Main menu

Pages

WATA RANA complete hausa novel written by Mardeeyat A Taheer

WATA RANA complete hausa novel written by Mardeeyat A Taheer

Description

You are about to download WATA RANA complete hausa novel written by Mardeeyat A Taheer released on 2022 just proceed with your download by following the below instruction.

Gargadi

Godiya ga Wanda ya halicci ruhi yahadashi da gangar jiki.Ina Neman taimakonka ga dukkan Abinda nasa gaba.Ina rokonka ka tsareni da tsarewarka ka bani ikon rubuta Abin da ya yi dai dai da tarbiyan musulinci. KO wuya KO dadi ka doramu bisa tafarkin da ba bu kamarsa,A duniya da lahira,kasamu cikin cetonshi bijahidil sayyadi warah Wato Annabi muhammadu s a w.


“Ina mika godiyata da jin jina ga marubuta aduk inda suke a fadin duniya inayimaku fatan alkhaeri ,gani a duniyarku ta marubuta ina Neman saka albarkanku da shawarwari kuma ina fatan wata Rana nashiga gasar marubuta da wannan littafi nawa. Ina Neman gudumuwarku 🙏🙏🙏
Wannan littafi na sadaukar dashi ga dukkanin wadanda suka rayu bata re da maifiyarsu ba.Suka rayu gun Matar uba .Labarine mai cikeda ban tausayi da tsantsar zalinci,dakuma tsantsar zazzafar kauna tsakanin Ahalin.
Wannan labari kirkirarren labarine nayishine domin fadakarwa dakuma ankararwa ga iyayenmu da shuwagabannin mu.

Gabatarwa

Ka juyamin littafi kota wacce hanya!Kada asauyamin KO watakalma ko harafi !idan har ba’a nemi izinina ba aka sauyamin littafi banyafeba ina Neman sakayya a wajan Allah .Kada asiyarmin da littafi domin nayi shine kyauta ,dukkan Wanda ya siyarmin da littafi banyafeba !Dan girman Allah a kiyaye.

Tsakure

“Aina’u ni na haifeki KO wannan yaran?nafadamiki bazan aurar dakeba yanzu saikinyi karatu.”Abba ka tausaya mana wlh ina sonta kuma Abba Zan kyautata mata k….bai karasaba cikin fusata Abba ya hankadashi tareda fadin “yimin shuru kawai !me ka ke dashi?dazaka kyauta ta Mata dashi?waye kai ?to na rantse da Allah ka kiyayeni maza katashi ka barmin cikin gida .sojojin gidan ya dannama Kira sukazo suka fitar da mlm Abu yana kuka hakama Aina’u na kuka .da gudu ta tashi zata bishi yaya kasim ya rikota Abba yace “Cikata nace kasim cikata tabishi! Da gudu tasaka kafa zata karasa fita Abba yace “idan ki ka fita Aina’u hakika kin fita kenan babu mu babu ke!. Waywayowa tayi cikin matsanancin kuka mai ban tausayi kana ta kalli mahaifiyarta dake waye tana gilgiza Mata kai sai ta mayar da kallonta gun kannenta suma kuka taga sunayi kana ta kalli yayansu shima dai fuskansa harda tausayin kanwarsa .juyawa tayi ta sa kai tareda daga sawunta ta fita.


Kuka Aina’u ta cigaba dayi kana ta dago ta kalli dukkan wadan da ke falon taga yanda sukayi jugum-jugum masu kuka nayi musamman su nusaiba sai Dada itama kuka take harda sharce majina.hankacif yaya kasim ya fiddo ya mika Mata ta share hawayen kana ya mika Mata wani kawataccen gilas cop Wanda yake dauke da zallan ruwan sanyi masu sanyaya zuciya .Karba tayi Tasha kana ta cigaba da labarin .

