Note:wanan littafin kagagen labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba in ya Zo dai’dai da rayuwarki/ka toh akasi aka samu,ai amfani da Mai amfani ayi wasi da na banza
Warning:ban yarda wani ko wata ta juya min littafina ta ko wace tsiga ba tare da izinina in kunni yaji……….
In dedication to Anty Binta godiya Mara iyaka munyi kewarki da Ahmed
Tukuici ga anty Nibras that lady is kind infact she is superb the warm hospitality da Kika bamu Yana Nan dankare a zuciyarmu so this book is about you and Ahmed……..
🅿1️⃣&2️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mali’s empire,
babban masarauta ce Wanda kallo d’aya zakawa gidan kasan suna ji da mulki da Kuma dukiya,wanan babban masarauta tana tafiya ne a karkashin jagorancin mansa khalifa Wali shi ke rike da sarautar kasar Mali Kai da kaji masarautar Mali ai kasan za a ji da sarauta saboda kasa ne da har yanzu suke practicing monachy,wanan gidan tana da abin al’ajibi..gidane dake tafiya ko ince suna rayuwa ce da son zuciya,hassada,kishi a wanan gidan kowa ta kansa yake domin rayuwa ce akeyinsa ta do or die affair most expecially matan mansa watoh su Gimbiya’s,Kai hatta bayi da kuyangi in short ma’aikatan gidan Basu da dabi’a ta son juna sai ta kushe juna da son ganin na d’ara d’an uwana a matsayi.balle Kuma a Zo Kan ya’yan mansa Wanda kowa so yake a ce shi zai gaji sarautar mali akan wanan sarautar zasu iya kashe juna ko ince wasu sun kwanta dama akan wanan battle din..wanan abin na ciwa mansa khalifa tuwo a kwarya Wanda har ya haifar me da hawan jini da kullum yau lafiya gobe babu….ya rasa ta inda zai b’ullowa wanan al’amarin Taya zaisa iyalansa su so juna wani lokaci ji yake kamar ya sawa kujerar sarauta wuta ko zai huta da takaici,kamar dai cikkaken sarki matarsa hud’u….ta farko itace gimbiya Zenabu Yar kasar Mali ce,ta biyu Kuma akwai gimbiya Hadizatuo itama Yar maki ce,ta uku akwai gimbiya meryam ita Yar kasar Cameroon ya’ce ga wani attajiri,ta hud’u akwai sultanan Bintu yar kasar Nigeria ya’ga sarkin adamawa cikkakiyar bafullantana,mahaifinta mohammadu barkindo….the lamido of adanawa
Gimbiya Zenabu tana da ya’ya 6 Mata biyar,namiji daya watoh aliyu duk matan na gidajen mijinsu wasu na gidan sarauta wasu Kuma sun auri attajirai suna kasanshen ketare..hadizatou Kuma ya’yanta uku duk maza Amma Kuma kanana ne kasancewar Bata samu haihuwa da wuri ba
Meryam tana da Yaya biyar maza biyu Mata uku saidai mazan ne kanana itama matan suna gidan miji Amma idanunsu na Kan sarautar kowa so yake a ce d’an uwansa ne zai gaji sarautar mali dukda sun San they don’t stand a chance yakin tsakanin gimbiya Zenabu ce da Kuma gimbiya Bintu dukda ita gimbiyar bintu sarautar be dame ba be d’ad’a a kasa ba ko kad’an ba shine gabanta ba itako gimbiya Zenabu fargabanta shine Kar fa yarima Ahmed ya gaji sarautar kullum in tayi duba da inda akayi haihuwarsa da aliyu d’anta…watoh a rana daya aka haife yarima Ahmed da yarima aliyu Wanda tazarar awa daya ne tsakani,gimbiya Zenabu ta Riga sultanan Bintu samun ciki domin cikinta na wata biyu sultanan Bintu ta samu ciki a lokacin tana amarya Bata damu da cikin gimbiya bintu ba mussaman da cikinta na wata bakwai aka tabbatar Mata namiji zata Haifa sai take ganin ta tsallake babu Wanda zai kamota a tunaninta ko namiji sultanan Bintu ta Haifa toh fah saidai ya Zama kanin d’anta domin a wanan lokacin babu Wanda ya haifawa mansa Dan namiji saidai shi Allah ba ayi mishi shamaki a lokacin da Cikin sultanan Bintu ke wata bakwai na gimbiya Zenabu na watanin haihuwa har ta Shiga ta goma shiru Bata haihu ba kwasam aka wayi gari sultanan Bintu ta tashi da matsanancin ciwon Mara aka Kaita royal hospital dake gidan ko minti ashirin ba ayi da kaita ba nakuda ya tasowa gimbiya Zenabu aka Kaita asibiti itama
Gimbiya bintu ce ta Fara santalo d’anta namiji pre-matured saidai ta jigata sai bàyan awa d’aya cifff gimbiya Zenabu ta haiho d’an namiji itama laffiyaye
An Kai dan bintu kwalba domin Bata da isashen lafiya dan shima Yana bukatar kulawa
Madadin gimbiya Zenabu tayi farin ciki kawai sai ta tsinci kanta cikin matsinacin bakin ciki yanzu me hakan ke nufi???d'anta shine karami kasa da d'an bintu?? Hankalinta tashi yayi da akayi bikin suna aka had'a da bikin nad'a A'hmed watoh yarima Wanda zai gaji sarautar ita Kuma Bintu Sultanan watoh uwa ga sarki me jiran gado...
