akan lokaci” Da sauri ta ɗago suna haɗa ido ta mayar da kai ƙasa tare da amsa “Na gode” Ta fita cikin natsuwa, sai da yaga shigarta kafin ya sauke numfashi ya tada motarsa zuwa gida. Dare ne dan kusan tara da rabi hakan yasa ba kowa tsakar gidan ko da yake ko da rana ba cika zama sukayi ba, direct ta nufi ɗakinsu, hannu ta sa ta kunna gulop ɗin ɗakin da a kashe ta iske shi kuma akwai nepa. Tar! Idanuwanta ya faɗa ana Umma don ba bacci take ba, da sauri ta ƙarasa tare da ajiye ledar maganin ta nufi Umma “Kiyi haƙuri Umma wallahi ina can ina tunaninki” Ɗagota tayi tare da ɗibar ruwa ta bata sosai tasha ruwan, hawaye taji ya zubo mata ina da ta kwana ƙila da sai dai ta dawo ta taradda gawarta. Abincin ɗazun ta ɗauko tare da bata, ƙin amsa tayi tana ƙifta ido, ta gane abin da take nufi tana tambayarta inda taje ne “Umma na fita sayen magani kaina na ciwo ban samo ba, na faɗi a hanya wani ne ya temaka mini” Ta sanar da ita komi tare da jawo ledar maganin, kuɗi ta gani a ciki bandir guda gabanta ya faɗi ta ciro kuɗin tana juyawa tana zazzaro ido, Umma ma kallonta take ta ce”Shine ya saka min cikin maganin wallahi ko sanar dani baiyi ba” Ciro magungunan tayi tare da mayar da kuɗin leda ta ƙulle zuwa tayi ta ɓoye dan tafi tunanin ko bai sani ba kuɗin shiga shiga dan shi magani ne kawai ya ce ta amsa hakan yasa ta ɓoye da ƙudirin duk ranar da suka kuma gamuwa zata mayar masa da kuɗinsa.Abinci ta ɗauko taba Umma sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan ta ajiye ɗan ragowar dan ita kam a ƙoshe take, magungunanta tasha tare da gyarawa Ummanta kwanciya ita ma ta kwanta a ranta tana mai ƙara jin tausayin Umman nata wacce daga ƙwanciya sai zama shima zaman sai an jinginata da bango. Tunani ta faɗa akan temakon da Faruuk ya mata Maminsa da ƙanwarsa ta tuno abin su gwanin ban sha’awa sai ta tsinci kanta da sakin murmushi. Da haka barci ya kwasheta.. Aliyu pov.Cike da ɗacin zuciya yake tuƙin bayan barin shi gurin, yaja tsaki kam yafi cikin masaki “Mummuna me baƙar fuska!” Ya faɗa tare da fesar da wani huci me zafi, shi dai yarinyar bata mishi ba bai san dalili ba, ranar ya ganta a gidan abinci yau kuma a titi tana gudu anya ma kanta ɗaya? Ya tambayi zuciyarsa kafin ya ɗaga kafaɗa alamar bai dameshi ba. Yarinya ƙarama sai shegen gantalin tsiya daman matsalar ƴan ƙauye su shugo gari kenan. Da wannan tunanin ya ƙarasa gida, bayan ya shiga yayi parking kai tsaye part ɗin Ammi ya wuce. Sareenah zaune a parlour taci kwalliya kamar wacce zata gidan biki “Sannu da zuwa Yay…” Katseta yayi ta hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce”Ina Ammi?” Fuskarsa sam ba alamun wasa. Muryarta har rawa take wajen furta “Tana sama” Domin Aliyu va dai kwarjini ba. Cikin takunsa na isa ya fara taka saman ta bishi da kallo cike da so da sha’awa namiji har namiji irin mijin da take mafarkin samu, a fili ta furta “Wallahi tun da ina sonka duk yadda zanyi sai nayi ka zama mallaki, bari ka zama nawa sai ka gane kurenka” Zama tayi tare da ci gaba da kallon da take gefe guda kuma tana chart a waya. A hankaki ya tura ƙofar bedroom ɗin Ammi bakinsa ɗauke da sallama, zaune take bakin bed tana waya, saman kujerar dake ɗakin ya zauna jin da Daddy take wayar “Allah ya dawo da kai lafiya” Ta faɗa tana katse kiran, kafin ta ɗago