Main menu

Pages

 


21&22 

Nidai Yau sukuku na kasance a makarantar Hadda ,na ƙwazon karatuna duk ya tafi banma san me suke karantawa ba ,haka aka tasheni in biya haddana ,na ida inda inda ɗina ya mu'allim ya mun zanan rashin iya Hadda na koma na zauna ,tagumi kam in na gaji da wannan hannun in maida wani hannun a haka har lokacin tashi sallar magrib yayi ,duk ƴan aji suka watse suka Barni ƙatooo ba magana ,kunsan dai makaranta baya rasa tashin Aljannu tun Bama makarantar da aka tara ƴan mata ,so kowacce ɗaliba batayi gigin kulani ba ,a zatonsu inada Aljannune suna son su tashi ,haka kowa ya raɓa ya fice ya Barni Ni kaɗai a ajin  .

Prefect ne sukazo bibiyan marasa zuwa sallah aiko sai gani zaune a aji ,nan suka shiga yarɓamun dorina,nan kuwa nace dawa Allah ya gamamu ba dasu ba ,Nan muka carke da dambe ,suna zugamun dorina ina zaginsu ina buji buji da hijabi ina kaima iska Naushi .


Allah ne ya bani sa'a na damƙi hannun babbar su wato Ameera (Head girl) na yanka mata cizo ,nan ta fasa wani gigitaccen ƙara ,zafin hakan ta ɗaga hannu ta kwalleni da mari ,baya sauran prefect ɗin sukayi da sauri ,saboda sunsan Ameera nada kangararrun Aljannu kar su tashi makaranta yaƙi daɗi .


Kallonta nayi ido cikin ido "Ni kika mara? To bar ganin ana tsoronki wai kinada Aljannu ,bari kiji ba almatsutsai ba ,ko bishiyar tumfafiya ne bisa kanki sai na rama"

Zare mun ido tayi "Na mareki ɗin ai ga fuska zoki rama me yasa kika tsaya cika baki ? banza ƴar karuwa"


Habawa ina wuta ina jefata ciki? Wani kukan kura nayi na turmusheta Ni kaina bansan inada irin wannan ƙarfin ba ,dambe muke kamar zamu kasha juna ,tuni aljannunta suka tashi aiko ta ɗaga Ni ta nuna ma Allah ya damfara a ƙasa 


Wani tsuwwa naji ƙashin bayana ya ɗauki yi tamkar ya tsage ,nakuwa yanka wani irin firgitacciyar ƙara ,sauran ɗalibai a take sukayi wa ajinmu ƙawanya ana leƙe ta window "shikenan dukkansu Aljanunsu ya tashi " zumbur na kuwa miƙe na sake tunkararta still wuji wuji tayi dani ta Nana da bango ,a wannan karon saida goshina ya kwailaye ,jini ya shiga fita sharrrrrr ,lumshe ido nayi wani irin jiri na musamman me haɗe da zazzafan ciwon kai a take ya lulluɓeni,rangaji na fara yi ina neman faɗuwa inajin ɗalibai suna "Allah sarki Aljannunta sunfi nata ƙarfi wayyo" 

Daidai nan malaman suka kawo mana ɗauki itakam Ameera tuni ta fyalle hijabi ta yar da ɗankwali tana ɗaga jerangiyar kujerun ɗalibai tana tandarasu da ƙasa duk sun karairaye ,malamai sun sha wuya kafin su iya riƙe ta ,Nikam ina gefe ina jan numfarfashi ,ina ganin sun riƙe ta ana ɗaureta


"Ku kama bilkisun ku shaƙa mata maganin sai a fara mata ruƙiya" ai inajin batun ya mu'allim na zaburo da sauri na fixgo Ameeran ban wata ² ba na nana mata cizo a kafaɗa ana ƙoƙarin riƙe Ni itakuma ta miƙe nan dambe ya dawo sabo ,faɗinike "Ni kike kiran uwata da karuwa??" Lallasani ta cigaba dayi dukda ana riƙe ta tana zubar da mazan ,can da Allah ya bani sa'a na damƙi Nonon ta da suka gama cika suka tumbatsa amma ba'a saka masu brazier , aiko na gartsa ma kan Nonon  cizo wani ƙaran Azaba ta saki ,a take aljannun suka jirge suka barta nan ,muka cigaba da damben mutum da mutum ,tunda na gano lagonta ,ai tana dukana ne ina harin ƙirjinta Har Allah ya ƙara bani sa'a na damƙosu na shiga lilo ,ji take kamar ana ɓara mata ƙirji haka take ihu tana roƙon don Allah azo a rabamu


Sukuwa malaman sunyi fushi sun ja gefe ,ana haka saiga malam Yakubu da bulala nan ya shiga shishshigar mana a jikinmu 


Saida duk yaga mun kwanta muna birgiman muna kiran "Malam ba Aljanu bane mune Ameera da Balkisu ...."