Wanan shine dalilin kiyyayar da takewa yarima Ahmed da uwarsa Wanda yanzu shekarunsa talatin a duniya Yana da matarsa Kamar inda aliyu ke da matarsa…aliyu ya tsane Ahmed ya Sha attempting kashesa Allah na kuburta dashi domin har poison an tab’a basa Wanda har yanzu ba a gano Wanda yayi wanan aika aikan ba
Watanin shidda da Suka wuce
A wata daran laraba....da misalin karfe biyu na dare
Lullube take cikin bargo cikin duhun dare nan rike da jariri Wanda da alamu akwai abinda aka bashi yake wanan baccin
Dube dube take tana bin private Chambers da ba kowa yasan dashi ba sai tsohon mazaunin gidan duk inda tasan akwai haske Bata bishi ba sai ta baya
Can kofar baya Wanda private door ne Wanda ba kowa yasan dashi ba,tsaye yake Yana jiran fitowarta tana karasowa ta Mika me jinjirin da ko wata uku beyi ba a duniya ba,ya amsa ita kanta Bata gane fuskar waye ba domin ya rufeta kamar inda shima be nimi sanin ko ita wacece ba umarnin aikin da aka Basu suke bi ita ance ta fito baya zata gan mutum shima ance ya jira anan
Mika me envelope tayi ta juya da sauri ta fita shima haka ba tare da sunma juna magana ba
Abinda zai baka mamaki kafin ya karasa kofar wani ya bude Masa kofar ya fita
(This is just a tip of the story……..stay tuned”)
#
South SudanYariyar ta ja hankalina har na bita da kallo Ina Kare Mata kallo da mamankinta yariya ce da a kalla bazata wuce shekaru goma Sha biyu zuwa uku ba sanye da wata doguwar Riga data fita a hayyancinta hatta hijab din kanta ta yage abinda yafi Jan hankalina shine tana tare da goyo d'an namiji,sai Kai komo take cikin yarensu ta shuwa Mai Kama da larabci tana cewa ku siyi pure water domin roba ruwan ne akanta kana ganinta kasan rayuwa Bata Mata adalci ba
Bismillahir Rahmanir Rahim
🅿3️⃣&4️⃣
Ba laifi tana samu masu siyan ruwa kukan da yaron keyi yasa ta nimi inuwa ta sauke robar ruwa ta saukosa a baya tana jijjigasa tana peting bayansa Amma sai tsala ihu yake karamar Jakarta ta bude ta Ciro feeda da da sachet cerelac dinsa ta kwab’a Masa da ruwan sanyi ta sa Masa a Baki Amma yaki amsa,hawaye ya kawo idonta cikin tausayinsa ta rungumesa tasan yunwa yake ji Amma in yayi fushi Yana da wuyar saukowa zuciya ne dashi na wuce iyaka sai ajiyar zuciya yake saukewa
Zama tayi ta ajiye shi a cinyarsa ta zuba me Ido tana kallonsa sai Kuma ta fashe da kuka saboda in akwai abinda ta tsana shine ya gan A’med dinta na kuka Saida ya gaji Dan kansa yayi shiru Yana sauke ajiyar zuciya ta rungumesa tana lallashi kafin ta kafa me feeder a Baki bàyan ta bude ya Fara kwankwad’a har ya shanye ta sake dama Masa wani ya Sha ba a Jima ba bacci Mai nauyi ya d’aukesa
Ajiyar zuciya ta sauke ta zuba me Ido so dayawa in ta kalleshi sai taji tausayinsa na kamata damuwarta yanzu Taya zata samu kudin kula dashi itafa a rayuwarta ba Arabi ba Boko..marainiya ce ita da abinci ke gagara ga Karin responsibility toh kodai zata amince da auren baba Musa Wanda ya kusan shekara 70 da aure in har zata samu biyan bukata na ya ta ciyar da ita da A’med ai ba komai,girgiza Kai tayi tunawa da tayi inda rayuwar sauran Yan matan da sukayi irin wanan auren ke tagarrayya karewa ake a wahala tun mahaifinta na Raye be yarda da wanan auren da ya zame musu al’ada a ce Yar shekara 8 za a aurawa tsoho da ya Isa yayi jika da ita,ya Kuma ja Mata kunni duk rintsi ko bàyan ransa Karta yarda tayi wanan auren but rayuwa na niman tura ta bango