ta kalle shi “Abuturrab” Ƙyawawan idanuwansa ya ɗago tare da sauke mata su. Ƙwarjininsa yasa abin da tayi niyyar faɗa masa ya kasa fitowa “Ammi kin kirani lokacin ina masallaci ne” Ya faɗa cikin sanyin murya. Ta ce”Abin da kake baka ƙyautawa Amma tun da jibi Daddynku zai dawo ai ya gani da idanuwansa” Ƙara zuba mata ido yayi ta gane nufinshi ƙarin bayani yake so yafi ƙarfin ya mata maganar ne, ƙarin tsaki taja tare da faɗin “Yau baka kwana gidan nan ba, ina ka kwana?” Kasa dena kallonta yayi yana mamakin Ammi yo shi ƙaramin yaro ne da za a masa wannan tambayar ko bai kwana gidan ba balle ya kwana. Ya ce”Gida na kwana” Wani kallo ta masa na ka rainani kafin ta ce”Ƙarya kake Abuturrab jiya nice parlour har wajen biyu na dare amma banji shugowarka ba” Bata san sanar dashi parlourn ta kwana saboda taji dawowarsa domin kar ya zargi wani abu. Ɗan smile ya saki dan da wuya kaga yana dariya yafi murmushi, “Na dawo, da yake Faruuk ne ya sauke ni a waje na shugo” Ƙura masa ido tayi kafin ta taɓe baki. Bai ƙara cewa komi ba, ganin shurun yayi yawa ne ta ce”Kayi mini zugun dan Allah tashi ka fita idan baka da maganar yi min” Da mugun mamaki yake dubanta sai kace ba ita ce tayi kiransa ba, to daman me zai ce yana jiran ji daga gareta akan kiran da take ta masa. Miƙewa yayi ba tare da ya ce komi ba ya doshi hanyar fita “Kaji Alhaji zai dawo jibi?” Ta wurga masa tambayar yana gab da fita “A‘a!” Ya amsa mata tare da ficewa. Cije leɓe tayi wani abu na taso mata a zuciya, ta fesar da huci me zafi tana gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa.Da sauri Sareenah ta miƙe ganin fitowarsa, kai tsaye ƙofa ya nufa “Am Yaya Ali….” Kallon da ya mata ne yasata kasa iya ƙarasa abin da zata faɗa fuww! Ya fita daga parlourn, jagab ta zauna zuciyarta na mata zafi kamar wuta. Wayarta da ta fara ringing alamar ana kiranta ta duba ganin ƙawarta Layla ce yasa tayi saurin ɗauka”Layla kina ina ne?” “Gani a hanyar gidanku” Layla ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta saki tare da furta “Sai kin ƙaraso” Ta ajiye wayar direct bedroom ɗinta ta wuce ta huci, kusan minti goma Layla ta ƙara so, “Reenah lafiya kike ta faman kai kawo?” Kasancewar ƙawayenta Reenah suke kiranta, zaunawa tayi bikin bed bayan ta dubi Layla ta ce”Hmmm! Ke dai bari, wallahi yadda Aliyu ke wulaƙanta ni abin na damuna” Ƙarasawa Layla tayi tare da zama kusa da ƙawar tata ta dafata da faɗin “Wai kina nufin har yanzu Aliyu bai shugo hannunki ko bakiyi aikin da aka saki bane?””Wallahi nayi sai dai my Aliy yana da wata kafaffiyar zuciya gani nake kamar magani baya cin sa” “Ƙarya ne!” Layla ta katse Sareenah ta ɗaura da cewa”Tun da asiri yaci Annabin Allah uban waye zai ce yafi karfin asiri? Tun da na wannan Malamin bai yi ba ki haɗa kuɗi akwai wani sai mu sake zuwa” Numfashi ta sauke “Ni wallahi har na fara gajiya da kashe kuɗi ba biyan buƙata” “Idan kin dena son sa shi kenan amma ai dole sai da kashe kuɗi idan ba a ci nasara a wannan ba ai a gaba idan da haƙuri juriya da jajircewa za a samu” “Haka ne kuma” Sareenah ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa “Tun da kikazo sai zuba muke bari in kawo miki ruwa” Tana faɗa ta fice.Washe gari Tataah bata tashi da wuri ba, tun bayan sallar asuba da tayi ta koma, sanin cewa ba zata fita