Main menu

Pages

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

Description of

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

You are about to download TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbalereleased on 2022 just proceed with your download by following the below instruction.

BOOK INTERNAL INFO

Godiya

Na fara wannan littafin na TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale da sunan Allah Mai rahama mai jinkan bayinsa wanda ya halicci sammai bakwai da kassai bakwai.

Arashi da Gargadi

WANNAN LITTAFIN K’AGAGGE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BANYI DOMIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE

BAN YARDA WANI KO WATA BA YAYI AMFANI DA WANI B’ANGARE NA RUBUTU NA BA,BA TARE DA IZINA NA BA, AYI HATTARA

Binta Umar Abbale

WANNAN LITTAFIN NA KUD’I NE, NAIRA D’ARI BIYU IN MUTUM NA BUK’ATA SAI YA BI WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA
08089965176
07084653262

Gaisuwa

KUNA RAINA, BINTA UMAR FAN’S HAK’IK’A BANI DA ABUNDA ZANCE DA KU SAI FATAN ALKAIRI

GAISUWAR KU DABAN TAKE, DOMIN BAKWA GAJIYA DA YI MIN COMMENT

UMMAHANI “YAR MUTAN BAUCI

NANA AISHATU ” YAR MUTAN KATSINAWA

PREETY “YAR MUTAN BARNO

ZAINAB ” YAR MUTAN KATSINAWA

MAMAN SUDAIS SAKWATTO

HAJIYA INDO AMADU

FAUZIYA MA’AWIYYA

RAHAMA ALIYU

MAHILLA UMAR

HAK’IKA BAZAN TAB’A MANCE KARAMCIN KU GAMI DA FATAN ALKAIRIN KU A GARE NI, NAGODE SOSAI DA ADDU’AR KU.

KUYI HAKURI WANDA BAN FAD’A BA KUMA KUNA RAINA SOSAI ANA MUGUN TARE🤝🏻

Gaisuwa Ta Musamman TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION


KUN CANCANCI YABO DA GODIYA A GARE NI

1 HUSAINI ATK 80k

2 ZAINAB ABDULLAHI,SHAXXI

3 NASMATU “YAR MUTAN ARKILLAH

Tsakuren TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

Fad’a sosai Hajiya Gaji takewa Rabi’a ta inda ta shiga ba tanan take futa ba,Rabi’a sai kuka take. Hajiya Tabawa tace”Ai ba ita kad’ai zaki wa fad’a ba harda Sumayya, kai dukkaninsu ma zaki had’asu domin su kiyayi gaba,ni kam wannan hukunci da Habibu ya yanke yayi min dai-dai wallahi,to amma ya cire maganar Sumayya a ciki, tunda bata kai shekarunsu ba,kuma bata dawo har yanzu”.

Hajiya Zulai tace”To in banda abun Habibu an tab’a aure babu miji,Sumayya ina taga saurayi ma,gwarasu suna dashi,rashin fuska ne yasa basu kawo shi ba,amma yanzu tunda sun nuna suna so ai shikkenan”

Rabi’a tayi da tasani yafi cikin kwando, kuka take Suwaiba na taya ta, ita kuwa Sumayya shiru tayi tabar kukan jin abunda Hajiya Zulai tace, bands ita a Wanda za’ayi wa aure tunda bata da saurayi.

Ranar gidan kwana sukayi zuciyoyinsu babu dad’i, domin Alhaji Madu ma, da yaji labarin abunda ya faru,yayi mamaki sosai kuma yayi fad’a ya kuma goyi bayan hukunci da Habibu ya yanke akansu Rabi’a dole su turo samarin nasu, su turo magabatansu domin a tsai da magana,amma ya cire Sumayya a ciki,a cewarsa yarinya ce, kamar yadda Hajiya Zulai tafad’a.

Da safe,sukuku suka tashi sukayi shirin makaranta kamar ko da yaushe Sumayya ta hau sama, gurin Babansu,suka gaisa,ta karb’o kud’in makaranta,nan Alhaji Madu yayi mata fad’a sosai,kuma ta d’auka domin ta tsorata da hukuncin da akai wa su Rabi’a,in akwai abunda ta tsana a duniya bai wuce ace za ai mata aure ba.

Tana k’okarin sauka k’asa , Habibu yana k’okarin hawa, tsayuwa tayi ya k’araso inda take,yana mata kallon sama da k’asa, fuskarsa a had’e, Da sauri tace” Yaya Habibu ina kwana”?