Yarda bulalan yayi ya fice yina sababi 


"Haba ,ruƙiyyar da kuke zama kuna yiwa yaran nan shi yike sasu iskanci da karyar Aljannu da sai anfi bayan isha ana fama da kantagara , mma yanzu ba gashi sun tashi..mtseww"


****

Daga wannan ranar kunyan zuwa Hadda ya dasu mun a rai sam ta cire mun mora da Hadda ,ƙarshe dai nasa saida aka cireni a haddar aka sakani wani,Halin uwata yina taka muhimmiyar rawa wajen kashemun karsashi a cikin jama'a ,nikan kasance shiru,fiye da in yi magana dukda kasancewa ta ada yarinya mai kazar² me ya jawo mun duk hakan? Ina tsoron kar Inyi ƙwaƙwaran motsi a aibata mun uwa da halayyar da ta ɗiba ta axawa rayuwarta da rana tsaka


*****

10.am Monday

Da sanyina Nike komai tunda aka tashi a break sam Banida karsashi ,sosai sanyina nayau ya zama over .


Duk yara sun watse sun tafi break sai Ni ɗaya ƙwalli ,na ɗauki littafi na kange kaina kamar me karatu amma damuwa ce fal raina da zullumin yau kuma wani gori su rahama en gidanmu za suyi mun in na koma gida?


Mahmud Abbas Yarone matashi , kyakyawa mai ƙoƙarin gaske tun daga primary ɗinsa har SS2 ba a Nigeria yayi shiba ,a taƙaice kwarafniyar Nijeriya sam bai santa ba,Baban sa shine Commissioner of education meci a wannan lokacin ,sakamakon naƙasu da koma bayan ilimi a ƙasar mu dama jiharmu sai mutane suka fara zagin mulkin su Hon. Abbas ,babbar zaginsu shine Hon.Abbas ya kasance Commissioner ilimi amma ba wani background ɗin karatun ɗansa ɗai da yayi a ƙasar nan saboda yasan ƙasan babu nagartaccen Ilimi,matsayinsa na ɗan siyasa don ya guje ma yawan zagi kawai sai ya yanke shawaran ya ciro Abbas ya dawo dashi gida ya sakashi a wata makarantar kuɗi wanda ace ba laifi sai ya cigaba ,wannan dalilin yasa aka kawo Mahmud makarantar mu Ni Bilkisu Idris Makama.


Mahmud ɗan leƙowa ajinmu yayi baya dashi abokansa ne sunkai bakwai ,hannunsu da kayan su chocolate da chips  


Ya daɗe yina lura da sanyina ,kyawuna kuwa yina mugun firgitashi ,hakan ya saka masa ƙwarzababben so na Nikam banma sani ba a matsayina na ÿar js 3


A hankali cikin nutsuwarsa yau dai yayi kundumbala ya tako inda nike ,Knocking (ƙwanƙwasa) desk ɗina Yayi a hankali 


A fizge na jawo lulun eyes ɗina na watsa masa ,fuskata sarau ba yabo ba fallasa 


"Zan iya zama?" Ya nuna mun saman desk inda na ɗaura hannuwa na 


"A'ah ba'a zama a nan rubutu akeyi akai saidai wani wajen" 


Murmushi yayi ya dawo gefena ya zauna ,shiru ya biyo bayan zamanmu saima tsaki da nikeyi lokaci bayan lokaci saboda yanda abokansa sukayi mana tsatsaye kamar wasu guards 


"Kinada kyau kin sani?" 

A bazata maganar yazo mun ,ɗan caɓe baki nayi 


"Haka akan ce " lafiyayyen murmushi ya saki d ya ƙara masa kyau yarantarsa na ɗan shekara sha bakwai ya daɗa fitowa 


"Oh baki sani ba ? Ah u have to know ya kamata ki sani" 

Karkacewa yayi ya zaro smart phone ɗinsa mai azaban kyawun Camera ya saita selfie bai Ankara ba saidai naga ya kango kansa wajen kafaɗana ,a sanyaye yace dubi nan 


Ina ɗago idona ya maza ya ɗauke mu a tare ,ɗaure fuska nayi zan masifa kawai ya saƙa yatsun hannunsa a gefen bakinsa ya saki fitoo


"Nagode beauty " ya raɓa ya fice suka Barni da tulin ledojin kayan ƙwalam da suka siyo wai Inyi break


Ÿan matan ajinmu da suke maƙalƙale ta window kuwa ,suna ganin fitansa suka zagayo da sauri harda wainda Bama magana dasu ,sukazo suna tambaya na ko ɗan uwana ne ? Ko na san shine?