wajen aiki ba, kuma daman ba lafiya gareta ba ƙarfin hali ne kurum. Kwance take wajen misalin ƙarfe tara na safe, sai juyi take tana tunanin yadda zata iya wuni a gidan tare da Gwoggo da kuma tunanin abin da zata ce idan ta tambayeta dalilin barinta aiki, tasan wuya kam sai tasha, amma wuya bata kisa, cikin mutuwar jiki ta nufi hanyar kitchen bayan fitowarta daga ɗakin, har lokacin su Gwoggin basu tashi ba, hakanne yasa ta fara aiyukanta cikin kwanciyar hankali. Ta kusan idawa Ruhaima ta shugo, kallon sama da ƙasa tayiwa Tataah kafin ta kau da ka tare jawo ƙaramar tukunya ta kunna ƙarimin rishonsu ta ɗaura, Tataah na gurin tana aiki har ta gama tafa indomie ɗinta biyu da ƙwai biyu, ta zuba a plate tare da barin wata a ciki ta miƙawa Tataah, kallonta tayi sannan tabi rahowar Indomie ɗin da kallo, gyaɗa mata kai Ruhaima tayi alamar ta amsa, hannu tasa ta ƙarɓa tare da furta “Na gode.” A hankali. Juye indomie tayi cikin ƙaramin plate ta ida komi da sauri ta shige ɗaki Ummanta ta ɗaya tare da bata taci kuwa sosai ɗan murmushi tayi da cewa”Umma kina san infomie naga kinci” Lumshe ido kawai tayi tana bin Tataah da kallo wacce taci ragowar indomie ɗin. Wuni tayi a ɗaki alwala kawai ke fitar da ita, haka Tataah ta ɗauki tsawon kwana uku tana huda ba tare da Gwoggo ta sani ba. Kwatsam yau ta fita alwalar sallar azahar Gwoggon ta fito sukayi kiciɓis, bin ta da kollo tayi a wulaƙance kafin ta ce”Ballaga gantalalliya yau kuma zaman me kike a gida” Gaban Tataah na faɗuwa ganinta bata yi tsammani ba, ƙasa tayi da kai kafin ta ce”Uhm…Uhmm…da…ma….daman ai…!” Duk cikin inda-inda take ta kasa ma furta abin da ya kamata duk ta ruɗe. Baba ne shima ya fito binsu yayi da kallo Gwoggo ta dube shi “Baban Sudees kana ganin gantalalliyar nan yau bata fita ba ko? Wallahi kuwa zata ga yadda ake gantalewa a gidan” Kafe Gwoggo yayi ta kallo wata tsawa tadaka mishi “Kallona na kiraka kayi ne Malam? Wallahi yau idan banji hujja me girma ba akan ƙin zuwanki aiki, sai na lahira ya fiki jin daɗi, da ni kike zancen!” “Kiyi haƙuri bana lafiya ne, shine Madam ta ce na dawo gida sai gobe naje!” Tataah ta tsinci bakinta da furta hakan domin mafita take nema…..*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*1, *MU GANI A ƘASA..🔥* _Ummu Affan_2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚* _Ummu Maher_3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨* _Miss Hajo_Guda ɗaya N300Guda biyu N500Guda uku N600Guda huɗu N700Guda biyar 1k*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*Fatima Rabiu Sunusi0037219728StanbicIBTC Bank.Shaidar biya tanan 👇0810 433 5144Masu tura katin MTN👇0814 179 9224………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇Guda biyar 1000fGuda huɗu 700fGuda uku 600fGuda biyu 500fGuda ɗaya 300fKai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp +227 84 50 64 76*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻__*infection*__Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

https://arewabooks.com/u/ummuaffan

Page 9-10