“Lafiya lau”
Yafad’a yana nazarinta, sunkuyar da kai tayi cike da tsoransa, yace” Wannan itace damar ki ta k’arshe,a gidanan, kiyi k’okari ki maida hankalin ki kan karatu,idan ba haka ba, zaki cuci kanki ,domin ko da miji ko babu miji aure za’ai miki domin shi kika nuna kina so, duk sanda kika kuskura, naga wani abu na, shashanci daga gare ki, to irin hukunci su Rabi’a zan yanke a kanki”

Muryarta na rawa tace”Insha Allahu na daina zan nutsu sosai kuma zan maida hankalina kan karatuna”

D’aga kafad’a yayi ya wuce yana fad’i “Wannan shine ya dace dake dama”

Sumayya ta sauka k’asa jikinta a sanyaye,duk wannan rawar kan babu shi,ta nutsu sosai, tare suka tafi makarantar, ko a ji ma,Sumayya shiru tayi babu hayaniya da surutu har k’awayenta sukaita janta tayi shiru kawai tana d’aukar darasi.

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale


Sati hud’u da faruwar Al’amarin, maganar auransu Rabi’a ta kankama, domin Habibu ya zauna da iyayen Ansar saurayin Rabi’a an tsaida magana, hakanan iyayen Saifudden saurayin Suwaiba suma sun a munce, an sanya rana shekara me zuwa,lokacin sunyi candy, tunda basu dad’e da shiga ss3 ba, haka rayuwa take,Wannan karon Habibu Cotonou suka tafi,domin cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin su.

Sumayya ta nutsu sosai,ta dage da karatu, a boko da isilamiyya,har da makarantar dare, yanzu isilamiyya an sata a layin”yan sauka,domin dama can tana gane karatu itace take maida kanta koma baya
Makarantar boko kuwa dama da aji d’aya,su Rabi’a suka wuce ta, ta k’ara girma yanzu, k’irjinta a cika ta zama babbar mace yanzu ta daina sanya k’ananun kaya, kullum cikin hijabi ko a gidane ma cikin hijabi take,sai zata kwanta bacci Hajiya Zulai take matsa mata ta cire.
Wannan sauyin da aka samu yasa Alhaji Madu yaji dad’i don haka ya kirata samansa, yayi mata albishir da cewar ta shirya ranar asabar zasu tafi saudiya domin suyi umara.

Da murnar ta ta sauko k’asa tana fad’a,aikuwa da gudu “yan matan gidan, suka nufi saman gurin Alhaji Madu, kowa naso aje dashi,nan yace” Subari in sun dawo zasuje dab da bukinsu Rabi’a,haka suka hak’ura domin sun san halin Babansu,in yafad’a magana.


cigaban tsakure TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

Watansu Habibu goma a Cotonou suka dawo gida, Khamis duk inda Habibu yaje k’afarsa,nan yake aje tasa,yak’i tafiya harkokinsa, shima, Habibu yana mamakin wannan lamari,amma da yake bashi da bin k’wak’wafi, kawai sai ya k’yaleshi, suka cigaba da sabgarsu.

Tunda ya dawo gida ya hautsine ana ta murna,gami da rabon tsaraba, bayan k’ura ta lafa, d’aya bayan d’aya suka dunga hawa Sunai masa sannu da zuwa, Sumayya ce a k’arshe, Habibu yayi mamakin sauyin da aka samu,ta fanni Sumayya,kallon ta ya dunga yi a fakaice,idan ba idonsa ne yake masa k’arya ba,sai yaga ta k’ara girma,da kwarjini, lafiya lau ya amsa mata gaisuwar ta, babu kyara babu hantara, Khamis kuwa duk ya susuce sai mutsu-mutsu yake kan kujera,yana janta da wasa,yak’i sakar masa fuska kamar da, Habibu yace”Je ki d’auko min jakunkunan makarantar ki, in duba”.’

Da k’warin jiki,Sumayya ta taje d’auko masa, ta makaranar boko ya fara dubawa, ya ga sauyi sosai, ya mayar da littatafan, ya fara duba ta isilamiyya, nan alhamdullahi, kallonta yayi,a nutse yace”Yanzu I zufinku nawa”?.

“Hamsin da biyu”
Tafad’a kanta,a k’asa.

Gyad’a kai yayi ya mayar da alk’uranin da sauran littatan addinin cikin jakar ya fara bud’e jakar makarantar dare, Khamis yace”Lallai Malama Sumayya an kusa sauka Ashe,gaskiya ranar zamu sha hidima”
Murmushi Sumayya tayi kawai ta sunkuyar da kanta k’asa.