Girgiza masu kai nayi na daɗa rufe fuskata da littafina na barsu a tsaye a nan 


Nadiya ce tayi zaraf ta janyo ledar ,ta ɗebi chocolate da chips leda ɗaya 


"Sweetheart in ci"

Banza nayi mata ,a hankali ta daɗa matsowa kusa da fuskata "My loveee magana nikeyi ,muci don Allah"


A ƙufule nace "To dama nawane ,kuci mana Ni ina ruwa na " 


Wow kamar ƙudaje ,kundai san yaran masu kuɗi basu iya son banza ba ko bazasu ci abu ba don kawai ayi dariya haka suka dokawa kayan nan wawa suka parke ledan kowa ya ɗebi rabonsa ,tas suka rabe i junansu ƙarshe wanda suka Ajemun nace banaso Nadiya ce ta karɓa ta sakamun a jaka  .


*****

Washegari 7.20 

Muna assembly field na saka uniform ɗina da er ɓingilar Army blue ɗin sket mai ɗan yalwa iya saman gwuiwa yasha guga da farin Safa na shi ma ya hayo har gwuiwan ,na karkata hulan beret ɗina akan gashina da yasha kitson ibira style na shiku an jera mun white bids a ƙarshen kitson da wanda suka watso ta gaba 


Tsaye nike a layin en ajinmu ƙafana sanye cikin cambas mai kyau baƙi na goya ƙatuwar jakar bayana , Sosai nayi kyau kowa Ni yike kallo 



Mahmud tunda motar gidansu ta ajiye shi a tsakiyar makaranta yike wiwwurga idonsa cikin layin en ajinmu sam bai ganin ko wacce mace sai Ni ,Ni Bilkisu 


Malamai ana dakatar dashi ana komai saida ya kutso cikinmu ,ba zato naji an riƙe mun hannu a ɗan tsorace na ɗago ,kafin in magana ya tari numfashina "Kinyi kyau beautyy" yana faɗin haka ya sakeni ya juya a take wani ƙwarzababben ajiyar zuciya da bansan ya ƙwacemun ba . 


Caaa malamai sukayi masa da faɗa wai yayi kneeling 

Kallonsu yayi 1 on 1 ,sai kuma ya ɗaga kai wajen da malamai ke tsaitsaye za ayi assembly ya ƙwallawa shugaban makarantan kira ,wanda yasa kaf makarantar yin tsit 


"Principal ,baki faɗawa malamanki sharaɗin Babana bane ,babu duka ba tsawa,tsakaninsu dani su koya mun karatu a biyasu haƙƙin koyarwansu ,ko baki faɗa masu raayina ne ya kawoni makarantar nan ba tilastawa ba??....ku matsa in wuce ko anjima kuga takardan dakatar da makarantan nan domin Ni a USA ba haka ake mu'amala da ɗalibai ba ,daidai da jarabawa roƙonmu akeyi ana lallaɓamu sai mun ce mun shirya zaai mana kuma mu ɗalibai mune zamu tsara time table ɗin jarabawar"


Sosai yaja masu warning kuma aka kiyayesa 


Saida aka tafi ajine principal ya kirasa yina masa nasihan me ya kaisa wajena ba shayi babu komai ya tsaida idonsa akan principal 


"Ina sonta ne sir, jiya na kasa barci har mafarkinta saida nayi ,ina zuwa ita nikeso in fara gani ,sai kuma nayi tozali da ita cikin kyakyawar gani ,dole zuciyata ta azzala mun inje in faɗa mata tayi kyau....kuma ina faɗa mata najuyo"  


Sakin baki yayi yina mamaki ,ƙarshe dai ya sallamesa ya tafi .....Abokansa suka biyo bayansa ɗuuuuu


"Mahmud wasup? Yayi maka faɗa?"


"Um um ai principal is understandable person (mutum ne mai fahimta) Ya tambayeni mai ya faru Ni kuma nace masa ina sonta ne ...." 


Buɗe baki sukayi 

"Chaiiii 😱 Yaro kana ruwa"  


****

Daga wannan ranar Mahmud ya daɗa shiga rayuwata sosai ya takureni matuƙa gaya ,kyaututtukan banza da hofi yinmun shi yake ,fulawa kuwa da kullum yike mun kyautarsu irin yanda yike ganin yaran turawa na yi,dole nike amsa saboda nacinsa gashi yinada ɗaurin gindi ,dole in Inaso ya ƙyaleni Nike karɓa nakuwa Tara Sosai cikin wata jaka


Sun saba sosai da nadiya tana moransa yina kashe masu kuɗaɗe don kawai a ja raayina ,yau da gobe kuma abun ya fara tasiri gashi yanzu nima na fara biye masa 


Now na yarda ina son Mahmud ,Mahmud he's my first love 💞


Comments

table of contents title