Wani kukan kura da Gwoggo tayi sai gata ta shaƙe wuyan Tataah. Ƙarar azaba Tataah ta saki daidai ƙarasowar Baba yana ƙoƙarin ƙwatarta “Dan Allah Zainabu ki rabu da yarinyar nan” Wata bangaza ta tayiwa Baba sai gashi a gefe, ya yin da tacigaba da kaiwa Tataah duka ta ko ina, “Kiyi haƙuri Gwoggo!” Abin da Tataah ta iya furtawa kenan cikin tsananin wahala, dama gashi ba ta lafiya ga ƙarin dukan Gwoggo. Bata ƙyaleta ba sai da ta mata ligib kafin ta ce”Mu zuba ni dake, shege ka fasa ɗan halak kuma sai yanka, dan ubanki yanzu wake da isasshiyar lafiya wallahi duk wanda kikawa sannu zai amsa da kowa takanshi yake sai dai ta wani tafi ta wani amma kowa ba lafiyar nan gare shi ba. Har ni zaki faɗawa baki da lafiya shi ya sa kika ƙi fita aiki saboda ke ga isasshiya to nima bana lafiyar ubanki ma ba lafiyar gare shi ba kuma haka yake fita nima in fita ai daurewa kowa keyi dan yanzu a ƙasar nan dai kowa bashi da lafiya.” Sosai Tataah ke kuka kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa sai zubar hawaye da take, hakan kuwa ya ƙara ƙufular da Gwoggo ta kai mata wani mari wanda tsabar zafinsa yasa mata sakin fitsari bata san lokacin da ya fito ba. Duƙewa tayi a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tafin hannunta ɗaure akan kuncinta da ƙarfi kuwa ta runtse idanuwanta sakamakon wasu fararen taurari da ta gani “Shegiya me baƙar fuska da baƙin hali, wallahi gobe idan kika kuma zama baki fita aiki ba sai na illataki, wallahi sai na miki abin da ya taka wannan algunguma ƴar kaza-kazan uban can.” Kan Baba ta nufa tana huci “Kai kuma munafiki zamu haɗu da kai, wai har ina mata hukunci kazo wai zaka tare ta?” Ummm tayi wani murmushin takaici kana ta ce”Kai game ƴa! Ƴar ma da kake ƙila wa ƙala akanta” Da sauri ya ɗago ido yana kallonta tare da girgiza mata kai bai iya cewa komi ba, dan mugun tsoranta yake ji. Fuuu! Ta wuce ciki tana huci kamar kumurci. A sanyaye ya dubi ƴar tashi “Komi yayi farko yana da ƙarshe da izinin Allah!” Abin da ya furta kenan yabi bayan Gwoggo. Wani kuka Tataah ta saki, sai da tayi mai isarta kafin ta wuce ciki, tana shiga Umma ta kura mata ido, saddar da kanta ƙasa tayi sam bata so Umma ta gane tana cikin wani hali dan kar ta sawa Umma damuwa a rai, gashi ba lafiya gareta ba… A yau Daddy ya dawo sosai Ammi tasa aka gyara ko ina ga abinci kala-kala da ake ta shiryawa na tarbarsa.. Abuturrab tun safe yana part ɗinsa yana bacci, wajajen ƙarfe sha ɗaya yaji wayarshi na ringing kamar ba zai ɗauka ba sai ya jawo wayar ganin Faruuk ne ya ɗanyi murmushi tare da amsa kiran “Anaci kenan lafiya zaka kirani da sanyin safiyar nan?” Girgiza kai Faruuk yayi daga ɓangaranshi kafin ya ce”Dalla Malam fito ina bakin gate” Gyara kwanciya Abuturrab yayi tare da cewa”Bacci nake kuma bana san takura please!” Ƙit ya katse kiran yana jan tsaki tare da ajiye wayar ya gyara kwanciyarshi yana sake naɗewa cikin bargo. Gabaɗaya yaci an yaye bargon da fushi ya juyo idanuwansa suka sauka a fuskar Faruuk “Lafiya Malam!” Ya tambaya a fusace fuskarshi ɗaure. Faruuk gyara tsayuwarsa ya yi tare da rungume hannayensa a ƙirji ya ce, “Tambaya kake ko neman sani? Abey Malam tashi muje, mutum ya duƙa bacci kamar wata mace saboda lalaci” Saurin yaye bargon da ya rufa ya yi ya tashi da sauri ya duro gadon yana jan tsuka “Mtsuw! Kai kasan kallo ɗaya aka mini an san jarumi ne ni” Yana faɗa direct ya yi toilet. Zaunawa Faruuk yayi gefen gadon yana dariya, daman yasan za a rina Aliyu bai san a kirashi rago ko kalmar dake kace-ceniya da hakan. Kusan mintina sha biyar Abuturrab ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ɗayan kuma yana goge sumar kansa, gaban mirror ya ƙarasa ya shafe jikinsa da lotion tare da buɗe durowa ya ɗauko doguwar riga ta jallabiya me matuƙar ƙyau da tsada. Taje sumar kansa yayi yana kallon Faruuk wanda shima idanuwansa yana kanshi “Haufa Guy!” Faruuk ya furta yana miƙewa, ɗan tsaki yaja yayi gaba yana furta “Ko kuturu ne kai akan naci haka ka barni haka” Faruuk na biye dashi har suka isa parlour, guri suka samu tare da zaunawa saman sofa. Faruuk ya ce”Kana ɓata mana lokaci fa Ma’aruf ya ce idan mun fito a kirasa ba zai iya zuwa zaman jira ba” Ya ƙarashe maganar da tsokana, kau da fuska Abuturrab yayi ba tare da ya ce komi ba. Ganin haka yasa Faruuk saurin tashi daga inda yake ya dawo kusa da Abuturrab cikin taushin murya ya ce”Please Aliyu idan zaka ka taso, idan kuma mu wuce ne shi kenan” Ɓata fuska yayi kafin ya ce”Da wucewar ku kayi da yanzu kunyi abin da ya dace, Faruuk kasan halina bazan iya zuwa gurin kuchakan yaran nan ba har na iya abin da kake tunani” A fusace ya miƙe cike da jin ɗacin kalmar da ya kira “Matar da zan aura ne kuchakar? Na gode Aliyu!” Faruuk ya fita da sauri. Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shin nan. Faruuk na fita Ma’aruf ya kira suka wuce duk abin da ya dace sai da sukayi sannan kowa ya wuce gida, tun da bikin ya ƙarato hankalin Faruuk duk ya koma can yana san zuwa duba cikin Tataah amma hidimar bikin kanshi sosai ya ɗauki zafi da komi kusan shi yake yi sai Ma’aruf dake temaka mashi amma sam Aliyu ya zare hannunsa kami da sha’anin auren. Faruuk ko ta kanshi ba yabi, har zuwa yau juma’a da ta kama bikin, shagali sosai ake babu masaka tsinke a gidansu Faruuk duk kuwa da girmansa, don shi ɗin ɗan dangi ne sosai. Ko yau da ake ɗaura auren Faruuk bai bi takan Aliyu ba harkar gabanshi kawai yake don yaji zafin kalmar da ya yaɓawa matar da zai aura Hibbah ta kuchaka shikam a haka yake ƙaunar abarsa. Baiyi tunanin ma zai zo ɗaurin auren ba abin mamaki sai gashi cikin wata ɗanyar shadda tamkar shine angon. Duk inda ya yi kallonsa ake tamkar wani tauraro, saboda ƙyawon da yayi cikin wata ɗanyar shadda marun tamkar shine angon har da malin-malin, masallacin sosai ya cika da al’ummar Annabi, bayan idar da sallar juma’a ne aka ɗaura auren Umar Faruuk Hassan da amaryarsa Muhibbat Kabir akan sadaki dubu ɗari biyar. Ana cikin ɗaurin auren kafin a tashi akaji muryar wani mutum na furta “Assalamu alaikum jama’a ga duk wanda ke buƙatar auren ƴata Jameelah ni mahaifinta zan bashi aurenta akan sadaki ƙalilan kai idan ma baka da kuɗin a yanzu? To zan baka aurenta a sadaka!” Gabaɗaya gurin ya ɗauki shuru baka jin motsin mutane ballantana kuma maganarsu, jin kowa yayi shuru ne wasu hawaye masu zafi suka sakko akan fuskar mutumin. Idanuwan sa ne suka faɗa akan fuskar Abuturrab shima kallonsa yake cike da mamakin uba irinsa. Gani yayi mutumin ya ƙaraso gabansa tare da ɗago shi, wani ikon Allah sai yaji ya miki mutumin ya buɗe baki da ƙarfi ya ce”AlhamduLillah wannan bawan Allah ya amince zai auri ƴata Jameelah!” Gaban Aliyu ya wani bada sauti me ƙara kamar yadda Faruuk da Ma’aruf suke dubanshi cike da mamaki, a tunaninsu shi ɗinne ya furta haka dan basa tunanin mutumin haka kawai zai ce ya amince, gaban limamin mutumin ya kai