Yana tsaka da duba littafin ishimawi,Wanda ya futo dashi daga jakar Sumayya,kawai wata takarda ninkakkiya ta fad’o k’asa.
Hannusa na rawa,ya d’auka ya bud’e ya fara karantawa kamar haka.

Assalamu alaikum.

Sumayya ma’abociyar kyau da kyawun zuciya,kyakykyawa, zinari mai d’auke,da sirika da ba ko wace mace,take dasu ba, Sumayya mai cikakkiyar sura,me cikkaken k’irji,me cikkaken mazaunai,wanda suke sakani sha’awarki, Sumayya kin cika mace,domin duk inda ake son mace kin kai,kin kawo,wallahi Sumayya ina son nonuwanki, ina zumud’in ranar da zanjisu a hannuna ina lailayasu, ranar nasan mutuwa kawai zanyi dan dad’i,Sumayya INA bala’in son inji zak’in miyau d’in bakinki, ina so ji gard’inki ma’aciyar kyawun sura, bazan tab’a daina sanki ba har k’arshen rayuwarta.

Daga masoyin ki.
me k’aunar ki har abada.

cigaban Tsakure

Wani gumi ne ya tsinkewa Habibu,cikin tashin hankali! ya d’ago kansa,ya zubawa Sumayya idonsa,jajur, gabanta ya fad’i ganin yadda duk ya burkice lokaci guda, k’asa tayi da kanta, jikinta yana b’ari,mik’a mata wasik’ar cikin bada umarni yace”Karanta min abunda yake cikin takardar nan” cikin rashin fahimta Sumayya ta karb’i takardar ta fara karantawa.

Wani gumi ne ya yanko mata lokacin da tagama karantawa,kuka tafashe dashi,tana gyad’a kai kamar d’an k’adangaruwa, bakinta sai motsi yake takasa cewa uffan.

Cikin wata irin tsawa yace”Wane d’an iska ne wannan”?

Shiru Sumayya tayi,tana kuka Habibu ya d’aga hannunsa ya kai mata duka a fusace! Zama tayi a gurin.ta d’ora hannunta a bakinta.

Ba dake nake ba ne”?
Yafad’a cikin b’acin rai!

“Wallahi Yaya Habibu ban sanshi ba,asali ma ban san daga ina takardar ta fito ba,wallahi ban san wanda ya aje min ita ba”

Wani dukan ya k’ara kai mata a karo na biyu,Khamis yayi saurin rik’e hannunsa,yace”Banda duka Habibu, ka bita a hankali mana”

Fuzge hannusa yayi, yace”Ki fad’a min wanene shi”?

“Wallahi ban san ko waye ba,don Allah kayi hak’uri”
Tafad’a tana share hawaye.

“Sumayya wannan rayuwar kika jefa kanki ko,wato ke kunnen ki na k’ashi ne ko,za’ai ta fad’a miki magana ki toshe kunnen ki,shikkenan, hukunci ya tabbata a kanki,kije ki turo min saurayin naki zamu zauna dashi,tunda ya matsu dake,kema kin matsu dashi,sai ai muku aure kawai”
Ya k’arashe maganar yana had’iye wani mugun d’aci irin na b’acin rai.

Kuka take sosai ta ririk’e masa hannu,tana fad’in”Ka yarda dani Yayanmu wallahi, bansan da wannan wasik’ar ba,asalima ni bana tsayawa da wani d’a namiji saboda fad’an da kake mana kullum,ka tambayi su Rabi’a ma kaji”

“Babu Wanda zan tambaya ni,na riga na gama maganata, aure babu fashi,sai anyi miki,dama shine cikar duk wata ” ya mace a duniya”

Cikin kuka Sumayya tace”Yaya Khamis ka bashi hakuri don Allah kaji,wallahi nayi rantsuwar ban san daga inda wasik’ar ta futo ba”

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

Khamis ya sosa kansa cike da farin ciki, tabbas burinsa ya kusa cika, akan Sumayya, yasan yana cewa zai aureta za’a bashi, don haka sai yace”Ki kwantar da hankalin ki, kin jiko Sumayya, zanyi bunkice akan hakan,nasan baza ki aikata ba, kije kawai zan rarrashe shi, ya janye maganar”

Sumayya ta mik’e jiki a sanyaye ta futa daga,d’akin, Habibu ya bita da kallo yana girgiza kai cikin bak’in ciki da damuwa.

Khamis yace”Ni fa ina ganin wannan abun ba na tada hankali bane, dama yarinyar ta isa aure saboda haka ana samun irin wannan, in suka kai wannan matakin saboda haka ka daina d’aga hankalinka, kamar yarda ka fad’a ta turo saurayin nata sai a tsaida magana idan kuma babu ni ina so sai ayi dani”.