“Bayan mun bar garin nan muka tafi jos dama tun muna mota ya yi waya zamu zo kuma da muka isa garin jos muka isa wani gari waishi gaisa .Bamu zarce KO ina ba sai gidan mai garin gaisa mukaje mlm Abu ya fadamasa komai nan bayan sallan zuhur aka daura mana Aure kana muka tafi gidansu.Gidansu gidan babanshi ne na gado dakuna 3 ne sai madafa .Daki daya mahaifiyarsa ce a ciki sai daya nasa ne anan mukashiga. Bayan mun Dan huta nikuma inata kuka na zafin rabuwa da Ku mlm Abu yazauna ya rarrasheni dakuma yimin alkawarn nan da 1 year zai kawoni gida kuma yana tunanin Abba zai yafe mana. Haka dai harnayi shuru kana yace nazo muje dakin mahaifiyarsa na gaisheta haka muka fito mukashiga .Matace nagani ba laifi tana da Dan kyau dai – dai kuma farace na tsuguna nace”mama ina wuni ?fatan munsameku lafiya? Wani wulakantaccen kallo ta wurgomin tareda wani gatsine tace “kai Abu wannan itace yarinyar da nakeji anata ya-yatawa wai ka gudo da ita kazo an daura maku Aure? Cikin inkina yace” e ehh umm mama itace .” to barikaji Abu ni bataminba kuma bazata minba!yanzu dai ya alkawarinmu?Eh um am dama . dama mama “dama me eh Abu wlh ba fashi gobe Zan maka Aure wannan auren ka ne ba nawa ba.kuma dama na fada maka tunda har ka dage saika auri wannan Mayyar yarinyar to dole kacikamin burina ka auri Zaitu kaji na fadi maka gobe kashirya zuwan Amarya.tana gama fadan hakan ta wurgomin wani wukantaccen kallo tare da fadin “tashi ka janyemin ita daga nan ta tsareni da kallo ga wasu shegun idanuwa Nata.


WATA RANA complete hausa novel written by Mardeeyat A Taheer

Haka Abubakar ya mikar Dani sabida nakasa koda motsi abin kaman A mafarki nake ganinsa .
Kuka nakeyi sosai A daki tareda wani tsantsar kewan gida da yan uwana .Hakuri yafara bani “kiyi hakuri Aina’u ban fadamikiba mama akwai yar kawarta zaitu tana so ta hadamu aure .Zaitu tunda na dawo bautar kasa taganni ta nuna tana sona .Gashi zaitu bata da kamun kai kuma bata da ilimi domin KO sallah bata bi Mata jikiba ta raina kowa A unguwan nan. WATA RANA complete hausa novel written by Mardeeyat A Taheer Gata da bin malamai gida-gida mai kofa tasan inda zata samu boka .tafadawa mama tana sona ita kuma mama lokaci guda ta gada Mata A’a inada macen da Zan Aura wato ke! Bayan kwana 2 ki ka kiran kinafadamin Abin da mahaifinki yace. nace miki zanzo insha Allah to Ana kamar gobe Zan zo sai mama ta kirani take min maganar Zaitu hartana cewa zata Auramin ita. Abin ya bani mamaki matuka nan na bata hakuri amma taki tace kuma in har na Aureki sai na cikamata nata burin na Auri zaitu! Haka naje nagayawa baffanta shikuma yazo yanata masifa taya zata ka-kabamin wannan marar tarbiyar yarinyar tabarni in auri wacce nakeso amma mama taki hartace zata tsinemin dole aka bar maganar .haka nazo garinku kuma kinga ga abinda na taras to kinji Abinda ya faru Amma ina mai baki hakuri .

Cikin kuka dakuma tausayin kaina nace shike nan WATA RANA SAI LABARI .

Source

Just to let you Know that all musics files appeared or discovered on our website are from third Party sites, so we dont owned or controlled them we only shared them by link, the only internal files we shared is Ebook, to know more about our policy pls see our Privacy Policy page.

Also Download DEEJAMAH complete hausa novel written by Fareeda Basheer (ummu safwan)

Download

Kindly click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Comments

table of contents title