Aliyu wanda ya koma tamkar mutum mutumi yana duban uban wannan ƴa tamkar me taɓin hankali. Sai lokacin masallacin ya kachame da surutu na irin yadda Aliyu yayi shahadar wannan aure, su kansu limaman cike da mamaki suke, nan dai aka sa kowa yayi shuru kafin me ɗaura auren ya ce”Kana da sadaki a hannunka?” Mahaifin Faruuk ne wanda yaji tamkar an ɗaure mishi baki sai lokacinne ya iya cewa akwai kuɗi amma basu fi dubu ɗari biyu ba, Mutumi mahaifin ƴa ya ce dubu hamcin sun isa sadakin ƴarsa, haka Faruuk ya amsa gurin mahaifinsa aka bada inda nan take kuwa aka ɗaura auren Aliyu Muhammad Aliyu A.M.A da JAMEELAH Mahmud Abdullahi akan sadaki dubu hamsim. Abuturrab kallon mutane kawai yake tamkar wanda akawa asiri ko aka rufewa baki, ƙala ya kasa cewa har aka ɗaura auren inda mahaifin Faruuk ne ya wakilce shi. Faruuk ne ke masa wani kallo cike da al’ajabi “Angon Jameelah!” Yaji bakinsa ya furta daidai lokacin da Aliyu ya ƙaroso kusa da shi “Jameelah!” Ya furta ƙirjinsa na mugun bugawa da sauri da sauri, Mutumin nan kuwa na liƙe da Aliyu duk inda yaga yayi sai ya bisa, bayan angama komi aka fara watsewa mutumin nan ne ya kira Aliyu gefe, wata magana ya faɗa mashi da ni kaina ban jiyo ba sai wata ƙatuwar takarda wacce ko mene ne a ciki? Oho! Da ganan kuma sai ya nemi mutumin ya rasa, haka suka koma gida cike da al’ajabi. Anci gaba da gudanar da bikin Faruuk cikin farinciki ba wanda yasan da auren Aliyu sai wanda yaje gurin. Shi kuwa Aliyu tun da ya dawo gida bai kuma bi takan zancan ba, don duk a tunaninsa mafarki ne yayi ko kuma hasashe hakan yasa sam sai yaji ya manta da batun. Ƙatuwar takardar nan kuwa tun da ya buɗe durowa ya ajiyeta ya manta da batun ta.
Washe garin kammala bikin Faruuk ne, Daddy ya dawo sosai aka mishi tarba ta kece raini Ammi kuwa an ɗauki wanka na alfarma an shirya mishi abinci da nasha kala-kala. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe jirginsu ya sauka a filin jirgi na birnin tarayya Abuja direba ne yaje ya ɗaukosa, lokacin Aliyu na ciki yana bacci kamar kasa, har mamakin yawan baccinsa Faruuk yake yanzu domin ada ba haka yake ba. Daddy sai da yayi wanka sannan yazo yaci abinci Ammi sai nan-nan take dashi haka Sareenah cike da girmamawa take komi. Wajajen sha biyu na rana Aliyu ya shugo part ɗin cikin ƙananun kaya, tun da ya shugo Sareenah ke bin shi da kallo har ya sami guri ya zauna kusa da Daddynsa “Abuturrab!” Daddy ya kira sunansa. A hankali ya ɗago kai fuskarsa ɗauke da ɗan murmuahi ya ce”Welcome Dad!” Shafa sumar kansa Daddy yayi ya ce”Thank you Son! Fatan na sameku lafiya?” “AlhamduLillah Dad” Gyaɗa kai Daddyn yayi ya ce”Wai ya batun gurin aikinka? Ko kuwa sallamarka sukayi kazo zaman gida tsawon sati biyu?” “No Dad na amshi hutu ne saboda ina san na huta kuma ga bikin Faruuk amma AlhamduLillah jiya angama komi” “Ma sha Allah” Cewar Daddy ya ɗaura da cewa”Ummaru yayi aure saura kai kuma” Wani irin sauti ƙirjinsa ya bada tunowa da jiya an ɗaurawa Faruuk haka an ɗaura mishi” Girgiza kai ya fara a ranshi yana cewa”Ba haka bane, mafarki nayi” Daddy ya ce”Me yafaru ne kake girgiza kai kamar wani kaɗangare” Chak! Ya tsaya da girgiza kan tare da tuno abin da mutumin nan ya ce da shi…

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

Comments

table of contents title