Mikewa tayi ta maidashi baya ta aza robar ruwanta ta cigaba da tallah sai dai duk tana Jin zafin jikinsa dama Kuma ya tashi ne da zazzabi
Bata Bari ta Sayar ba ta koma inda take d’aukar ruwan ta biya matar ta tafi da ribar
Chemist ta je ta siya me maganin zazzabi ta juya gida
Tana zuwa gida ta tarar da ma tsaye kofar gidan cikin yarensu Dan ba hausa suke ji ba bàyan ta Mata wani kallo ji tayi ta fisgi A’med a bayanta cikin matsifa take cewa’yau wallahi sai kin aureshi ko Baki so ga jama’a an Zo za a sa Miki lalli mutumin Nan Nima yake ya daureni Dan naci kudinsa ya bani daga yau zuwa jibi ko a kaiki gidansa ko Kuma a biyasa kudinsa nikuma sisi bani dashi Dan haka yau za a sa lalli gobe a d’aura aurenki ko Baki so
Shikuma wanan tsinanne d’an da ba a San inda Kika tsintosa ba yau Zan san inda zanyi dashi
Kuka A’med ya sake itama tana kuka tana kokarin amsarsa Amma ma tayi me rikon wulakanci yaron da duk ya firgice daman Kuma tsoronta yake
Nibras tayi ta kuka tana rokon ma Amma fuuuuu tayi ciki Kamar zata tashi sama
Ciki tayi itama tana bin ma tana kallo ma ta wurga A’med d’aki ta kulle ita Kuma kanne ma biyu Suka Kama ta Suka cire Mata hijab a dole Suka Fara gudanar da wasu abubuwa na kamun amarya
Kuka take tana fisgewa Kamar ranta zai fita babu abinda yafi d’aga Mata hankali Kamar inda take jiyo kukan A’med har shid’ewa yake sai dare suka barta duk inda ta so d’auko A’med abin ya fassakara
Tun tana Jin kukansa har taji shiru ita kanta kukan ya daina zuwa mata tayi ta leken d’anki sai Kuma ta zauna lokacin kowa yayi bacci ita kadaice a waje tana Kai komo tana Jin wani ciwo azuciyarta yanzu dan mahaifiyarta ta rasu mahaifinta ya rasu sai a zalunceta in auren ma ke son tayi Mata me zai hana ta had’ata da Bashir me sonta Kuma shima yaro Amma Saida ta shiga ta rabata da Bashir ta tura me yar’ta yace ya fasa aurenta shine ita dan rashin gata zata had’ata da tsoho Wanda a zamanin da akayi wanan al’adan yanzu Kai ya waye
Kuka ta fashe dashi ta Kuma leka d’akin d’an haske ta gani kad’an alamu ta window ne ajiyar zuciya ta sauke ta fita da sauri zuwa bayan gida Aiko window na bude
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke ta budeshi Daman ta katako ne ta shiga ta d’auki A’med ko tashi beyi ba Dan da alamu yayi wanan mugun baccin nasa dakeyi in yayi kuka sosai
Fita tayi ta window ta goyashi cikin Daren ta dau hanya cikin gari ko waigawa da tsoro babu
Tafiya Mai nisa ya kaita gidan kakanta watoh mahaifiyar mamanta sai kusan asuba ta Isa gidan
Nigeria
Kamar kullum goye take da d’anta cikin dare a bakin hanya shikuma Yana jiran mechanic Dan motarsa ce tayi paci
Kura me Ido tayi shima ya zuba Mata Ido a lokaci d’aya hawaye ya wanke Mata fuska karasawa yayi da niyyar Yi Mata magana kawai sai ta b’ace b’at
A firgice ya tashi Yana sauke numfashi kanshi na mugun tsara me,zufa ya goge yace”a dream again,same girl???”
Ya dafe Kai ya kunna bedside lamb dinshi saidai zuwa yanzu wanan mafalkin ya Fara d’aure me Kai dole yayi sharing da wani
Sauke kafarsa yayi a saman had’adiyar slippers ya sauke net dinsa me rumta irin ta gidan sarauta d’akin kadai duniya ce ya shige bayi yayi wanka ya d’auro alwala Yana fitowa ana Kiran sallah asuba
Jallabiya kawai yasa ya fesa turare ya saka wata dogon wando sport Yana tafiya cikin izza da taku irin ta jinin sarauta ya fita massalaci
Bayan idar da sallah Suka
Comments
Post a Comment