Habibu ya girgiza kai cikin damuwa yace”Lamarin yaranan yana bani mamaki wallahi, wai har sun San aure da abunda akeyi a cikinsa,da gani wannan ma mugun d’an iska ne,duba don Allah yadda yake wasu maganganu na shashanci”.

Khamis yasa dariya yana fad’in d’an iska irinka ba, ni banga wani iskanci ba,anan gaskiya ce abunda ya fad’a”.

Habibu ya mik’e cikin b’acin rai yace”Ai halinka ne kaima baku kimtsa bakinku,gurin mata,sai Ku tsaya kuna zantukq da basu dace ba”

Dariya sosai Khamis yakeyi.

Kwanan damuwa da bak’in ciki Habibu yayi a ranar,da ya juya ya juya,wannan kalamai na cikin wasik’ar zasu fad’o masa a rai,wani irin kishi da damuwa su dame shi,wani abu ne yazo ya tsaya masa a mak’ogaro yaki ya fad’a masa, haka ya wayi gari cikin damuwa, shi kuwa Khamis cikin farin ciki ya tashi, kana ganinsa kasan bashi da damuwa, bayan sun futo daga masalaci ne, Habibu ya bi Babansu d’akin sa yana shakar fad’a masa abunda yake bakinsa,yasan ba lallai ne ya yarda ba,amma shi yana ganin Wannan itace maslaha.

Ko da Habibu ya gama wassafa Babansu abunda yake faruwa,sai yaga babu wata damuwa a tare dashi, murmushi ma yake yi, shiru d’akin yayi na wajan minti biyar kana Alhaji Madu yace”Anzo gab’ar da zanyi magana akai, Habibu naji dad’in hukuncin nan,kuma ina alfahari da kai gurin ganin ka kare min Martaba da ta iyalina,tabbas kazama d’aya tamkar da dubu, a zahirin gaskiya akwai wani k’udiri a raina Wanda ya dad’e shekara da shekaru,kuma Wannan kudirina akanka yake ina fatan zaka yi min biyyaya kamar ko da yaushe”.

Habibu yace”Duk abunda ka umarce ni dashi zanyi mutukar bai sab’awa addinin Allah ba”

Alhaji Madu yace”Alhamdulilahi, so nake ka auri Sumayya”

Wani irin gingirim Habibu yaji a kansa,yayi masa nauyi sosai, yace”Alhaji anya wannan lamari zai yi wu”

“Babu abunda zai hanashi yiwuwa Habibu babu haramci idan ka auri yarinyar nan, tunda baku sha nono d’aya ba”

Habibu ya girgiza kai fuskarsa da damuwa yace”ina tunanin halin da yarinyar zata shiga mutuk’ar ta gane,cewar Ku ba iyayenta ba ne,kuma mu ba “yan uwantq na jini bane”

Alhaji Madu yace”Nafi ka tunanin wannan Abu,domin ina tunanin zuwan wannan ranar,to amma ni akwai abunda nake hangowa a game fa rayuwarta,Habibu kaine nawa ina kyautata zaton zaka rik’e min ita da mutumci da amana”.

Shiru Habibu yayi yana share gumi, yace”Hakane Alhaji,bani da abun cewa a wannan al’amari sai dai in ce Allah ya sanya alkairi a ciki”.

Alhaji Madu yace”Ameeen ya rabbi nagode sosai, inayi maka fatan alkairi a rayuwarka,ina fatan Allah ya saka ka haifi “yaya masu albarka da biyayya”.

TSANTSAR BUTULCI complete hausa novel written by Binta Umar Abbale

Habibu yace “Ameen Alhaji”
Mik’ewa yayi zai futa, Alhaji Madu yace”Ai yanzu za’ayi ta ta k’are kaje ka kira min iyayenka,da ita Sumayya”.’

Habibu ya sauka k’asa domin cika umarnin mahaifin nasa,a zuciyarsa yana ganin wannan abu da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa, A zuciyarsa baya jin son Sumayya kuma baya jin k’inta shidai gashi nan dai.

Source

Just to let you Know that all musics files appeared or discovered on our website are from third Party sites, so we dont owned or controlled them we only shared them by link, the only internal files we shared is Ebook, to know more about our policy pls see our Privacy Policy page.

Also Download SABON AL’AMARI complete hausa novel written by Bilyn Abdul

Download

Kindly click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Book 1

Book 2

Comments

table of contents title